Sashe 150
Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hurriya ta mike tsaye ta matsa kusa da inda take jin muryar mahaifinta sai wata daga cikin kanen Appa ta kamata ta zaunar da ita gaban Appanta. Hurriya ta rike kafafuwansa tana kuka.
“Na gode Appa, da yardar Allah ba zan saka ku ji kunya ba, Appa ka yafe min dan Allah”
“Na yafe miki Hurriya baki min komai ba, ke yar albarka ce.”
Shigowar Yasir ne ya hana kwalla dake idon Appa zubowa domin ya shigo da zolaya ne.
“Wayo take Appa dan ta samu a yafe mata, ai ba mutuwa zaki yi ba aure ne dan haka ki daina wani rokon gafara, ko Appa ya yafe idan ban saka baki ba ba ta yi ba”
Duk suka yi dariya har Hurriya da ta daga kai tana jin kamar ace zata iya ganin yayan nata mai tsananin nuna kauna a agare tun kurciya har girmanta. Yasir ya daga mayafinta ya dubi fuskarta.
“Kanwata, yau zaki tafi ki barmu ko? Rayuwarki zata koma wani gida tare da wasu Iyali da ba mu ba, Allah ya baku zama lafiya, kuma zan jaddawa angon nan cewar kanwata mai zurfin ciki ce ko da tana cikin damuwa bata fada dan haka ya rika kula”
Hurriya ta kwanto jikinsa tana kuka.
“Yayana yayan da ya fi na kowa”
“Ina alfahari da ke kanwata”
Appa da kansa ya bukaci a shiga da ita gurin yan'uwanta ta yi musu bankwana, haka kuwa aka yi bangaren Hajiya Kaltume aka fara shiga da ita, aka zaunar da ita a falon, Hajiya Kaltume ta fito ta tsaya daga sama bata sauko ba saboda bakinciki, daga inda take tsaye ta yi Allah sanya alheri. Khairy kam saukowa ta yi tana kuka sosai kamar ranta zai fita ta yi rama kamar ba ita ba, da kanta ta zauna a gaban Hurriya ta kira sunanta da muryar kuka sai Hurriya ta kasa amsawa.
“Ki yafe min dan Allah... Na san na cutar da ke amman ki daure ki duba hakkin jinin dakw tsakaninmu ki yi hakuri ki yafe min dan Allah...”
Rukayya Allah Allah kawai take kar Hurriya tace ya yafe mata, domin ta san halin yarta da sanyin hali. Hajiya Kaltume dake tsaye can sama kuma tana jin kamar ta sauko ta lakadawa Khairy shegen duka akan wannan abun kunyar da ta yi mata. Ruma ma ta roki yafiyarta tana kuka ta rumgumeta, daga bangaren Hajiya Kaltume aka wuce da ita bangaren Momy, a falo aka samu Momy tare da Namra suna zaune da Miwan. Hurriya ta zauna kasa tana neman yafiyarki tana kuka.
“Babu wanda zai ce kin masa wani abu da saninki Hurriya, halinki mai kyau ne, ni na yafe miki haka Allah ya kaddara haka ya so, Allah ya ba ku zaman lafiya”
Shi ne abun da Momy ta fada tana hawaye, domin a yanzu ta yarda babu sarki sai Allah babu yadda zata yi da abun da Allah ya kaddara faruwarsa. Daga gidan Appa aka wuce da ita family house din mijinta ta gaisa da su Nene da Hajiyar Maru, kanen Mahaifin Captain da kanenen mahaifiyarsa da wasu daga cikin danginsa, babban akwaiti aka bude mata kowa ya kawo nasa kyautar a zuba wasu tufafi wasu kudi. Da aka kawo a gurin Ammy sai ta kama hannun Hurriya ta saka mata key mota.
“Barka da zuwa Turaki Family yarinya, ba dan Captain yana ďana ba, amman tabbas kin yi dacen miji fatan ba zaki ba shi kunya ba”
A take falon ya dauki ihu kowa na murna da mamakin Ammy ta yi ma Hurriya kyautar mota, a sabuwar motar aka saka Hurriya da masu kaita gidan mijinta suka kama hanya zuwa gidan Captain. Kusan rabin unguwar Gidan dawa sai da suka san da Amarya a unguwar saboda manyan motocin da suka rika ratsa titin suna shiga cikin unguwar. Wani mamaken gidan da za a iya karamin gida hudu a ciki aka shiga da Hurriya, har gaban babbar kofar falon aka faka motar, kan wani jan carpet da aka shimfida na musamman domin Amarya Hurriya ta sauko da kafafuwanta tana lullube da fuskarta aka shiga da ita gidanta mai cike da kamshi ga guďa na tashi ta ko'ina.. Dakin da aka ware a matsayin na Captain a ciki dakuna biyar da Appa ya cika mata da kayan daki aka zaunar da ita akan gadon na alfarma, kan lallausan zanen gadon da aka siya mata gurin Khadeeja Candy. Iyaye suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi, aka barta da Husna sai yan matan Amarya. Ba dauki dagon lokaci ba aka shigo da ango yana sanye da shaddarsa fara mai matukar kyau. Kana ganinsa ka ga ango baki baya rufuwa fuska dauke da annuri. Kusa da matarsa kuma uwargidansa ya zauna abokansa na zolayarsa shi dai be ce komai ba sai murmushi yake. Su ma abokansa da yan'uwa suka yi ta su nasihar sannan su Husna suka kara da taku suna dariya domin babu mai aure a cikinsu.
