← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 163

Sashe 53

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi dariya dake kara tabbatar da gaskiyar abun da yake fada.

“Hajiya kenan ai suma suna son mata sosai fiye da yadda maza bil'adam suke son mata, shiyasa suke auren matan hausawa”

A take hankalin Hajiya Fatee ya kara tashi.

“Malam ni ai ka kara firgita ni, ni ba yarinya ba balle ace sun ga wani abu a jikina ya burgesu”

“Ko tsohuwa ce ke babu ruwansu matukar kin yi musu, balle ke Hajiya jikinki ma ba za'ace kin yi shekarunki ba ga ki fara kin san aljannu suna son farar mace, dan haka ki natsu ki yi shawara da zuciyarki, kuma karki kuskura ki fadawa kowa domin suna nan tare da ke kuma sun ce basa son magana, saboda haka ki yi shawara da zuciyarki duk abun da ta yanke miki sai ki yi amfani da shi, amman lallai kin ji abun da suke bukata”

“Amman Malam ba za'a iya ba su wani abun ba su hakura?”

“Babu wani abu da suke so sai abun da na gabatar miki, wato abun da baki sani ba shi ne, kamin na same ki da maganar nan sai da na yi ta lallaba su amman ina suka ki yarda, dama na san zaki tsorata ai amman ina son ki kwantar da hankalinki ba wai zai zo miki a mutum ba ne, a cikin jikina zai shiga, kuma babu wani abu nawa da zaki ga ya canja, ni zaki gani a zahiri amman a badini ba ni ba ne Aljanine”

“Shi ke nan Malam zan yi shawara”

Ta sauke wayar cikin tashin hankali, ta rasa ta ina ma zata fara tunani, anya aljannu ke bukatar haka ko kuma Malam? Ta ina aljannu zasu ce sai sun shiga a jikin wani za su kwanta da ita, har ta fara lalaben number Hajiya Kaltume sai kuma ta tuna ya ce mata aljannun sun ce basa son magana.

“Kai.... Kai.... Kai... Wannan bala'i da me yayi kama? Wannan tashin hankali duk na minene? Abun da ban yi kurciya ba zan yi yanzu? Haka ina ji ina gani yara kanana suka keya min rigar mutunci, yanzu kuma ga wata sabuwar matsalar ta fuskanto ni, karshenta kuma idan ban amince ba zai ce cikin nan bayyana zai yi idan kuma haka ta faru ya zan yi da duniya”

Ta fashe da kuka sosai ta sauko kasa ta zauna tana kuka har wani gurnanin ke fita.

“Wanna yarinya Afrah kin cuceni ba dan ke ba da ban san kofar gidan ko wane malami ba, da yanzu duk wannan bala'in be same ni, saboda ke dan abun da Alhaji ya bar min duk ya kare, kuma ban samu biyan bukata ba, ko da Matsalar ba taki ce ke kadai ba, tun da zuwan na Kaltume ne, kuma ita ba a mata komai ba, gashi ta samu biyan bukata ni kuma ina cikin bala'i”

Kuka take sosai tana kara jin tsanar surukarta a cikin ranta, kuka ta yi sosai har sai da idonta ya kumbura bakinciki ya hade mata, idan cikin bayyana babu wanda zai yarda a daji ta samo shi, domin shekara uku yanzu da faruwar abun, sannan kuma bata san abun da zata fadawa danta da yan'uwanta ba, gashi kuma ba zata iya amincewa da bukatar Aljannu Malam ba, idan ta tuna da fason dake kafarsa ma sai ta ji kamar zata yi amai balle kuma ace ta kwanta gado daya da shi, bakauyen da gora ya gama yi ma fenti a hakora, mutumen da be wuce zama mai gadin gidanta ba. Har aka kira Isha'i kuka take ko da ta hakura idan ta tuna sai ta ji kukan ya dawo mata, ita ba da samun nasara ba ita da kwasar ciki ga kuma bukatar Malam a yanzu, da zuciyarta take shawara ko dai ta kyaleshi ta nemi wani Malamin ne, ta wani bangaren kuma tana ganin kamar kamin ta samu Malamin da zai iya kwantar mata da cikin kamar yadda wannan yayi abu ne mai wahala kuma bata san sherin da zai iya binta da shi ba, ta kuma san cikin ba zai cire a yanzu ba a lokacin da yake wata uku ma aka fada mata akwai matsala a zubarwa bayan kuma ta sha magani be zube ba balle kuma yanzu da ciki ya sha kwanci shekara uku. Carbin dake hannunta kawai take ja ta rasa ma ta ina zata fara, salati zata yi ko tasbihi ko istigifara gaba daya ta rasa abun kamawa sai kuka kawai take tana juya carbin.

“Sallamu Alaikum”

Ta yi gaggawar kawar da fuskarta ba tare da ta amsa sallamar ba, sai dai haka be hana danta Fadeel fahimtar kuka take ba, ya fahimci fushi take dashi domin dazun da ya shigo gaisheta da safe bata amsa masa ba.

“Subhanallahi Hajiya Lafiya”

Ya fada bayan ya zauna a gefenta yana kallonta damuwar dake tattare da shi ta gagara boyuwa. Kamar mai nema sai kawai ta fashe da kuka, abun yana cinta a rai kuma bata isa ta yi labarin da kowa ba, domin babu wanda ya san komai sai aminiyarta Kaltume, ko da zata fadawa kowa a duniya ba zata yi gangancin fadawa Fadeel ba, tana jin kamar ace abun da zata iya fitarwa ne ta tattauna amman babu hali.

