← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 163

Sashe 27

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aa ni da Hajiya Fatee duk ba mu gama warkewa daga damuwar da muka shiga ba, baka san yan ta'adda suka kama mu ba?”

“Kai na ji Hajiya, zuwana talatin gidan nan sai ace min bata nan, wai wasu ne suka kamata, da an fada min ba za a biya sisi ba zan karbota ni sai a ba ni kudin, akwai mutanenmu fa masu harkar kuma ni Wallahi jan wuya ne, bana inda bana iya shiga, karfe be fasa ni bundiga bata kama ni sai dai ayi min tambo, danjar nan da kika ji ance Hajiya ni fa danja ne, uban fitina kuma bana tsoron kowa”

“Kai zaka iya aikata komai kenan Danja?”

“Zan iya komai Hajiya mun zubar da hannaye mun cire kafa, rai ma mun wulgar da shi barzahu, Allah dai ya shirya mu kawai”

“Shiyasa Hajiya take tsoron ka, ni ma ina gudun na janyo ka jiki na jawa kaina matsala”

“Kai... Kuturi”

Ya rike baki.

“Wai Hajja Fatee tsorona take? Ita din ai uwa ce ba za a mata komai ba, wani ma be isa ya mata ba balle kuma ni, ba dan ita ba da yanzu na barar da hanjin masu aikin nan nata, alkur'ane da yanzu ka ga hanta ya lilo shushushushushuuuuuuu”

Ya nuna yadda hantar zata rika raea idan ya sareta.

“Toh yanzu dai zan shiga gida, zan aiko mai aiki da number wayata idan ka samu waya sai ka kira ni mu yi magana, amman dan Allah ka daina damun Hajiya Fatee da yawan zuwa”

“An gama amman Hajiya yanzu akwai wani abu nan? Ina fatar ke ma kina da yan abubuwa yan timatinmai eh... Eh.. Kin dai gane”

“Zan aiko mai number tare da kudin da zaka hau babur ka koma”

Tana fadin haka ta yi gaba tana nufi gate zata koma ciki, shi kuma ya bita da kirari yana daga mata hannu.

“Chau chau chau chachachau lafiya lau ne Hajiya, Allah dai ya kara miki kwanciyar hankali ya kara miki ƙiba kai kana ganin Hajiyar nan ka san akwai manyan kaya, Allah ya kara sutura”

Cikin gidan Hajiya Kaltume ta koma ta shiga dakin Hajiya Fatee ta samu biro ta mikawa Hajiya Fatee domin ita bata iya rubutun ba.

“Rubuta masa number ta a nan”

“Numberki kuma? Me ya faru? Karki jawa kanki matsala fa irin wadannan ba su jin magana”

“Ke dai rubuta babu komai, ke na ke yi ma jihadin ai, wayo yake masa”

Hajiya Fatee ta karba ta rubuta mata number ta mika mata. Hajiya Kaltume ta bude jakarta ta dauko 3k ta hade ta takardar ta fita falo ta bawa mai aikin ta umarce ta da ta kai masa. Sannan ta juyo ta dawo dakin tana tambayar Hajiya Fatee ya aka karkare da Salame.

“Na kirata na mata bayani, ta ce ai ya canja line saboda rufe masa wacan da masu gidan line suka yi, amman yanzu zata turo min sabuwa numbersa kuma zata kira ta masa bayani”

“Haka nake son ji, to yanzu ki kwnatar da hankali ki kira ki fada masa ya shirya komai na sa ya zo garin nan zamu aika da mota a dauko shi a kawo mana har gida, daga nan sai mu gabatar masa da matsakarmu”

“Amman kina ganin zai yarda ya zo?”

“Hajiya Fatee miye kudi ba zai yi ba? Muradi dai abashi kudi shi kuma ya biya mana bukata kawai”

“Ni dai Allah yasa cikin nan ya tausu, idan ba haka na zan shiga uku ga shegiyar suruka zata ji dadi”

“Komai zai wuce Hajiya Fatee ki kwanatar da hankali”

Cewar Hajiya Kaltume ga aminiyarta tana murmushi.

IYAMI POV. .

“Iyami ba a zama haka, ke kanki kin san mijinki yana sonki, ga yaya yanzu kuma ga cikin nan da kika shiga watan haihuwa, kamata yayi ki nemi taimako idan ma wani asirin aka yi masa aka rabaku a karya shi, ki koma dakinki bana son ki haihu a gida Wallahi”

Amma ta yunkura da katon cikinta ta tashi zaune daker tana kallon Hindu dake maganar.

