Sashe 111
Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Rayuwarki tana da amfani mana Hurriya karki kashe kanki”
Yayi saurin kankameta ya saka a kirjinsa.
“Ban Aikata ba Jamal ban aikata Wallahi ban aikata ba, ban aikata ba, ban aikata ba”
Shi ne abun da take ta maimaita sai ya daga kansa sama yana kallon ruwan da aka sako ba tare da hadari ba...
“Captain... Captain”
Ya bude idon a hankali har a lokacin dizzy yake gani kamin fuskar Momy ta fito masa clear, duka hannayensa biyu suna rumgume a kirjinsa dayan mai drip dayan babu.
“Sannu...”
Ya kalli wata yar'uwar mahaifinsa dake tsaye a kansa, a lokacin ne ya gane mafarki yake na rumgume Hurriya da kokarin hanata aikata kisan kan da take son yi. Maida idon yayi ya rufe zuciyarsa na wani irin fisga. Momy ta kai hannu ta taba kansa
“Jikin nasa babu zafi kuma”
“To Doctor ya kamata a kira, sun ce idan ya farka a kira su”
Cewar kanwar Momy Hajiya Ikilima, Momy ta mike tsaye tana rike da wayarta dake ringing.
“Namra ce”
Ta fada sannan ta amsa wayar
“Eh ya farka..”
“Ita ma sai yanzu ta farka”
“To yayi kyau sannu da kokari uwarta, ta farka ba dole sai kin sanar da ni ba”
Captain ya bude idon tun gabanin Momy ta yanke wayar.
“Bari na kira likita”
Momy ta fice da sauri domin kiran Likita, Hajiya Ikilima kuma ta zauna a gurin da Momy ta tashi tana kallon Captain da ya tsayar da gudun ruwan ya cire drip din hannunsa ya sauko da kafafuwansa.
“Ina zuwa? Kai da ka tashi yanzu? Hankalin kowa a tashe yake tun jiya baka farka ba sai yanzu, saboda yana asibitin sojoji ne suka hana kowa shigowa sai ni da Alhaji Usman suka bari sai kuma Hajiya Nafisa”
Be ce mata komai ba ya sauko daga kan gado sai ta mike tsaye ta rikoshi.
“Ina zaka je wai?”
Be samu amsa mata ba, Hajiya Turai ta turo kofar dakin ta shigo tare da Mijinta Engr Aliyu Turaki, Ammy ta jefar da jakarta ta rumgume Captain da sauri tana kuka sosai. Sai a lokacin ya samu kuzarin yin murmushi cikin nauyin baki ya ce
“Ammy I'm fine”
“You're not... Baka taba suma ba tun da na haife ka, kuma ka dauki lokaci baka farka ba, na tsorata da na rasa ka ban san ya zan yi ba”
Cikin kuka take maganar tun a jiya da ya kasa amsa tambayarta take cikin tashin hankali har zuwa yau da ta yi zuwan da bata shirya ba, ta dago tana shafa kansa ta taba jikinsa.
“Me yake damunka? Me kake ji?”
Yayi baya baya ya zauna yana kallon mahaifinsa da ya kasa cewa komai sai damuwa da tsantsar kulawa ke dawainiya da shi.
“Ya jikinka Jamal?”
“Na ji sauki Daddy, da ba ku zo ba ai Momy ta isa ga Momy Ikilima ma sun wadatar”
“Da ba mu zo ba, hankalinmu ba zai kwanta ba”
Daddy ya fada yana kai hannu ya taba kan Captain cikin tsananin so da kauna. Ammy ta shafa kansa da fuska tana taba ko'ina na jikinsa hawaye na sauko mata.
“Na yi waya da Dr George na saka Mustapha yayi booking appointment tun a yau, ko da ka farka ko baka farka ba zan mu fitar da kai England a duba lafiyarka”
“Ammy wannan duka na minenen? I'm”
Ta girgiza kai tana kuka sosai tana shafashi ji take kamar ta bude cikinta ta saka shi ciki ta rufe, tsoro take kar ta rasa ďa ďaya tilo da Allah ya mallaka mata iyakar zamanta a duniya.
“You're not sauran kadan ni ma na mutu a jiya, da na kira Momy ka ta zo kuma na kira abokan aikinka suka shigo suka fada min ka suma, na fi son na tabbatar da lafiyarka... ”
Yayi murmushi a kokarinsa na karfafawa iyayen nasa guiwa.
“Ba zai wuce stressed ba, kin san yanayin aikin Ammy babu hutu kullum”
“To zaka aje aikin da daga yau...”
Daddy ya fada kai tsaye da fuskar dake nuna ba da wasa yake ba, Captain yayi masa kallon mamaki.
“Is this a joke?”
“No... I have alot of money, ina da arziki ina da dukiya ina da hannayen jari dabam dabam, ina da Campany's ba daya ba, ina kasuwancin jiragen ruwa Alhamdullah... Ina da komai Jamal kai ka zabawa kanka wannan aikin ba dan ka rasa komai ba, kuma ba dan bana bukatarka a cikin kasuwanci na ba, ina da arzikin da har ka mutu ba zaka iya cinyewa ba, har jikokinka sai sun gada, fada min akan wane dalili zaka wahalar da kanka? Idan har wannan tarin duniyar bata hana ka gajiya ba da samun hutu miye amfaninta?”
