Sashe 157
Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yasir ya rika shi ya zauna yana girgiza mai shi ma abun ya daure masa kai, ya san be rage Hajiya Kaltume da komai ba, akan wane dalili zata azantar da kanka ta azabtar da shi kuma ta bi ta yayansa da matarsa? Ta wani bangaren kuma yana ganin laifin ba nata ba ne nashi ne saboda be rike addu'a ba tun farko, kuma be tsaya ya zabo mai addini ba da bata so ta masa wannan aika aikarba a gidansa. Hankalinsa be kara tashi ba sai da ya shiga da kansa ya duba halin da Hajiya Kaltume take ciki, a nan ya tabbatar da abun da dansa ya fada masa yan'uwanta kuma suka bukaci tafiya da ita gida a tare da su, Appa ua daga hannunsa sama yace ba su bukatar umarninsa domin ba aurenta yake a yanzu ba. Momy da Namra sai suka shigo suna kallonta a lokacin da labarin ya isa kunensu, Momy wani sabon tsoron Allah ya kamata daman can ta san Kaltume zata iya aikata fin haka ma, amman ba ta yi zaton da hannunta dumu dumu a satar Hamad ba, a nan ta gane ita kanta Allah ne kadai ya tsare wata kila ita din ma ta an sace mata Namra ko Miwan ko Musib.
Ta bangaren Iyami ma haka ta kasance cikin mamaki ta tashin hankali a lokacin da Appa ya sanar mata halin da Kaltume take ciki, sai ta fashe da kuka tana mamakin tsananin kiyayya da zafin kishi da zai saka mace aikata irin wadannan munanan abubuwan, daman can sun yi tsammanin da hannu a cikin lamarin saboda yadda ta nuna bata damu ba kuma yake nunawa yaran kiyaya ta zahiri. Hakan sai ya kara sanyaya guiwar Amma dake shirye shiryen tarewa a gidan Appa, duk kuwa da ta ji cewar a yanzu Hajiya Kaltume bata cikin hayyacinta, kuma ita ma ta rike addu'a da tsarin jiki ba kamar da can ba, ta wani bangaren Gwaggo da Iyami suna ganin kamar Hajiya Kaltume ta yi haukan karya ne saboda ta san asirinta yana daf da tonuwa. Faruwar hakan ya sakawa Amma yarda cewar yaron da zai baro Ethiopia tare da Hurriya da surukinta da kanwarta lallai danta ne wata kila Allah ya raya shi ne saboda zuwan wannan ranar da asirin Kaltume zai tonu, domin wani abun tun a duniya yake bayyana. Ba sai an je ba, lahira karbar sakamako ne kawai da sanin makoma.
HURRIYA POV.
Cikin tsoro Mama Rukayya take kallon Hamad da ke zaune a masaukinsu, Hurriya na zaune a kusa da shi tana kuka shi kuma yana hawaye.
“Taya wai za ace wanna Hamad ne ni fa ban gane ba..”
“To ke da kika san kan labarin kenan balle ni da ban san komai akai ba”
Cewar Momy Ikilima. Captain ya dan dago ya kallesu kamin ya dauke kai ya cigaba da amsa wayar Appa.
“Hakan nake tunanin zai fi, sai mu dunguma gaba daya mu dawo tare, saboda bana son karatun nasa ya samu matsala ka san su nan sai da doka suke komai ba kamar kasarmu ba”
“Shikenan za'ayi haka, zan kira ka duk yadda ake ciki”
“Na gode Appa...”
Ya sauke wayar ya kalli Hamad.
“Hawayenka su suke saka yar'uwarka kuka kuma kasan yadda idonta yake”
Hamad ya kalleta sai ya mike tsaye da sauri Hurriya ta rike hannunsa ganin take kamar idan ya fita ba zai sake dawowa ba.
“Dan Allah karka tafi..”
“Hurriyana sake ki babu inda zai je tare zamu koma nigeria, na yi magana da Appa zai yi magana da jami'an tsaron can a matsayinsa na Mahaifin Hamad sai su aiko da takarda zuwa ga Ambassador Nigeria da yake nan shi kuma zai yi magana da makaranta su ba mu aron Hamad mu tafi tare da shi a can za a warware komai”
Ta sake shi ba dan ta gamsu zai dawo ba idan ya fita sai dan babu yadda ta iya.
“Bana son ya sake tafiya ya bar ni..”
“As long as you're with me you're not alone, you will never be, babu sauran damuwa Hamad ba zai sake tafiya ba..”
Captain ya fada mata yana kokarin kwantar mata da hankali. Hamad ya share hawayensa ya ce.
“Idan ace Hajiya bata mutu ba, sai na kashe ta da hannuna...”
“Baka bukatar yin haka, jami'an tsaro da kotu zasu yi aikinsu”
Captain ya fada sannan ya karasa ya zauna kusa da matarsa ya kama hannunta ya rike sai ta kwantar da kanta jikinsa.
“Da gaske wai Hamad din ne dai? Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'u, wannan wane irin abu ne? Hamad...”
Mama Rukayya ta fada sannan ta nufe shi ta rumgume tana kuka sosai shi ma kuka yake yana kewar kanwar mahaifiyarshi...
Sai da suka sake yin two days a garin saboda processing din da Appa ya bi na ganin an samu dawowa tare da Hamad ba tare da wata matsala ba, a tsawon kwanan biyun nan kullum Hurriya tana tare da Hamad sai idan ya bar hotel din zuwa school, idan ya dawo Hurriya tana tare da shi tsawon wunin ranar tana labarta masa abubuwa da suka faru bayan baya nan yadda rayuwa ta zame mata a gidan Appa bayan tafiyarsa har zuwa aurenta da sherin da aka yi mata. Duk abun da suke Captain sai da yayi ta kallonsu gwanin sha'awa domin shi dai be san dadin dan'uwa ba.
