← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 163

Sashe 32

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ato... Da ma Hurriya ce wata kila na tausaya mata, amman Hamad shegen yaro. Kaji min yarinya wai ita mai zuciyar tausayi, ke idan ke aka kama waye zai yi wannan kuka? Kuma ni bana raba dayan biyu, Wallahi Kaltume zata iya sakawa a sace yaran nan saboda muguwar mata ce, yaushe ta dawo? Ta sace kanta kudin be mata ba yanzu kuma ta koma gurin yara, balle kuma ta san Hurriya Alhaji yana ji da ita, ke ma kuma idan baki kula ba sai ta saka an dawo kanki, wannan bakar matar mutuwa kawai zata yi kowa ya huta, ni daga yau ma ba zaki sake komawa makarantar ba, canja miki makaranta zan yi, kuma direba dabam zai rika kai ki yana dawowa dake”

“Amman Momy baki ga yadda Hajiya take kuka ba, haba Momy za'ayi ta sace yarta?”

“Kukan munafurci ne, ke yarinya ce baki san kan duniya ba, ni dazun da na san Captain zai zo ai ba zan ma shiga bangarenta ba, ke kuma kika ki kirana gashi har sake zuciyar ya tafi”

“Shi yace kar na kira ki na barki sai kin kare abun da zaki yi, bayan ya tambaye ni abun da ya faru”

Miwan ya zauna yana daukar katin ya duba.

“Wallahi Momy Captain yana sonki sosai if not wulakancin nan da aka yi ta masa ba zai sake dawowa ba”

“Ai nima na san haka, shiyasa nake son zage dantse na kyautata masa a bikin, ga abu dai ya matso kusa”

Daga haka suka dauko zancen bikin kamar babu ruwansu da damuwar kowa. Appa sai da ya biya unguwar Gidan Dawa ya dauko Hajiya Binta sannan ya nufi gidan Gwaggo, a mota Hurriya na kara fadawa Amma abun da ya faru tana kuka. Appa be shiga ciki ba, daga Hajiya Binta sai Hurriya suka shiga, Hajiya ta hadu ita da Gwaggo suka yi ta bata magana suna kwantar mata da hankali. Sannan taja ma Hurriya kunne kan fita waje duk kuwa da ta san Hurriya ba ma'abociyar yawo bace, daman kuma Appa yayi mata nasa jan kunne a mota.

*** *** ***

Wasa wasa aka kwashe kwana uku shiru babu Hamad da Ruma babu labarinsu, police din da aka damkawa case din kuma ba su samu wani bayani ba, sai dai suna ta kokarin zafafa bincike iya yinsu. Tun daga ranar kuma Amma bata iya bachi, dare take rayawa tana fadawa Allah bukatarka ya kare mata danta ya dawo mata da shi cikin aminci. Abinci ma Amma bata iya ci sai Gwaggo ta yi da gaske. Hurriya kuma tun daga ranar bata sake zuwa makaranta ba saboda tsoron fita da take ko kofar gidan bata yarda ta tafi, daman kuma Appa ya daukarwa yaransa hutun sati daya a school dinsu har zuwa lokacin da abun zai dan sake su. Appa ma ya yarda Hurriya ta zauna a gurin Amma ne kawai saboda Hurriyar ta zaki haka, kuma ya san hankalin Amma zai dan kwanta idan Hurriya tana kusa da ita, ba dan ransa yana so ba, domin gani yake ko a can za a iya tafi a dauki Hurriya ko Amma.

Ranar da Ruma da Hamad suka cika kwana bakwai da sacewa su aka kira wayar Appa ana neman miliyan dari na Hamad, miliyan dari na Hurriya. A ranar hankalin Appa ya tashi sosai ya nemi su hada shi da yaransa su yi magana, sai suka ce mutum daya za su ba shi wato Ruma, suka bata wayar ta yi magana da shi tana kuka sosai tana fadar sun ce za su kashe su idan ba a kawo kudi ba. Appa ya bukaci ta ba sake ba su wayar, ta mika musu suna karba Appa yace yana neman ragi sai suka jaddada masa babu abun da za su rage masa kuma idan be biya kudin da wuri ba za su kashe su. Kamin Appa ya sake cewa wani abu suka kashe wayar a take ya sake sanar da yan sanda. Bayan ya sauke wayar Hajiya Kaltume ta share hawaye ta ce.

“Alhaji ka ba su kudin nan dan Allah su sako yaran nan kar su kashe su, kana jin sun ce za su kashe su fa, mutanen nan ba su da imani ko kadan ni na san yadda suke yi ma mutane”

“Dole ai za mu nemi sassauci ai, miliyan dari biyu wasa ne?”

“Amman ai kana da su, ba su fi karfinka ba, dan Allah ka ba su kudin nan, idan ma sun maka yawa, ni zan hada da dan abun da yake hannuna ita ma Iyami a fada mata ta bada abun da take da shi a hada a karbo yaran nan”

“Aa babu kudin da zan karba, kuma idan za a fadawa Iyami sun kira ba sai kun ce mata yace zai kashe su ba”

Hajiya Kaltume ta sake fashewa da kuka.