“Ba sai kun fada mana ba, angonta ya ta jadda mana amaryar mai tsada ce, dan haka ba mu bukatar tayawa zamu bada abun da ba a isa a mayar mana ba... Ko wace mota da zata yan matan amarya akwai jakar kawayen amarya a cewa kowa jaka tana dauke da kyauta da kuma kudi na siyen bakin amarya”
Hakan da Cousin din Captain ya fada va karamin faranta ran amarya yayi ba, suka ji dadi suka daga mazan har matan suka fice suna murna tare da addu'ar alheri ga ma'auratan. Sai da kowa ya fice sannan Captain ya daga mayafin Amaryarsa ya leka fuskarta ya kalli hawayen dake zubo mata.
“Mai tsada... Idan ba ni ba wa za a kawo wa Amarya tana kuka har yanzu?”
Ta yi murmushi cikin kukan ta ce.
“Idan ba kai ba, wa zai auri makauniyar amarya?”
Sai ya rumgumeta yana dariya.
“Ni ne idonki ai, na huta baki bukatar kallon kowa daman a yanzu”
Ta sauke ajiyar zuciyata tana lafewa a jikinsa kamar wata kyanwa. Ya kama hannunta ya rike yana murza yatsun a hankali.
“Na gode Allah da ya nuna min wannan ranar Alhamdulillah, ban yi tsamanin abubuwa za su zo mana haka da wuri ba, ko da yaushe tsarin Allah mai kyau ne”
Ita dai bata ce komai ba tana kirjinsa sai shakar dadaddan kamshinsa take. Ya dago ya ssauke lifayar daga kanta zuwa wuyanta ya shafa kanta.
“Maa Shaa Allah, Amarya ta kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, kin ga yadda kika yi kyau yau kuwa?”
Ta girgiza kai alamar aa. Sai ya fara fada mata yadda komai yayi kyau a jikinta yana tana hancinta da bakinta har sai da ta yi dariya.
“Taso mu yi alwala”
“Na yi a gida”
“Shi ne baki fada min ba na yi?”
Ya ja lebenta a hankali sannan ya sake ta ta tashi ta cire babbar rigarsa Falo ya fara fita ta rufe musu kofar gidan sannan ya dawo ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya shimfida musu carpet ya daga matarsa yana rike da ita ita ya tsayar sa ita daga baya shi kuma ya matsa gaba kadan ya tsaya kabbatar sallar. Cikin natsuwa suka yi sallah Nafisa yayi musu addu'a ya juyo ya kama goshinsa ya karanta addu'a sannan ya kwanto da ita jikinsa.
“Yan mata na...”
Ta yi shiru tana jin wani bakon al'amari da bata saba ji ba, wani yanayi take ji na dabam a tare da ita. Hannunsa ya saka aljihun rigarsa ya ciro dabinon da Daddy ya damka masa ranar da aka daura aurensu ya saka a bakinsa ya tauna dabinon da yawunsa sai da yayi taushi sannan ya saka hannunsa ya ciro ya kai mata saitin bakinta.
“Dabinon daurin aurenmu ne, ranar da Daddy ya ba ni a raina na ce zan aje sai kin tare mu ci a tare”
Ta bude bakin da tunin yawunsa da ya tauna dabinon da su suka jika mata lebe, ya saka mata a baki sannan ya lashe hannunsa, ya sake tauna wani har yayi taushi sannan ya dago fuskarta ya hade bakinsu suka ci dabino a tare. Kamin ya cire bakinsa ya kalli fuskarta yatsansa ya saka ya matsa hancinta har sai ta ta fara masa kukan shagwaba.
“Da zafi”
“Uhmmm wannan kawai tukuna ma”
Ya tsakani idonta yana murmushi, kamin ya tashi ya dauko musu abun tabawa, sai da ya fara ciyar da ita ta koshi sannan ya ci, daga bisani ya kawar da komai ya dauki Amaryarsa cak sai kan gado. Wardrobe ya dauko musu kayan bachi, sai da ya saka nasa sannan ya fara kokarin rabata da lifayar dake jikinta.
“Ke me yake zuciyarki? Hummm me kike tunani?”
Ya rada mata a kunnen kamin ya dago ya kalli fuskarta. Sai ta yi shiru domin bata da abun fada, tun da ba wani abu yayi mata ko yace mata ba.
“Kayan bachi zan saka miki”
Ta kanne kafada.
“Aa da wannan zan kwanta”
“Hey don't try to act smart here”
Ta fara rare masa kuka a hankali, sai yayi murmushi yaje kayan bachin ya zauna kusa da ita ya rumgumeta. A dole ya hakura ya kyaleta ta yi bachi da lifayar har safe.
HAJIYA KALTUME POV.
“Kin ba ni kunya Khairy ban yi zaton zaki iya haka a gaban mutane ba, idan ma neman yafiyarta zaki yi ai sai ki yi daga ke sai ita a cikin mutane ba, yanzu ai ta ji dadi ita da Iyami sai su ce gashi nan kina kuka kina neman yafiyarta”
“Hajiya wanda aka yada video shi a duniya kamar ni da yana da sauran jin kunya ne? Ni fa yanzu rayuwata ta kare, da ina tunanin auren Fadeel zai rufe abubuwa da yawa akaina kuma ya saka ni jin sanyi amman haka ya gagara, shi ma ya juya min baya”
Ruma ta kalli Hajiya cike da damuwa ta ce.
“Hakan da ta yi ba laifi ba ne Hajiya, idan ba irin yau ba yaushe zata roki yafiyarta?”
Hajiya Kaltume ta ja tsaki, bakinciki ya zame mata kashi kashi. Khairy ta mike tsaye tana kuka ta haura sama ta shiga dakinta sai ta kife akan gado ta fashe da kuka.
“Ka cutar da ni Adam.. Ka gama da rayuwata ka ruguza shiri ka tarwatsa duniyata wayyo Allah na...”