“Na yi kewarki sosai Hurriya na fi jin kewarki fiye da kowa, saboda ina yawan dukanki ina zalintarki, da Captain ya fada min cewar bani da kowa a yanzu, sai na tuna abubuwa da nake miki na ji kamar na akashe kaina abun yana ta damuna...”
Hurriya tana hawaye ta ce.
“Yanzu duk mun girma Hamad, daman can kurciya ce, kana da zafin zuciya ni kuma bana iya raba kaina da kai, shiyasa har Amma ta yi maka takwara ban yarda ka mutu ba..”
Captain ya mika mata waya.
“Cry Cry Baby Ammy zata yi magana dake”
Ta karbi wayar ta kara a kunne.
“Hello Ammy ina wuni..?”
“Lafiya kalau, ya idon naki?”
“Alhamdulillahi ina ta samun sauki”
“Ya na ji muryarki wani iri? Ko Captain din ne yayi miki wani abun?”
“Aa ba shi ba ne”
“Ba shi wayar”
Hurriya ta mika masa wayar sai ya zauna kusa da ita ya kara wayar a kunne.
“Ammy”
“Wani abun ka yi mata ne? Na ji kamar tana kuka?”
“Ban mata komai ba, ya za'ayi na mata wani abu Ammy yaushe muka yi auren ma da za'ace har mun fara samun tsabani?”
“To waye be san halin maza ba? me take yi ma kuka?”
“Tana tare da dan'uwanta ai na fada miki abun da ya faru, kuma idan suna tattauna labarin baya tana yawan kuka shi ne kawai”
“Ayyah ba ka ce gobe za su dawo ba?”
“Eh in Sha Allah daman amincewar makaranta Muke jira kuma sun ba mu takardar a rubuce za mu taso gobe da safe da yardar Allah”
“Allah kawo ku lafiya, ku kula da kanku”
“I will i love you Ammy”
Ta gwatsale shi.
“Dan Allah can ko kunya baka ji a gaban matarka da kanenta sai ka ce wani yaro”
Yayi dariya ya sauke wayar. Hamad ya kalleshi.
“Kai mutumen kirki ne Captain ka kula da ni yadda ya kamata, Hurriya ta ba ni labarin yadda ka yi mata yaki, amman me yasa ka ce min kowa ya mutu?”
“Idan mun je zaka ji”
Captain ya juyo da fuskar Hurriya
“Mai tsada me za miki order?”
Ta juya ta kalli Hamad.
“Hamad me zaka ci?”
“Haba Baby ina lallabaki ki ci abinci ke kuma da wannan gwaskan kike? Babu inda be sani ba a garin Addis Ababa ki daina damun kanki da cinsa”
“Ko a gida haka muke, inda har zan ci abinci to zan zuba masa ne ya ci, ka yi hakuri
Yaja hancinta yana murmushi.
“Tsokanarki nake, tambaye me yake so sai na siyo muku”
Hamad yayi murmushi yana ganin kamar mafarki ne, wai yayarce da mijinta zaune tare da shi a yau.
“Yayata mai kaunata yar'uwata abar alfaharina”
“Ba ka ce ni ba yayarka ba ce?”
Ta tambaya tana hawaye shi ma hawayen yake yana murmushi.
“Ada kenan yanzu na bar miki girman”
Ta yi murmushi cikin hawaye, Captain ma Murmushi yayi ya tashi ya fita.
Ya sake daukarsu awa biyar da mintuna kamin su iso Nigeria daga babban birnin Ethiopia. A Abuja suka sauka, ba su tsaya komai ba suka sake booking flight from Abuja to Kaduna, Ammy ta yi musu tarba ta musamman tana ta na'am na'am da matar danta kamar daman can babu wani abun da ya taba shiga tsakaninsu. Sai da suka yi wanka suka huta sannan suka hadu a teburin cin abinci da yake gidan. A nan Hurriya ta gane ubanta Alhaji Haruna Mai Yadi karyar arziki yake domin falon Ammy ma ba tile ba ne wani abun ne aka shimfida mai kamar ruwa, ga manyan kujerun da bata taba ganin kalarsu ba a rayuwarta, dinning din ma wani abun kallo ne a gurinta balle kuma dakin da suka sauka. Ko'ina na gidan kyalkyale ni kamar an watsa zinari. Bakauya ta zama a gidan komai ta gani sabo yake zama mata, a nan ta yarda da Momy take ganin kamar bata dace da auren Captain ta bangaren arziki. Masu aikin gidan ma kansu abun kallo ne basa barin komai ya zuba a kasa da zarar an aje abu za su zo da gudu su dauke.
Captain da kansa yaja mata kujera ta zauna, sannan ya zauna yana magana da mahaifiyarsa da ta zabi serving din matarsa da kanta ba kamar Momy Ikilima da Mama Rukayya da masu aiki suke zuba musu abinci ba, sai da ta fara ajewa Hurriya plate din abinci sannan ta zubawa Captain ta aje masa warin kwai dake kan salad ya saka shi jin tashi zuciya da sauri ya kawar da fuska yana yunkurin amai.
“Me ya faru wani abu ka gani a abinci?”
“No kwan ne na ji shi wani iri, bana son warinsa”
Ammy ta dauke plate din ta zuba masa wani abinci babu kwai har ya fara ci sai kuma ya ji baya son abinci kawai wani abun kwadayi yake so.
“To ko dan kun yi tafiya a jirgi ne?”