← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 163

Sashe 47

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta taso ta karaso kusa da shi, ba duka take tsoro ba domin be taba dukanta ba, fadansa take tsoro tun daga lokacin da ya canja mata sai ya zame mata abun tsoro bata ma son zuwa kusa da shi sai da dalili domin ta lura baya bukatar ganinta.

“Appa gani”

Ta durkusa gabansa tana kallonsa ta cikin gilashin idonta, Yasir na tsaye gefen Hajiya Kaltume dake zaune kusa da Appa, Khairi kuma na zaune a dayar kujerar tana shafa man zafi.

“Miye wannan?”

Appa ya nuna mata video karin kudin da aka yi mata. Sai ta saka hannu biyu ta karba tana kallo jikinta na rawa kamar yadda bakinta ma yake rawa domin bata san me zata ce ba.

“Wace ce a nan?”

“Ni ce Appa”

Ta amsa da sauri.

“Waye wannan da yake miki liki”

“Ban san shi ba Appa Wallahi”

Tana rufe baki Hajiya Kaltume ta kai mata duka a bakin da mugun karfi.

“Baki san shi ba zai zo yana zuba miki dollars haka?”

Apoa ya kalli Hajiya cikin yanayi na rashin jindadin kai hannu da ta yi ta daki Hurriya.

“Ba sai kin dake ta ba, magana ma ta isa a yanzu shata nata line zan yi”

“Ai idan ba a dake ta ba, ba zata san Annabi ya faku ba, karya da munafurci babu kalar wanda bata iya ba, ka duba yadda ta zuga Yasir ya fasawa Khairi jiki”

Appa ya daka mata tsawa da ta saka ta fashe da kuka ta ja baya tana girgiza kai.

“Waye wannan mutumen na ce?”

“Ban san shi ba Appa Wallahi ni ma yau na fara ganinsa?”

“Karya take yi Wallahi Alhaji bata san shi ba”

Hajiya ta kai kafa ta halba mata wani shuri, kamin ta janye da sauri saboda ciwon da kafar take mata har yanzu.

“Karya take munafuka baki san shi ba zai zuba miki kudi haka kuma kina zaune gashi har sunanki ake fada”

Yasir dai yana tsaye sai kallo yake baya son yayi magana Hajiya Kaltume ta rufe shi da fada, bayan kuma ga wanda ya kamata a rufe da fada nan wato Khairi.

“Ku dai duk abun da zai zubar min da mutunci ko kima a idon duniya shi kuke kokarin aikatawa? Ko soyayya zaki yi me zaki yi da mashayi? Kaltume ta fada min yaron nan yayi kaurin suna gurin iskanci da shaye shaye”

Hurriya ta saka hannu ta rufe bakinta, ta san duk wani abu da zata fada ba zai wanke ta ba, ita kan da ta sani ma ba zata tafi bikin ba.

“Sannan kuma ka ja mata kunne akan munafurci abun da take ba shi da kyau, kina hada yan'uwa fada kina sa a ciya daya mutumci a cikin mutane”

Sai a lokacin Yasir ya saka baki.

“Ni ba ita ta fada min Khairi tana wani abu a gurin ba, daukarwa kawai naje yi sai kuma na yi decide na shiga ciki, kuma idan ma Hurriya tana da laifi to laifin Khairi ne, domin ita ta shirya biki kuma Appa da ka ga irin shigar da ta yi da irin mutanen da ta tara a gurin sai ranka ya bace”

Hajiya Kaltume ta watsa masa harara.

“Ita Khairi da ka raina ba, ita meye laifinta? Birthday kawai ta yi fa, kuma ina ce Hurriya ce silar kowa ya fara yin birthday a gidan nan amman ba ayi mata fada ba sai Khairi”

Appa ya mike tsaye.

“Ban shigo nan dan ku rufe ni da ka ce na ce ba, and Hurriya ina jan kunnenki idan wani abu makamancin wannan ya sake faruwa sai na baki mamaki”

Yana kaiwa nan ya fisge wayarsa da Hajiya Kaltume ta tura masa video ya fice daga falon. Hurriya ban da aikin kuka babu abun da take yi, ta rasa ta ina zata fara wanke kanta.

“Munafuka sahibar kuka, ki yi ta rerawa mutane kuka saboda a tausaya miki a kyale ki ko? To yanzu dai kin ji abun da Alhaji ya fada idan zaki kama kanki gurin yan iskan samarin nan ki kama, idan kuma ba zaki yi ba yi, ga ki ga guri duniya ce”

“Wallahi Hajiya ban san shi ba, ni ban taba ganinsa ba”

Ba dan Yasir na tsaye gurin ba da babu abun da zai hana Khairi saka baki, sai dai tana tsoron ta yi magana ya sake rufeta da duka. Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru sai kallonsu take, Hajiya Kaltume kuma ta rufe Hurriya da fata ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, sai balbale Hurriya take da bala'i ta ko'ina kamar ita ce ta aikata abun da Khairi ta aikata. Sallama aka yi sai suka dago baga dayansu suka kalli kofar amman aka rasa wanda zai amsawa Rukayya sai Yasir dake kokarin sakin fuska.

“Rukayya”

“Na'am Yasir ya gd”

“Lafiya kalau”

Hurriyya ta tashi da sauri ta nufi kanwar mahaifiyarta ta rumgume ta da sauri tana kuka.

“Mama Rukayya kara da kika zo”

“Idan ta zo magani zata miki? Idan dai zaki canja hali ki canja domin hanyar da kika daukarwa kanki yanzu ba mai daurewa ba ce”

Hajiya Kaltume tana fada tana tabe baki, Rukayya da ke rumgume da Hurriya ta kalli Hajiya ta ce.