“Allah yasa ba ni ne silar zubar hawayen nan ba Hajiya”

Ta kara kawar da kai ta tsakaiga kukan ta share hawayenta, sai dai bata yarda ta kalli gefen da yake ba ma, hakan kuma sai ya kara daga masa hankali.

“Hajiya... Ki yi hakuri dan Allah idan ni na bata miki”

“Fadi ba shi da amfani domin na sha fada babu abun da ya canja, amman dai zan baka zabi uku a yanzu, Fadeel ko dai ka saki Afrah, ko ka kara aure, ko kuma na yafeka yafewa ta har abada...!”

Be san lokacin da jikinsa ya saki ba yayi nauyi a gurin.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Hajiya ta tabbata dai saboda da ni kike zubar da hawayen nan. Hajiya ina son matata sosai domin ina jindadin zama da ita, amman Wallahi zan iya rabuwa da Afrah matukar hakan ne burinki, kuma zan kara aure idan har hakan zai saka ki farinciki, amman ba zan iya hakura da ke ba, ba zan yarda ki yafe ni ba, ba nida wani abu da ya fi ki muhimmanci a duniyar nan, gaisuwar da na yi miki dazun ma na tafi baki amsa min ba, ban wuni cikin farinciki ba”

Ya sauke ajiyar zuciya ya sauke kansa kasa.

“Na ji dadin da kika saukaka min kika ba ni zabi har uku, kuma na zabi na uku zan kara aure kuma na miki alkawari matar da kike so ita zan aura, Allah ya huci zuciyarki”

Ya mike tsaye yana fadin.

“Zan tafi Allah ya tashe mu lafiya”

Har ya fice bata juya ta kalli inda yake ba, bata jin tana da wata makiyiya a yanzu fiye da Afrah, saboda tana ganin saboda ita danta baya mata biyayya kuma ya canja mata. Ada can baya kamin Fadeel yayi aure shi din Mommy's Boy ne kullum yana gida ba shi da abokin hira sai ita, komai zai yi sai ya fada mata tufafi ma ita take bashi shawarar wadanda zai saka, a gidanta yake zaune. Sai dai yana haduwa ya Afrah sai ya fara canja mata, bayan kuma ya guji matar da ta so ya aura da farko, har ta kai ya kasa zama a gidan kamar yadda ta bukata saboda Afrah ta nuna masa ta fi sha'awar zama a gidanta ita kadai ba dole sai a gidan mahaifinsa ba kamar yadda Hajiya Fatee take so, shi ma kuma da yayi tunani sai ya yarda da shawararta, yana yin auren sai rayuwarsa ta koma gaba daya a gidan matarsa, zabin tufafinbda zai saka wasa da dariya ko wani abun na rayuwa da matarsa yake ba da ita ba, idan ma zai nemi shawararta sai idan wani abun ne da ya shafeta ko kuma yake da muhimmanci sosai, idan zai siya mata tufafi zai dauki Afrah su tafi tare Afrah ta zaba mata tufafi mai kyau mai tsada su kawo mata, sai dai hakan baya kara komai sai wutar kiyayyar Afrah a zuciyarta, duk kuwa da kasancewar tana kyautata mata. Wannan ya saka ta fara zagon kasa tana son ya saki matarsa shi kuma ya nuna mata yana sonta sosai, kuma idan ya rabu da ita ba shi da mai rike masa yaransa.

Cikin matukar damuwa Fadeel ya isa gidansa, ya samu kansa da zama a cikin motar ya kasa budewa ya fita, shi dai a ra'ayin kansa ba shi da burin aure mace fiye da daya saboda baya son tashin hankali kuma yana son matarsa tana sonsa, ya yanzu ma yana cikin tashin hankalin rashin jituwar da suke samu da Hajiyarsa ina ga ya kara aure, and all this love da biyayya da Afrah take masa ya rasa da me zai saka mata sai kishiya. Jin yayi ana kwankwasa kofar motar yana daga kai sai yayi arba da annurin zuciyarsa tana aiko masa da murmushi. Ta tsaba ado kamar Sequence Wax din da ya siya mata a gurin Khadeeja Candy ta karbi jikinta sai kyali take kamar an wantsa mata gold. Ya sauke gilashin motar

“Madam”

“Yallabai yau lafiya kake kuwa”

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya bude motar ya fito ya rufe.

“Habibina fada min me yake damunka daman tun jiya na lura da haka, me ke damunka?”

Sai da ya kasa bakinsa sau biyu sannan ya iya aje numfashi a muhallinsa.

“Afrah yau na ga Hajiya a cikin wani hali da ban taba ganinta ba, ban san wata rana da Hajiya ta zubar da hawaye saboda da ni ba, sai na ranar da aka daura aurena shi amman na farinciki ne yau kuma akasinsa ne”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, me ka aikata haka wanda ya bata mata rai Abban Aiman?”

Yayi shiru yana kallonta ba tare da ya amsa mata ba, tana ganin haka ta san inda matsalar take kuma bata bukatar karin bayani, a take zuciyarta ta fara bugawa.
Chapter 53 · 0% Book details