Sashe 62
Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660
𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲
𝐏𝐚𝐠𝐞 1️⃣7⃣
“Be taba zuwa nan ba sai yau, kakaninmu ne guda da shi, amman su a nijar suke, sai bana Allah ya kawo shi”
Hajiya Fatee ta fada tana ta yan kama kame. Fadeel ya motsa hannunsa sai kuma ya mike tsaye ba tare da tunanin komai a ransa ba ya ce.
“Maybe da safe zamu gaisa, ni ma gida zanje yanzu, daman na fito gurin Khairy ne na biyo nan saboda akwai maganar da na so mu yi, amman zamu yi da safe”
Hajiya Fatee ta kalleshi tana murmushi.
“Okay Allah ya maka albarka”
“Sai da safe Hajiya”
“Allah tashemu lafiya”
Ya nufi kofar fita ta bude ya fice, sai da Hajiya ta leka ta ga motarsa ta bar gurin sannan ta tashi a fusace ta shiga dakinta.
“Haba Malam haba na fada maka kwana gidan nan ba zai yiyu ba, ka ce dole sai an yi haka saboda Aljanin da dare zai zo, kuma na fada maka karka fita daga dakin nan idan kana neman wani abu ka fada min zan dauko maka, saboda gudun irin haka, kullum dana sai ya zo da safe ko dare ya gaishe ni, yanzu ba dan yana da zuciya mai kyau ba ai sai ya wani tunanin ya zo masa”
Malam yayi yar dariya mai cike da tsoro abun ka da bakauye.
“Hajiya ban san cewa danki zai zo ba, ni ma kawai na so na fita na dan zagaya ta can baya ne akwai abubuwan da zan karanta saboda kiran rauhanai”
“Kuma ina ta kiranka ka fito mu gaisa baka fito ba, bayan na masa karyar cewa kai dan'uwana ne”
“Akwai dalilin da ya saka, amman karki damu danki ai wata rana zai ganin har sai ya gaji da gani na”
Kallon rashin fahimta ta yi masa.
“Kamar ya? Ai bana fatar haka, Malam bayan wannan za su sake neman wani abu ne?”
“Aa ba za su sake neman komai ba, yanzu din ma, ai shegen kwadayi ne da son mata irin na manyan aljannu, kin san yadda farar mace take da daukar ido ko tsohuwa ce balle ke da ba za ace kin yi shekarunki ba, shiyasa kullum ake fada muku ku rika rufe jikinku amman baku ji”
Ta sauke ajiyar zuciya, ranta bakikirin kamar an mata bushara da mutuwa.
“Abubuwan sun yi yawa Malam, bana fatan sake aikata komai bayan wannan, tun bayan rabuwata da miji wani abu be sake shiga tsakanina da kowa ba, sai da kaddara nan ta fada min yara kanana suka ci mutunci, duk shi ne silar wannan bakincikin”
“Karki damu Hajiya, daman tuntuna saboda kin dauki lokaci ne da tuni ma an wuce gurin, gashi har cikin ya kara satika, amman har yanzu ba mu makara ba. Amman Hajiya na yi miki wata tambaya mana, miye sa ba zaki yi aure ba, wato a lokacin da ina zurfafa bincike a kanki sai na hango maza da yawa da suke kaunarki, kina da wannan kwarjin na hallita”
A kaikaice ta kalleshi kallon da ya fi kama da harara.
“Miya kawo wannan maganar Malam? Ina ruwanka da rayuwata ko aurena? Samun gurin har ya kai haka?”
“Karki manta dai da Malam kike magana, kuma ina son na fada miki babu mai iya miki irin aikin da zan miki duk garin nan, ki ga aiki kamar yankan wuka, ai kin yi ta sake sake shi ya dauke ki lokaci, da kika ga babu mafita ne kika kirana kika ce kin amince, ina bibiyar duk wanda nake yi ma aiki, ina ganin duk halin da suke ciki”
Ta rufe zancen da rufe kwalbar turare mai tsananin karfi, irin mai hawan kanka ya tashi mai aljannu. Hajiya Fatee ta mike tsaye daga kan gadonta da take zaune ta kalli Malam dake zaune a kasa ta ce.
“Malam ina ganin kamata yayi ka koma dakin baki dake waje, idan dare ya kara yi zan zo da kaina, daman saboda gudun dana ko masu aikin gidan su ganka ne, kuma yanzu na samu mafitar hakan tun da har na yi ma dana karyar kai dan'uwana ne”
“Hajiya ai duk yadda kika ce haka za'ayi, rufin asirin na ki ne ba nawa ba”
Ya mike tsaye.
“Sai ki min jagora zuwa dakin bakin, ni ma hankalina zai fi kwanciya da haka”
Komawa ta yi ta zauna yayinda yake tsaye yana jiran ta wuce gaba ta nuna masa dakin, sai ta dafe kanta tana jin kamar ta fashe da kuka, abun duniya duk ua isheta, idan tace zata bar cikin,tonuwar asirinta ne gashi har ya fara tasowa dan lokacin data dauka bata mayar masa da amsar ta aminci ko akasin haka ba.
HURRIYA POV.
Kallo daya ta yi ma Appa ta san ba lafiya ba, domin fuskarsa a hade take kamar be taba dariya ba.
“Appa barka da dare”
Appa ya duba duban dake kara bayyana bacin ransa.
“Karata kika kao Hurriya?”
Ta nuna kamta.
