Sashe 76
Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Lallaba min ita zaki yi, yau ma zan shigo gidan kuma tare da dan'uwanki In Sha Allah”
Har zata tambaya ta ce wani dan'uwanta sai kuma ta ji bata bukatar hakan, domin ya nuna ba ita yake ra'ayi ba, dan haka be kamata ace ta shiga hancinsa ba.
“Okay zan yi kokari, amman daga wannan ba zan sake ba gaskiya, baka fada min ya kuka kare ba a wacan karon”
“Idan na zo zamu yi maganar”
“Okay”
“Thanks”
Ta cire wayar kunnenta tana hautsina fuska, kamar zata ji haushinsa kuma sai take ganin babu dalilin haka. Aje fillon tayi ta sauko saman gadon,
‘Babu wani lalaba ta da zan yi, yarinya ta nuna vata yinka dole ne, ai maganin namiji mai shegen ruwan ido kenan da son mata’
Ta fada a ranta kamin wasu zantunka su fara zagayar kwakwalwarta, yanzu da Momy ta fada mata kudirin da suke da shi akansu ita da Captain sai take ganin wata kila canja mata ne Allah zai yi da son Salim da ta fara, ya bata wanda ya fi shi komai, dan murmushi mai kyau ne ya kawata fuskarta, ta mike tsaye ta nufi kofar dakinta ta bude sai da ta shiga dakin Momy ta duba bata ciki sannan ta sauko kasa domin ta san idan bata dakinta to tana kasa ko bangaren mahaifinsu ko kuma ta fita daga gidan. Tun kamin ta karasa saukowa stairs ta ji fadan da Momy take yi ma Hurriya har da rantse rantsen abun da zata mata idan ta sake zuwa kai tsaye ta bude mata kuloli ta zuba abinci.
“An gama abinci ban zubawa mijina ba, ni ban zuba ba sai ke ki zuba ke gaki issashiya ko? To ba zan daukar miki wannan ba, daga yau sai yau karki sake bude min kula ki zuba abinci ki jira sai na diba, ai na fada miki nan ba bangaren Iyami ne ba, wannan rashin tarbiyar da kuke ni ba zan dauke shi ba”
“Ki yi hakuri Momy, hakan ba zai sake faruwa ba”
Hurriya ta fada cikin muryarta mai sanyi, dake nuna tsantsar nadamarta. Momy ta sake daka mata tsawa.
“Idan ma ya faru ke ce a matsala domin kanki zaki jawa bala'i”
Hurriya ta ji kamar ace zata iya gyara komai kamar bata taba ba, amman ba dama domin mai afkuwa ta afku, cikin tsananin damuwa ta nufi stairs tana tambayar kanta.
‘Wai haka ko wace ya take fuskarta matsala a gurin kishiyoyin uwa, ko kuma ita ce ta fita dabam?’
Bata da mai amsa mata tambayarta kamar yadda ita ma bata san amsar ta ba. Namra ta bita da kallo har ta haye sannan ta sauko.
“Abinci ta zuba?”
“Eh saboda iskanci da rainin wayo, ni kaina ban zuba ba amman ta zo ta bude warmers ta zuba abinci”
“Wani sabon iskanci ne ta kirkiro kuma yanzu?”
“Oho mata ita zata sha wahala ai”
Momy taja kujera ta zauna, Namra ma ta ja nata kujerar ta zauna, sannan Momy ta fara zuba abincin.
A bangaren Hajiya Kaltume kuwa tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira, Malam rashin samun wayarsa ya saka ta kira kawarta.
“Ikon Allah, hausawa suka ce dan halak kaki ambato, yanzu fa nake son kiranki na tambaya size din Khairy na talkami”
Hajiya Fatee ta fada daga dayan bangaren bayan ta amsa wayar kawarta Hajiya Kaltume.
“Hmmm ai ni wani abun ne na ji da ya so daga min hankali, kuma dai be daga ba shiyasa na kiraki”
“Me ya faru?”
“Wai anya baki tunanin Malamin nan yana tayar da aikin da muke ba shi ne saboda ya bukaci wani abu?”
“Ah touh Hajiya na ga cikin nan naki fa an kwantar kuma ya kwanta daga baya abu ya tashi, har kika ce ya bukaci wani abu agareki, ni na ma manta ban tambayeki me ya bukata ba”
“Hmmm wannan maganar kuma ai ta wuce Hajiya Kaltume ciki kuma ya koma ya kwanta yadda ake bukata, ke dai yanzu me sa kika kira ni kuma me ya daga miki hankali tukuna bari mu ji na ki”
“Salma ce ta dawo dazun, bayan ta huta take min hirar wai mahaifinta yana son kawarta”
“Maa Shaa Allah Salma an dawo? Hajiya miye abun mamaki a maganar? Maza ko uwarki aka ce su aura ai aurenta za su yi, balle kuma kawar yarsu, ke maza fa ba su da kunya, ina ce Iyami ma ai yarinya ce kuma ya aureta ko kin manta”
“Amman ke Hajiya baki yi mamaki ace Alhaji yana zancen aure a wannan lokacin?”