Wannan karon dariya yayi mai sauti ya kama hannayen mahaifiyarsa da suke fuskarsa ya rike yana kallonta.
“Na musu alkawari ina lafiya, kuma zan kara samun wata lafiyar dan Allah ku kwantar da hankalinku”
Ya rumgume mahaifiyarsa tana kuka har lokacin. Momy Ikilima dake kallonsu gwanin sha'awa ta ce.
“Dole hankalinsu ya tashi, mu ma hankalin mu ya tashi balle kuma su? Kar ka ga laifinsu”
Ya kalleta yana murmushi kamin ya kalli Momy wanda ta dawo dakin tare da Likita.
“Hajiya Turai ashe kun iso?”
Ammy ta dago ta kalleta fa jajayen idanuwanta tana share hawaye.
“Eh mun iso Sannu da Kokari Hajiya Nafisa”
“Haba dai? Sai ka ce wata bare?”
Cewar Momy sannan ta nufi gefen gadon tana yi ma Captain ya jiki. Likitan ya duba shi da kyau sannan yayi masa sannu.
“Rashin hutu ne kawai yake damunsa, akwai bukatar ya samu ya huta kuma ya bi dokokin maganin da zamu dora shi akai da kuma shawarwari”
“In Shaa Allahu zai bi mun gode Likita”
“Allah ya bada lafiya”
Cewar Likitan sannan ya nufi kofa, Captain ya kira sunansa.
“Dr Rafiq ko zaka taimaka ka ba ni sallama yau? Idan ba haka ba iyayen nawa ba za su yarda stressed ne ba kawai, kuma ba za su bar ni na huta ba”
Likitan da aka kira da Dr Rafiq ya dawo ya dauki takardun Captain yayi rubutu akai yana murmushi.
“Zai iya bari asibitin a duk lokacin da ya so”
Sai ya fice daga dakin sannan Ammy ta girgiza kai.
“Ni ban yarda da wannan asibitin ba, ba ayi wani gwaji ba'a duba komai ba kawai ya ce ya sallameka kuma wai stressed ne, zaka je England a can za a duba lafiyarka da kyau za su gano ko minene”
“Saboda stressed din ne Ammy ko a can ne haka za su fada, ni kaina na san bana samun hutu, kuma wannan asibitin da kike gani asibiti ce mai kyau da akw kula da marar lafiya kamar a waje, asibitin Barrack ce fa, Barrack din ma babba”
“Idan haka ne me yasa ya sallame ka a yanzu? Ko da stressed din ne ai ya kamata ya rike a nan ka huta ko na kwana uku, ko dai suna son su kashe ka ne?”
“Da na musu me?”
Ya tambaya yana murmushi Momy Ikilima da Momy kuma suka yi dariya, daman sun san Ammy duk wani abun da ya shafi danta bata daukarsa da sauki bata saka wasa a ciki.
“A gida zan fi samun hutu, yanzu zan tafi na rubuta musu takardar na hada da shaidar takardun da za su tabbatar da ba ni da lafiya, na saka hannu na aje musu, Idan suka yi bincike suka tabbatar da gaskiya za su daga min kafa na kwana uku ko sati ko kuma wata, wata kila ma har shekara ya danganta da abun da likitan ya fada musu da kuma yanayin ciwon nawa da yadda suka gamsu”
“Dole sai na yi haka? Kuma dole kai zaka yi?”
“Aikin Soja ba kamar sauran aiki bane Ammy, dole na bi dokoki da ka'idodin manya kamar yadda na kasa da ni ma za su bi ni, zan iya tafi na yi yanzu?”
Permission kawai ya roka daga gurin Ammy sai ta kara masa da tukuici.
“I will escort you”
Duk yadda ya so ta zauna yaje yayi abun da ya kamata da akansa be samu haka ba, sai da Ammy ta raka danta da kanta har gurin da ya kamata shi kadai ya shiga sai da ya karya dokar ya shiga tare da ita. After ya dawo abokan aikinsa suka yi ta shigowa suna masa ya jiki, ciki har da manyansu and da yawansu sun san Engr AA Turaki wato mahaifinsa ba dan yana aikin sojan ba sai dan connection da kuma kudi mai sa asan mutum dan dole. Wasu kuma suka shigowa ne saboda Captain jindadin aikin da suke da shi da kuma kokarinsa. Momy bata bari sun fita a office din ba sai da Captain ya wanke bakinsa ya yi breakfast sannan suka fito wasu sojojin na take masa baya har gurin da aka faka manyan motocin gidansu, Daya ta Momy, daya wanda Ammy da Engr suka shigo sai kuma dayar da bodyguards din mahaifinsa suke ciki, dayar kuma ta Momy Ikilima ce. Captain ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da fargabar komai ya ce.
“Kamin mu wuce Ammy ina son muje mu duba Hurriya asibiti....”
Ammy zata yi magana Engr yayi saurin girgiza mata kai alamar kar ta hana, sai kuma ya tari numfashin mahaifiyarsa ya amsa masa.
“Okay zamu fara zuwa mu dubata tukuna sai mu tafi gida ko Family House?”
“Family House”
“Okay My Son”