“Hindu, Wallahi ban taba yi ba, su kansu da suke ganin kamar asiri na yi ma Alhaji yake ta so na ko na malleke shi, ban taba bada naira biyar na ce a mallake min Alhaji ba, tsantsar biyayya ne kawai da kawar da kai da kuma jin maganar duk abun da ya fada, ni yanzu ko zaki dora wuka a wuyana ba zan iya fada miki sunan Malami daya da na sani ba a garin nan, ban taba yi ba, Gwaggo ma bata taba ta yi ba mu ba mu da kowa sai Allah”

“Na sani, to ai tambaya ake kin ga har na tsarin jikinki sai ki sha kuma ki bawa yayanki, domin su ma ba barinsu zata yi ba”

“Ni dai ba zan iya ba, na kai kukana ga Allah shi zai min magana, ko yanzu ai ba yadda suke so suka samu ba, duk wata sai ya aiko min da abinci da kudi saboda cikin nan, yanzu kuma kina ganin yadda aka cika harabar gidan nan da itace saboda na shiga watan haihuwar, na san idan ra'ayinsu za a bi ba zasu so haka ba, yarana kuma idan ya auna lokaci ya kan aiko da su su gan ni na gansu, an rabu ne kawai amman kamar ana tare, idan Allah yayi zan koma sai ki ga na koma kamar yadda ban saka ran auren Alhaji ba Allah yayi kuma aka yi auren”

“Toh Allah yasa haka shi ya fi alheri, amman dai da kin tafi ba a san inda za a dace ba”

“Allah ya hada mu da dacewar”

“Ameen”

Ta amsa ba dan ta jidadin yadda Iyami ta ki amincewa da zuwan ba.
[10/20, 6:26 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy

𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣5️⃣

Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida.

*** *** ***

Ba kadan ran Momy ya ba ce ba, jin cewar Captain ya zo gidan tana bachi, kuma ya fita da bacin rai saboda Hurriya.

“Oh to wai miye na siya mata gilashin ma?”

Namra ta aje spoon din hannunta.

“To nidai ranar da ya zo last na ganta da shi cirko cirko, gilashinta a kasa tana lalabe to shi ne yau take fada min ai marinta yayi saboda sun yi karo”

“Ai gara da mareta ma, yarinyar nan bata da hankali, sannan yanzu ya zo ta ki ta karbi box din wata kila ba zai sake dawowa gidan nan ba kuma, ta ja min ya fara fushi da ni kenan”

“Shi ma fa Captain din nan ya cika zuciya ga zafin hannu, amman dai bata kyauta ba da bata karba ba”

“Bar yar iska bata san su waye iyayensa ba ne shiyasa, shi ma dai miye na kawo mata glass ko makancewa ta yi iya ruwansa”

“Kila ya ga be kyauta ba, ko kuma...”

Momy ta kalleta da duba kyama.

“Ko kuma me? Allah ya kiyaye ai ko mata sun kare duniya Captain ba zai yi komai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar na duka ma nawa take shekaranjiya ta yi 16yrs fa, kuma shi da yake da matar da zai aura”

“Toh ba sai idan anyi auren ba, wannan me bakar zuciyar? Ba kowa ce zata iya zama da shi ba”

“Ai ko fasawa aka yi sai dai ya aureki, daman Hajiya Turai ta so a hada wannan zumunci shi din ne ya ki, kuma kin san basa masa dole ”

“Ni”

Namra ta nuna kanta domin bata taba jin makamacin haka daga bakin Momy ba.

“Ke fa mun sha yin maganar da Hajiya Turai ai, amman shi Jameel din ne be yarda ba, yanzu dai ya samu wadda yake so an huta”

Namra bata ce komai ba ta maida idonta kan abincin da take ci tana motsa shi a hankali kamar mai tunani. Momy kuma ta tashi daga dinning din tana ta masifa saboda Namra bata tasheta daga bacci ba.

“Kiransa zan yi yanzu Allah yasa ya daga, kar wannan yar filfilwar ta jazamin masifa ni Nafisa”

Nan ma Namra bata ce komai b ta cigaba da motsa abinci tana tauna wanda yake bakinta ta kasa hadewa sai tunani take. Kamin ta juyo ta kalli falon da aka bude, Hurriya ce ta shigo kanta ba dankwali rabin kan nata a tsire.

“Yi sauri ki dauki abun da zaki dauka ki fice kamin Momy ta fito, dan na san sai ta miki fadan kin karbar box din da Captain ya baki”

“Abinci zan zuba”

Ta nuna abinci tana kallon stairs gabanta sai tsananta faduwa yake.

“Zo ki zuba”

Ta nufi dinning din da sauri ta dauki plate ta zuba abincin mutum biyu ita da Hamad ta saka naman kaza a sama ta dauki spoon biyu ta saka.

“Ke da Hamad zaku ci?”

“Eh”

“Dazun shi ya hana ki karbar glass din ko?”

“Na ga ya bata rai yana hararata, na san idan na karna zai iya min masifa kuma yayi fada ni, ko ya dukeni”

“Ke dai Hamad ya raina ki ya maida ke kamar kanwarsa, ko dan ya ganshi babba ke kuma ba ki ba”

Hurriya ta yi dariya mai sauti ta shiga Kitchen ta dauko tray ta dora ruwa da lemu a kai sannan ta fito ta dauki plate din abincin ta dora a tray ta dauka ta fice da sauri. A harabar Apartment din Hajiya Kaltume ta dawo ta zauna a balcony kusa da Hamad ta aje tray.

“Hamad zo mu ci abinci”

Ya kalli abinci sai ya bata rai.

“Waya ce ki hade? Waye zai ci abinci da ke to?”
Chapter 27 · 0% Book details