← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 163

Sashe 64

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kin yi tunani da baki tafi gidan Iyami a wannan yanayin ba, sai abun ya kara mata yawa a zuciya, idan ma zaki fada mata sai ki ce mata ni na dawo da ke nan gurina”

“Shiyasa na taho nan ai”

“Kim kyauta daman ina neman abokiyar zama, shi kuma Allah ya warware masa duk wani abu da yake cikin kansa, gaba daya an juye masa hankali ya canja kamar ba shi ba, gidan nan ma sai ya dauki wata uku biyu be zo ba, kiran waya kuma sai idan na kira shi, babu ruwansa da kowa sai Kaltume, gaba daya ta dauke masa hankali sai abun da tace yake yi”

“Kuma ni ban ce Babanta yayi masa magana ba fa Hajiya, ni ban yadda aka yi ma Babanta ya ji ba”

“Wata kila tana tausaya miki ne, sai ta aika hakan da kyakkyawar niya, shi kuma ya kasa fahimtar abun, daman kowaye zai ji haushi amman be kamata idonsa ya rufe har haka ba, maraicinki ya kamata ya duba, yanzu da baki da ni ko baki da uwa a raye sai dai ki koma wani gurin rabe gurin yan'uwa ko kuma wadanda baki hada komai da su ba?”

Ta kara gyara kwanciyarta jikin Hajiya.

“Allah ma yasa ina da ke”

Hajiya Binta ta yi murmushin dake kara bayyana tsufanta, ta shafa kan Hurriya.

“Kar Allah ya raba mu har sai na damkaki ga miji mai amana Hurriya”

“Ameen”

Ta amsa tare da rufe idonta tana dariya.

“Ja'irar yarinya wato har da cewa Amin ko?”

Ta saka dariya sosai sannan ta tashi ta dauke kayan ta shiga da su dakin Hajiya.

“Aa daki dabam zamu yi, wake zama da kishiya daki daya”

“Dole ne ki yi hakuri da ni Hajiya daki daya zamu zauna”

“Toh aje kayan ki fito ki ci abinci, na san cikin nan naki yana nan dauke da yunwa”

Kusa da gadon Hajiya Binta Hurriya ta aje luggage dinta sannan ta cire hijab dinta ta jefa saman gado ta juyo ta fito.

“Hajiya me aka dafa miki?”

“Zai wuce tuwo ne Hurriya kin san abincin tsufi ai ba kamar ku ba, idan ma baki son tuwon ki shiga Kitchen ki dafa indomie”

“Toh”

Ta amsa sannan ta nufi hanyar Kitchen din, tun da ta shiga bata fito ba har sai da Indomie dinta ta dahu ta zuba a plate ta dauko ta fito. Aje plate dinta yayi daidai da shigowar Yasir falon hankalinsa a tashe yana ganinta ya dafa zuciyarsa ya nemi guri ya zauna.

“Kin daga mana hankali, na je gidan Amma baki can, na dawo gidansu Husna aka ce baki zo ba, na dauka wani gurin kika tafi”

“Allah yasa dai baka dagawa Iyami hankali ba, domin ba su san abun da ya faru ba”

“No naje gurin ne in a code way, ban fada musu abun da ya faru ba”

“Dadina da kai ai akwai hankali, ka kyauta”

Hurriya ta dube shi.

“Yaya ina wuni?”

“lafiya kalau shi ne kika kama hanya kika taho a madadin ki kirani”

“Yaya ko na kiraka Appa ba zai saurara ba saboda ransa ya bace sosai, kuma ba ni da wayar da zan kiraka ma”

“Duk gidan nan ki rasa wayar da zaki dauka ki kirani?”

Hajiya Binta ta shiga tsakani ganin kamar Yasir yana neman mada abun fitina.

“Aa ba haka ba ne, ita kanta bata cikin hayyacinta a lokacin da ta baro gidan saboda tashin hankali, ta ina zata tsaya neman wayarka ma, kuma kana jin tana fadar cewar yayi fushi ba zai saurara ba”

“Tsohuwa kokari kareta kawai kike yi, amman  da ta kira ni ai ba zata baro gidan ba, yanzu da wani abun ya sameta fa”

“Laifin waye ba na mahaifinka ba? Akan me zai korota a dare yace ta tafi ta bar masa gida kamar wadda ta yi cikin shege”

“Ita ma tana da laifi ai, Hajiya ta fada min duk abun da ya faru ba zai yiyu ka zauna ka yi ta fadawa kawa karya da gaskiya ba, gashi yanzu har mahaifinta ta dauko kafa ya zo ma Appa da wani zancen banza”

Hajiya ta tabe baki.

“Uwarka kuma dai ai ba zata fada maka gaskiya ba, karya da gaskiya zata hada ta fada maka saboda ka yarda da ita ta karyarta Hurriya ka san sai ba son Hurriya suke ba”

“Haba Hajiya wace irin magana ce wannan? Wannan ai hadin fada ne, sai ki hada Hurriya da Hajiya ta dauka ko gaske ne”

“Yasir kai ma kasani da Khairiyyah ce ko Salma ko Rumana aka kora a gidan nan kana ganin Kaltume zata yarda ta fito a dare kamar wannan?”

“Sai da na yi mata magana tace min ita ma bata san fitar Hurriya ba”

Hajiya ta tabe baki, Hurriya kuma tana cin indomie ziri ziri. Yasir ya mike tsaye ko da ace Hajiya Kaltume karya ta fada masa ba zai so ya zauna a gurin da ake zagin mahaifiytarsa ba, domin komai lalacewarta mahaifiyarsa ce.