“Daman namiji mai son aure aure ai ba zaka iya hana shi ba, halinsa ne ke dai yanzu ba kin mallake shi ba ai duk wanda ta ji zata iya kawai ta zo”
“Aa, ina tunanin na gama da komai sai kuma wannan ya taso, na bar shi yayi aure ya kwaso mana wata ita ma ta zo ta hana mu zaman lafiya? Kuma tace zata zuba nata yaya? Ai kara ma Iyami da wannan yarinyar da take karama sa'ar Salma fa kuma kawarta, ni ban gama yarda ba shiyasa hankali yake kwantawa wani bangare, kuma na kira Malam wayarsa bata shiga ba, sai dai kuma ina mamaki idan har gaskiya me yasa Malam be fada min ba? Bayan kuma yace duka aikin da yayi yana bibiyarsa duk lokaci? Ko dai ya kwance kullin ne shiyasa har haka take shirin faruwa”
“Hajiya ki kwantar da hankalinki, idan ma ya kwance aiki wata kila akwai abun da yake bukata ne kamar yadda yayi min, sai ki ba shi karki zo ganin yadda yake min aiki a yanzu, ko jiya sai da ya bani maganin da zan saka a nama yanka tara na bawa Fadeel ya ci, kuma tun kwanan baya da ya fara min aikin nan Wallahi na fara ganin gaske, domin yanzu gidana yake cin abincin dare, na safe kawai yake ci a can shi ma kuma na san ya kusa dainawa, ga maganar auren nan har zumudi yake a yanzu ba kamar da ba”
“Idan kuwa haka ne, ai babu adalci a ciki, bayan ya fada min yanzu babu kowa a zuciyar mijina sai ni, sai kuma ace ya kwance aiki, idan ma wani abun yake so sai ya fada kai tsaye ba sai ya kwance ba”
“Ina ganin zai fi kyau ku yi magana da shi ki ji koma minene, ni kam Wallahi sai sam barka, yanzu har jinsa nake kamar wani dan'uwana”
“Zan yi magana da shi”
“Okay, kamin ki manta minene size Khairy”
“Hajiya zan saka ta turo miki daga baya, yanzu kam bana iya gane komai”
“Kar fa ki saka kanki a damuwa, komai zai warware”
“Ina fatar haka...”
Ta sauke wayar da tunanina kala kala a ranta.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
24
Tun da Hurriya ta shige dakinta bata fito ba, har Magariba, bata son Momy tace ta mata wani abun ba daidai ba dan haka ta kebance kanta a dakinta, da dare ma bata ci abincin dare ba saboda bata fito ba, ta inda ta samu sa'a abincin da ta ci na rana be yi saurin narkewa ba, dan haka bata kwana da yunwar rashin cin abincin dare ba. Da asubar fari ta farka ta yi sallah sannan ta dora da karatun kur'ane har sai da rana ta fito sannan ta yi azakar ta hau gadonta ta koma bachi.
Tara da rabi ta sake farkawa, a kasale ta sauka saman gadon ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin bakar atamfa mai ratsin blue. Ta dora dankwalin a kan gado ta zauna gaban madubi ta gyara gashin kanta ta yi farkin dinsa a baya, sannan ta shafa hoto kadan abun da ba al'adarta mai ma dan ya zame mata dole ne take shafawa, amman a yau da yake ranar jumma'a ce ta ji tana bukatar yin kwalliya. Ta dauki turare ta mai kamshi ta fesa, sannan ta dauki man baki zata shafa sai ta tuna karyawa zata yi, hakan ya saka ta mayar ta aje ta koma saman gadonta ta kwanta tana duba agogo dakin dake nuna karfe goma daidai. Sai dai duk da haka bata son fita ta karya a yanzu ba dan bata jin yunwa ba sai dan bata son tsaba dokar Momy, sanin kanta ne Momy bata karyawa da wuri idan ta fita ta taba abun da Momy ta aje ba tare da Momy ta ci ba bata san iya hukuncin da zai biyo baya, dan haka ta kara minti talatin akai sannan ta fito kanta a sake babu dankwali gashin kanta sai sheki yake. Masu aikin Momy kawai ta samu a falon dayar na kallo dayar kuma na saka turaren wuta.
“Dan Allah Momy ta gama breakfast dinta?”
“Wane breakfast kuma Hurriya breakfast tun yaushe har an wanke komai, na rana ma kadan ya rage a gama”