← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 163

Sashe 58

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan na je gurin bincikenta sai wani haske ya zo ya tare yadda ba zan iya ganin komai ba sai ma na yi saurin kawar da ido saboda kar ya illata ni, kuma na duba na ga ko ta can bangaren mahaifiyarta ake mata wani abu ban ga sun mata komai ba, wata kila wannan haske ne ma ya hana Mijinki hukunta ta, na rasa gane ko minene Wallahi”

“Toh Malam ko wani lakani ta samu kuma? Shiyasa ta fara sata? Zan saka a bincike min dakinta tsab a duba ko'ina idan ma wani abun ne ta yi a dauke shi”

“Ba ita ta yi sata ba, a cikin masu aikinta ne wata ta dauka, wata yar guntuwa baka mai jiki ita ta sata, kudin da sarkar suna nan bayan dakunansu ta boye a cikin itacen fulawa”

Hajiya Kaltume ta rike baki.

“Lallai Malam ka kai Malam wannan da kudi na ne sai kawai na je na dauko kuma na kori mai aiki, amman ina.... Sai dai ma na yi addu'ar Allah ya kara bata sa'ar daukar wasu”

Malam yayi dariya yana jinjina muguntar Kaltume.

“Hajiya na lura ke ma ba ƙyale ba ce”

“Malam mutane ai sai da haka, na gode sosai sai ka ga sakona”

“Toh shikenan Hajiya sai na jiki”

Ta sauke wayar da mamaki a ranta, me Hurriya ta yi? Gashi yarinya ce balle tace ta fara shige shige kuma gashi Malam yace ba Iyami ce ta bata komai ba.

“Toh minene? Bari Khairy ta zo zan saka bincika min yarinyar nan, ni kam na san ba a banza ba Alhaji ya wanke ta a gaban mutane”

Ya cije baki ta kashe ido tana motsa kafa.

HURRIYA POV.

Tana shiga dakinta ta kalli gabas ta fadi ta yi sujadar godiya ga Allah na abun da Appa yayi mata a yau, domin ta gama katsewa ta dauka zai yarda ta aikata ne har ma yayi mata hukunci, amman sai gashi yayi abun da ba ta zata ba a yanzu. Rumgume hannayenta ta yi tana jin kamar ace Amma ko Appan Hamad suna kusa ya rumgume wani saboda jindadi. Cikin kuzari ta tashi ta fara gyara dakinta da aka yamutsa tana maida komai a yadda yake. Har ta zo kan box din da aka hargitsa da Adam ya kawo mata, takardar ciki ta fara dauka ta warware tana dubawa.

_Hey Beautiful... How are you? You're doing good i guess. Na aiko miki da wannan sakon ne just to say sorry for what happen at Mall na lura kamar baki ji dadin haka ba, i promise you ba zai sake faruwa ba matukar baki so. And duk lokacin da zaki gama karanta sakon nan ina nan waje harabar gidanku a cikin mota ba zan tafi ba ko da kuwa ko wa zai zo ya ganni_

Ta yi saurin daga kai a lokacin da ta kai gabar da yake fadar haka, sai ta nufi windows dinta gabanta na faduwa da sauri ta daga curtains din tana rike da takardar ta bude window tana kallon Motocin Momy dake gurin bata ga wata bakuwar mota ba. Ta sake maida idonta gurin takardar

_Oops... Sorry wasa nake miki na san yanzu gabanki yana nan yana faduwa, relax take a deep breath_

Ta yi taking deep breaths din kamar yadda ya bukata tana daga kanta sama ta sauke. Sannan ta sake maida idonta gurin takarsar mai kyalli da zanen heart.

_Na san kin je kin duba ko zaki ganki i fooling you_

Ta yi murmushi kadan..

_You're Smile_

Sai ta saka dariya mai sauti mai dadi.

_And you're laughing_

Ta daga kanta sama gaba daya tana dariya tare da mamakin yadda aka yi ya sani.

“Oh my God, ya aka yi ya sani?”

Ta duba karshen sakon.

_Daman muradina kenan ki yi murmushi, i just want you to be happy and healthy... Have a nice Day, ki boye teddy nan da kyau and spray that perfume, till the bottle cried out for help, and also the chocolate can't wait to be on your soft mouth_

_Adam_

“Adam”

Ta maimaita sunan kamar yadda ya ke rubuce a jikin kakardar sannan ta kalli white teddy din dake kasa, ta kalli kwalin turare da chocolate dake kasa at the same time. Gurin ta nufa ta zauna ta dauki chocolate din ta fara ci, sai gata tana lumashe ido saboda dadinsa. Ta dauki turaren ta bude ta fesa kadan tana jin kamshinsa. And his words keep rolling in her head wani be taba mata haka ba, ita da bata ma taba tsayawa da wani da sunan hira ba. Kamar an jefo mata tsawa haka gargadin Appa da yayanta ya dawo mata a rai da kuma maganar da aka fada akansa cewar ba yaron kirki ba ne. Cikin sauri ta maida komai cikin box din ta rufe ta saka shi karkashin gado.
*I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaɗar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!*

Bayan Sallah Isha'i tana kwamce dakinta, Namra ta turo kofar dakin ta shigo, Hurriya ta tashi zaune da sauri tana jiran jin abun da zata karanta mata.