“Alhaji kenan kana jin matar nan kamar ranka, waya ke ta tashin hankalinta a yanzu? Ni ta yara nake ba nata ba”

Appa ya mike tsaye ya fice daga falon. Hajiya Kaltume ta dauki wayarta ta fadawa Hajiya Fatee abun da ya faru tana kuka kamar ba ita ba, Hajiya Fatee sai hakuri take bata, sai da suka gama wayar sannan ta fito bangaren Appa ta dawo nata bangaren ta fadawa yaransa abun da ya faru, haka suka yi ta juya maganar suna kuka, daga karshe ta umarci Yasir ya je ya fadawa Iyami halin da ake ciki.

“Kar naje kuma Appa ya zo yana fada”

“Amman ai tana da hakkin sani, tun da danta aka sace, shi kansa be hana a fada mata ba, yace dai kar a fada mata sunce za su kashe su, fada mata mana ta hado dan abin da take da shi ni na hada a karbo yaran nan”

“Amman kudin nan be fi karfin Appa ba, kamin ku yi wannan yunkuri da dai kun ba shi lokaci ku ga abun da zai yi”

“Ni zan iya jira ba, na san yadda mutanen nan suke ba zan so ko kwana daya Ruma ta kara hannunsu ba, idan ita ba zata yi ba ni zan bada nawa a sako min yata”

Yasir ya girgiza kai.

“Gaskiya ni ba zan iya zuwa ma Amma da wannan labarin ba”

“Ina fa zaka iya, da dai ni ce da gudu zaka zo ka fada min ai”

Ta fashe da sabon kuka, Yasir ya tashi ua fice daga dakin. Yana fita Hajiya Kaltume ta kalli Maama ta ce.

“Maama shirya direba ya kaiki tafi ki fadawa Iyami yadda suka fada”

“Sai kin masa magana Hajiya kin san tun da abun nan ya faru Appa ya saka dokokin fita masu tsauri”

“Zan masa”

Hajiya Kaltume da kanta ta fita ta yi ma masu gadin magana da kuma direban. Burinta dai a fadawa Iyami abun da mutane suka ce ko da hankalinta aka daga dadi zata ji a yanzu, domin ta san hawan jinin mai ciki yana da illa sosai balle ita da take da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Sai da ta fadawa direba ya jira ta fito sannan ta fita motar Maama ta shiga gidan Gwaggo kamar a ita ba, rabon da ta je gidan ma ta manta amman a yau zata tafi ta sanar da bakin labari ga Amma. Ko da ta shiga ta samu Amma na zaune waje harabar gidan kan tabarka, hannunta yana kan Hurriya dake kwance gefenta tana bachi.

“Wa'alaikussalam”

Amma ta amsa tana kallon Maama gabanta ma faduwa, kusa da ita Maama ta zauna har da gaisheta abun da bata saba ba, domin babu mai bata girma a cikin ƴaƴan Hajiya Kaltume sai Yasir.

“Maama lafiya? Fuska ki ya nuna akwai damuwa fada min me ya faru?”

Maama ta fede mata daga biri har wutsina na abun da ya wakana tsakanin Appa da masu satar mutanen ciki har da zancen da Appa ya ce kar a fada mata cewar sun ce za su kashe su.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne abun da Amma ta iya furta idonta na cika da hawaye, furucinta yayi sanadin tashin Hurriya daga bachi ta tashi zaune da sauri ta gyara zaman gilashin idonta tana kallonsu. Gwaggo da Rukayya suka iso gurin suna jin abun da ya faru kowa ya dora hannu saman kai, Gwaggo ta daki kirji.

“Miliyan dari dari?”

“Eh shiyasa Hajiya tace ita dai zata bada abun da yake hannunta Appa ya hada ya karbo mata Ruma, domim shi Appa so yake sai ya tsaya ciniki da su, ita kuma ta ce ita kadai ta san azabar da ta sha, mutane ba su da imani”

“Miliyan dari biyu be fi karfin Alhaji ba, rayuwarsu ta fi kudin amfani idan ma kyashin badawa yake ji ni ma zan hada abun da nake da shi na ba shi, ni dai a dawo min da yarona rayuwar yarona ta fi min komai, dan Allah ki karbo min number da suka kira a hannun Alhaji zan kira na yi magana da su”

“Toh”

Bata wani dade ba ta tashi ta fice ta bar Amma da Hurriya suna ta kuka. Sai da ta fita sannan Gwaggo ta kalli Amma ta ce.

“Allah masani, amman anya babu sa hannun Hajiya Kaltume a lamarin nan? Akan me zata nuna miki ki hada kudin da yake hannunki ki bada?”

Amma ta kalli Gwaggo tana hawaye ta ce.

“Wannan rashin imanin yayi yawa, Hajiya ba zata iya aikata haka ba, idan ma zata aikata ba zata aikata tare da yarta ba, ni dai zan gada komai nawa na bada dan Allah Gwaggo karki hana ni”

“Duk da haka dai, ki saurara har ki ji ta bakin Alhaji Haruna din, zan saka Bappanku ya kira shi yayi magana da shi ko ma yaje ya same shi mu ji yadda ake ciki”

“Appan Hurriya yana da kafewa wani lokaci ni ba zan iya jira har lokacin da zai karbo su ba, Allah kadai ya san halin da Hamad yake ciki”

“Toh ke yanzu ina kika ga miliyan dari Iyami?”

“Ba za a rasa ba Gwaggo ko kudin be kai ba, akwai kaddara”

Amma na fada tana kuka ji tana kamar ta tashi yanzu yanzu ta gada kudin ta mika musu su sako mata Hamad.
Chapter 32 · 0% Book details