“Ni...”
Hajiya Kaltume ta yi karaf ta ce.
“Aa ba ke ba shi.. Tun da kin raina mutane”
Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume da sauri domin kalamanta suna kara rudata ne kawai.
“Tafiya kike gida gida kina fadar na ki na saka ki makaranta?”
Ta fiddo ido kamar za su fasa gilashin dake fuskarta su fito.
“Ni Appa Wallahi ban yi haka ba, ya za'ayi na yi haka?”
“Toh waya je ya fada? Da Magariba nan Alhaji Garba ya same ni da zancen yana neman izini yana son ya nema miki makaranta, na gaza ne Hurriya?”
Tana jin Alhaji Garba ta san makocinsu ne kuma mahaifin kawarta Husna. A take idonta ya cika da kwalla.
“Wallahi Appa, ban ce ka gaza ba, ban fada mata cewar ka ce ba zaka saka ni makaranta ba, ni ban yi magana da Babanta ko mamanta ba, Appa Wallahi ban kai kararka gurin kowa ba”
Appa ya zaburo mata kamar zai kai mata duka.
“Idan baki fada ta ina suka ji cewar baki zuwa makaranta? Har zai same ni da zancen wai yana son ya sakaki makaranta baya bukatar sisina umarni kawai yake so, idan ba kin je ki fadi wani abun ba ta ina zai sameni da wannan maganar? Dukan sauran yaran babu wanda yayi wannan sai ke Hurriya?”
Hajiya Kaltume ta tabe baki.
“Ai ita dai Hurriya kamar tafiyar Iyami take jira, duk ta bi ta lalace abubuwa take marasa kan gado, Allah ya tsaremu karki kwaso mana abun magana nan gaba”
Cikin kuka Hurriya ta girgiza kai.
“Appa ka ce ka san halina, ba zan aikata maka irin wannan ba, ni dai na san na yi hira da Husna kawai akan karatuna, kuma ban ce mata ka kasa sakani makaranta ba, Wallahi Appa ban fada ba”
“Kullum ana fada min abubuwan da kike yi Hurriya, yaron nan ma da na rabaki da shi baki ji ba, an fada min har kyauta yake kawo miki, kuma yana zuwa kina fita hira da shi, yanzu kuma abun ya fara tsallakawa makota, to sai ki tashi ki tafi can gidan kawar ta ki ya hada ke da ita ya rike, makaranta kuma ba zan saka ki ba, ke da karatu har abada, sai dai ki ganina gurin wasu, sannan ban yarda kowa ya saka ki, sai na gani idan da karfi zaki yi karatu, babu wanda zai saka ki makaranta da yawun bakina, idan ke zaki saka kanki Bismillahi”
Hurriya ta tashi da sauri ta isa har gurin da Appa yake zaune ta rike kafarsa tana kuka.
“Appa ba ni da gata a duniyar nan sai Allah sai kai, na karbi laifina dan Allah ka yi hakuri”
“O tooo kin aikata kenan, daman na san kin yi ai, domin babu wanda zai fitar da sirrin gidan nan sai ke, kullum kina can gurin wannan Husnar ana zagina da yayana ana fadar cin amanarki matan ubanki suke, Momy ma da take rike dake bata tsira ba, balle kuma ni da kika maida abokiyar gabarki, ban da rashin hankali da tunani irin naki ta ina zaki zauna kina zagin ubanki da kawarki har mahaifinta yayi tsaurin ido ya tinkari Alhaji da wannan maganar”
Hajiya Kaltume ta fada, Hurriya ta girgiza kai da sauri, amman ta kasa magana. Kalamanta sai suka kara tunzara Appa ransa ya kara baci.
“Na fada miki, ki hada komai baki ki koma can gidansu ki zauna”
Hajiya Kaltume ta daga masa hannu.
“aa Alhaji ba za'ayi haka ba, ai sai ka kasa su kara zaginka kuma, mu ma kuma ace muna gani aka koreta, daman dai ta bata maka suna a unguwar nan, kai ne dai baka sani ba saboda sai yau Alhaji Garba ya same ka da wannan maganar, amman zance kala kala ni na ji, Nafisa ma ta ji, kawai dai muna shakkar fada maka ne saboda baka yarda da komai aka fada maka na Hurriya, duk da haka dai ba zan ce ka koreta ba domin bata gidan da ya fi wannan”
Hurriya ta kalleta tana kuka.
“Haba Hajiya ki ji tsoron Allah ki rika fadar gaskiya, bana zuwa ko'ina sai gidansu Husna ita ma ba kullum ba, Wallahi ban taba zaunawa wani guri na zagi Appana ba...”
Hajiya Kaltume ta rufe baki.
“Laa ke ni da nake miki yaki saboda kar ya koreki, shi ne zaki dubi idona ki ce na ji tsoron Allah na fadi gaskiya, to da can tsoronki nake ji ne? Alhaji ka ji min wata magana?”
Appa ya mike tsaye yana kokarin fisge kafarsa, domin ransa a matukar bace yake, Hurriya kuma ta kara rike kafar har sai da ya dago fuskarta ya dauketa da mari.
“Ba zaki sake min kafa ba, ki tafi can gurin wanda kika dauka ubanki ki zauna a gidansa, kuma daga yau sai yau ban yafe miki ba idan kika sake furta wata kalma marar dadi akan Hajiya”
“Ba zan saka bakina ba, kar ki rufe ni da duka”