“Ba zan mata magani ba, amman Allah zai mata”

Yasir yayi sauri cire hannayensa aljihu.

“Rukky Please aa karki fara abun da ba halin ba”

Ta kalli Yasir sai kuma ta dauke kai ta rika hannun Hurriya suka fice daga falon, Hajiya ta bita da harara da maganganun kala kala.

“A dare kamar wannan yarinya budurwa ace bata gidansu, kuma ta shigo nan tana neman fada min magana ita marar tarbiya”

“Haba Hajiya Rukayya tana da tarbiya Wallahi dan Allah ki daina fadar haka, kuma baki san abun da ya kawota ba, be kamata ku samu tsabani da ita ba, ni zaku haifar da matsala”

Yana magana fuskarsa a raunace kamar zai yi kuka. Sannan ya bi bayansu yana jin Hajiya na jan tsaki.

A waje Hurriya sai rantsuwa take yi ma Rukayya na cewar bata san yaron ba, amman saboda shi Appa ya rufeta da fada.

“To miyasa ba zaki bude baki yi magana ba, idan kina irin wannan zaman sai kin cutar da kanki, ba zaki bude baki ki yi magana ba sai ki zauna kina kuka, ko da kina da gaskiya a rashin gaskiyar za a baki”

“Basa bari na yi magana kuma idan na fada basa yarda”

“Amman duk abun da ba halinki ba ai an san ba halinki ba ne”

“Toh sarkin masifa me kike karanta mata?”

Rukayya ta juyo ta kalli Yasir da isowarsa kenan gurin, shi ma kansa yau sai ya bata haushi saboda abun da mahaifiyarsa ta yi. Bata ce masa komai ba ta kalli Hurriya

“Daman na fito daga gidan Anty Hauwa ne na ce mai napep ya biyo ta nan zan duba ki”

Hurriya ta rike hannunta tana jin kamar ta bita amman ba hali.

“Zan sallami mai napep din sai na sauke ki gida”

“Aa na gode yanzu zan tafi”

Ta saki hannu Hurriya ta fara tafiya sai ya kirata.

“Rukky”

Ta juyo ta kalleshi.

“Na ce zan sallami mai napep zamu sauke ki gida tare da hurriya daga nan ta duba Amma”

Bata son tace masa no, kuma ta san Hurriya zata so ganin Amma domin ta dauki lokaci bata saka ta a ido ba, ko da tace zata je sai Appa ya hana saboda Hajiya Kaltume tace zuwan da take tana tafiya ne dan ta fadi karya da gaskiya.

“Tahm”

“Hurriya shiga ki dauko Hijabinki”

page 12
Ya fada sannan ya nufi gurin motarsa ya ja motar ya iso har gurin da Rukkaya take tsaye, bata shiga motar ba sai da Hurriya ta fito sanye da dogon hijab dinta har kasa, sannan ta bude ta shiga front seat Hurriya ta shiga baya, ya fara driving suka fito gate a nan ya sallami mai Napep din sannan ya ja motar suka kama hanya.

“Rukky please bana son wani abu marar dadi yana shiga tsakaninki da Hajiyata, idan ma ta fada miki wani abu marar dadi ko ta yi miki abun da bw dace ba, ki danne ina son ki dauke ta kamar mahaifiyarki, saboda ni kuma ina tunanin ina da alfarmar da zaki yi haka a gareni”

Ta hade yawu can cikin ranta take cewa Allah ya tsare ta Hajiya Kaltume ta zama uwarta.

“In Shaa Allah”

Ya kalleta yana murmushi.

“Thank you”

Ita ma ta mayar masa da murmushin daga haka be sake cewa komai ba ita ma kuma bata sake cewawa har suka isa gidan. Hurriya ce ta fara budewa ta fita motar Rukayya na kokarin fita Yasir ya shigo ya dakatarda ita.

“Ina zaki je?”

Ta masa kallon rashin fahimta.

“Gida mana...”

“Ni kuma sai ki bar ni a nan?”

Ta yi dariya.

“To ka fito mu shiga gidan bakonka ne?”

“Ki dai tsaya mu yi hira ko raina zai saki ni raina ma duk a bace yake”

“Waya bata maka rai Hurriya?”

“Idan kina son jin labari zauna”

Ta yi murmushi sannan ta dawo ta zauna ba tare da ta kalleshi ba.

Hurriya na shiga cikin gidan ta fada dakin Gwaggo da sallama da muryar dake nuna alamar kuka ta yi. Amma na jingine jikin kujera ita kadai a falon tana fuskantar tv dake falon, ta dan karkato kadan ta kalli Hurriya. Hurriya ta isa gurin sai ta kwanta saman jikinta ta fara hawaye, bata son ta fada mata abun da ya faru saboda kar ranta ya bace gashi ba magana take ba balle ta bata shawara.

“Amma na Allah ya baki lafiya, Allah ya tashi kafadunki”

Ta cikin Amma ta iya amsawa da ameen ta kwanto da kanta saman kan Hurriya ta rufe ido. Gwaggo ta fito daga dakinta tana mata maraba.

“Yau Hurriya ce a gidan nan kuma da dare, amman dai Alhaji be san kin zo nan ba ko?”

Hurriya ta dago hawaye shakaf a fuskarta ta kalli Gwaggo.

“Be sani ba, Ya Yasir na biyo zamu kawo Rukayya ne”

“Daman tace sai ta biyo ta ganki, na dauka ma can zata kawana gidan Hauwa, saboda na ga dare yayi sosai”

“Tana waje ita da Yaya Yasir, Gwaggo zo”
Chapter 47 · 0% Book details