“Hurriya yau ba zaki ci abinci dare ba hala?”

Ta yi shiru ta sauke kanta kasa.

“Baki jin yunwa ne?”

“Ina ji i thought kun tsane ni ne”

Ta fada shagwabe, Namra ta yi murmushi ta karasa kusa da ita ta zauna.

“Why zamu tsane ki, ko da gaske ce kina sata Hurriya ke fa jinina ce dole haka zan so ki, balle ma ba halinki ba ne daman ni ban yarda kin aikata ba, baki jidadin da naji ba a lokacin da Appa ya wanke ki, ni nafi kyautata zaton masu aikin Momy ne suka dauka ko kuma wasu daga cikin gidan nan, amman ke da ake fadar kin fi mu kyau hali a gidan nan ai ba zan yarda kin aikata ba, besides Momy tace ba zata bari ga Allah ba kin ga ko waye zai bayyana kansa, ki daina damuwa tashi muje mu ci abincin dare”

Hurriya ta sauko ganin Namra ta mike tsaye suka fita tare, suka sauka kasa a plate daya Namra ta saka musu tuwon semu da miyar yauki ta saka manshanu sosai, ta dauko ruwa ta zauna a kasa.

“Sauko mu ci”

Hurriya ta tashi ta shiga Kitchen ta wanke hannunta ta fito ta zauna kusa da Namra, a madadin ta ci abincin kai tsaye sai ta kwantar da kanta jikin Namra.

“Yaya Namra na gode, ke da Yayana kawai kuke so na a gidan nan”

Namra ta yi murmushi.

“Ba komai yar kanwata, ni wannan abun da ake cewa yan ubanci bana miki kallon haka, ina kallonki ne kamar uwa daya uba daya muke, tashi ki ci abinci”

Ta tashi ta gyara zamanta sai dai kamin ta kai hannunta cikin abinci Khairy ta shigo sanye da karamin mayafinta wayarta a hannunta, is like kamar an mata dole haka ta tsaya bakin kofar falon babu ko sallama.

“Hurriya taso muje”

Hurriya ta kalleta.

“Ina?”

“Ki taso idan zaki taso Malama”

Namra ta daga kai ta kalli Khairy da duba na wulakancin.

“Ba zata tashi ba abinci zata ci”

“Okay sannu uwarta, bari naje na fadawa Yaya uwarta ta hanata zuwa, ita ma kuma ta ce ba zata je ba”

Hurriya na jin kiran na Yayanta ta tashi tsaye da sauri zata nufi kofar.

“Dauko mayafinki Hajiya”

Ta juya ta dauko mayafin kamar yadda Khairy ta bukata, sannan ta bi bayanta suka fice, at first ta yi zaton bangaren Hajiya Kaltume za su nufa sai kuma ta ga ta nufi gate.

“Ba yaya kika ce yana kirana ba?”

“Yana waje”

Huriyya ta bi bayanta suka fita gate, close to gate din wata mota ce fake da ba ta gidan ba. Gurin motar suka nufa ta bude ma Hurriya baya.

“Shiga”

“Amman wannan ba motar Yayana ba ce... ”

“Zaki shiga ko sai ya fito ya mareki? Ba shi ya ce mu jira shi a mota ba”

Hurriya ta shiga da sauri, Khairy ta rufe bayan sannan ta bude front seat ta shiga ta zauna tana taba wayarta. After like five minutes aka bude motar ta Driver seat aka shigo, tana leken fuskarsa yana juyo ya kalleta wa zata gani ba Adam ba.

“Thank you Khary”

“This should be the last time sa zaka cilasta min fitowa da yarinyar nan”

Ta fada a kufule. Hurriya ta kalleta fuska kamar zata fashe da kuka, murya kamar a shagwabe ta ce.

“Amman yaya Khairy kin san me Appa yace ko kuma kin san Yayana zai yi fada idan ya sani”

Adam yayi saurin tarar numfashinta.

“Ba dadewa zamu yi ba Hurriya, kawai ina son na ganki ne kuma na baki hakuri abun da ya faru, and na aiko da box an baki?”

Khairy ta watsa masa wani kallo.

“Okay ni zan hana mata box din kenan?”

“Waya sani, tun da har kika iya bata ni a gurinta ai zaki iya hana ta ganin box din”

“Ni ban bata ka ba”

“And why take min kallon mutumen banza? Ni ba iskanci ne ya kawo ni gurinta ba, ki daina fada mata bad things about me, na ga ai natsantsiya ce not like you that's why i like her”

With shock Khairy take kallonsa.

“Adam what's the meaning of all this?”

“Sonta nake yi, and I'm ready to prove it, i want to talk to her parents da duk wani mai son hana alakata da ita tafiya I'm serious”

Khairy ta tsaya kallonsa for some seconds kamin ta dauke kai ta bude motar, Hurriya ma ta bude motar zata fita.

“Fita zata yi idan kika fita, ki zauna sai na gama magana da ita”

Ya fada da kamar fada yana kallon Khairy da bata fita motar ba, jin haka ya saka ta fasa fitar ta rufe motar, Hurriya kam bata tsaya ba ta fice ta tana ganin Adam ya bude motar ta ranta a na kare ta shige gida da sauri, a fusace ya dawo motar ya rufe Khairy da fada
Chapter 58 · 0% Book details