“Alhamdulillah tun da tana nan, ni zan tafi idan Appa ya huce sai na dawo na dauketa”

“Toh a gaishe da gida”

Hajiya Binta ta fada tana raka shi da kallo, Hurriya ma ta dago kai ta kalleshi.

“Yaya sai da safe”

“Sai da safe”

Ya amsa ba tare da ya juyo ba.

“Ina zata fada maka gaskiya, wannan Kaltume ba baki na yi mata ba, amman da wahala ta gama lafiya”

Hajiya ta fada bayan ya fice. Hurriya dai bata ce komai ba, ta cire hannunta daga taliyar tana kallon wani gafen na dabam, zuciyarta na raya mata yayanta ma yayi fushi da ita a yanzu.

WASHE GARI....

_Barka da safiya Namra, fatar kin tashi lafiya ya su Mama da Daddy, And my beautiful Young Lady, hope kowa yana kalau, a mika min gaisuwa gurin gimbiyar please_

Ta aje wayar a hankali bayan ta gama karanta sakon ta manhajar whatsapp dinta, sai ta nufi windows dinta ta bude curtains din tana kallon kasan bene zuciyarta na gabato mata da wani abu na rashin dadi da bata san dalilinsa ba.
Me yasa zata ji haka, shi ne abun da ya fara zuwa mata a rai, daman ai be ce yana sonta ba balle har tace ya koma gurin kanwarta ne. But at first alamunsa sun nuna ni yake so. Wata zuciyar ta fada mata. Ta kai hannunta tana taba karamar sarkar dake wuyanta.
Yana yawan tambayar Hurriya, amman ban yi zaton ita yake so ba, ko kuma dai ya juya kanta ne saboda ya ga ta fini kyau. Sai kuma ta juyo tana kallon dakin kamar wani bakonta sai sake sake take a ranta, wai it's normal ya so Hurriya domin be furta mata so kai tsaye ba, but why take jin babu dadi so disappointed? It's because of ta fara sabawa da shi kwana biyu, the way he approached her gashi da saka nishadi da iya kula da aika ko kuma saboda tana tsamanin ita zai ce yana so.

Ta bar jikin windows din ta nufi gurin da ta aje ledar da ya kawo ma Hurriya ta bude ledar ta ciro waya tana dubawa irin wyar Momy ce sak daga kala har model. Ta sake saka hannu cikin ledar ta ciro Perfume set masu kamshi sosai. Sai da ta shaka turare sannan ya maida komai yadda yake, ta nufi wayarta ta dauka. Ta rubuta masa.
_Bata karbi komai ba, na yi try bata karba ba, tace na aje maka_

After ta yi sending sakon sai kuma ta ga kamar be dace ta yi haka ba, but me zata yi? Ta karba da sunan Hurriya ta karba, yayi ta jiran kiran Hurriya ya ga shiru, ai kara ta fada masa gaskiya, ta jefar da wayar a kan gado tsakanin faduwar wayar da shigowar kiran Salim ba za a iya fadar wanda ya riga wani ba. Hannu ta kai ta dauka ta danna picking

“Are you free mu yi magana?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa masa.

“Eh ina jinka”

“Me yasa bata karba ba?”

Ta daga kafadunta kamar ance nata yana tsaye gabanta yana kallonta.

“Ban sani ba, maybe she's not interested, kuma bata shirya ma hakan ba, domin wani be taba nuna yana som Hurriya ba, so ina tunanin ba abu ne mai sauki ta karbi abun ba, saboda tana da banbanci da mu, tana ganin abubuwan differently”

“Amman da kika fada mata ya kika ga reaction dinta?”

“Not good... Not Bad...”

“How do you think zan iya shawo kanta”

Ta taka zuwa gaba tana shafa goshinta.

“Ina ganin kamar ba a takurawa mutum akan soyayya she's 19yrs idan tana ra'ayinka zata sani”

“Or Maybe i can talk to her by myself? Ya kika gani na fahimtar da ita abun da ke zuciyata kuma na nuna mata ba da wasa na zo nan ba, ko kuma kina ganin sai mun fara daukar permission gurin iyaye? Maybe ita ma zata fi yarda da ni”

Ta yi shiru kamar mai tunani.

“Karka yi saurin tafiya gurin iyaye, ka fara magana da ita ka ji ta bakinta, domin Appanmu baya daukar komai da wasa”

“Okay zan yi haka, zan shigo yau da dare ko na zo yanzu”

Ya lumshe ido ta bude jin yadda yake rawar jiki.

“Da dare zai fi sirri, domin bata nan jiya ta koma gurin kakarmu da zama, zan kwatanta maka gurin”

“Zan fi jin natsuwa idan muka tafi tare, and Kakarta ma zata fi daukar abun da muhimmanci, idan kina ganin babu matsala zan fara zuwa na dauke ki sai mu tafi tare”

Samun kanta ta yi ta saka bijirewa rokonsa, duk kuwa da zuciyarta ta raya mata haka, domin tana son ta cire kanta ne daga duk wani abu da ya shafe shi a yanzu saboda ya nuna ba ita yake ra'ayi ba.

“Shikenan Allah ya kaimu”

“Ameen thank you”
Chapter 64 · 0% Book details