← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 163

Sashe 42

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dakiku ma akan samu canjin rayuwa, balle kuma azo ga mintuna da awanni, ranaku sati ko wata ba a lissafinsu balle kuma shekaru. Da yawa an shafe wasu shafunka a rayuwar Hurriya an sabunta wasu, an busawa wasu rayuwa. Ta kan manta abubuwa da yawa, kuma ta karbi wasu kadarorin ta rumgumi sabuwar rayuwar dake fuskarta, ta saba da wasu dabi'u da halayya. Sai dai har yanzu ta saka yarda dan'uwanta ya tafi ya barta, ta kasa karbar wannan kaddarar, kuma ta kasa manta ranar da aka sanar mata da mummunan labarin da har gobe take karyatawa. Musamman a yanzu da girma ya gina mata sabon daki, a duk lokacin da wani abun dadi ko akasin haka ya same ta babu wanda take tunawa sai dan'uwanta, idan wani ya tsangwame ta a gida, mai bude hannayensa ya tare mata fada take tunawa, ranar da suka yi Candy idan ta kalli dama da ita bata ganin kawayenta sai dan'uwanta, babu daren da bata mafarkinsa, babu sallah da bata addu'ar dawowarsa.
Yar karamar takardar ce a hannunta tana shafa harrufan da tuni ta da haddace rubutun dake jiki, hawaye na jika kumatunta, a ranta take ta maimaita karatun da. Numfashi ta ja da karfi ta daga kanta ta kalli madubin dake gabanta wata mace ce zane a gaban madubin mai tsananin kyau sura da kyawun halitta da haifa, mai fari da yalwar gashi kamar ƴar Ethiopia. Garin gilashin dake mata mata garkuwa ya kara mata kamala. A natse ta lumshe ido ta hade yawu a hankali.

“Hurriya kina ina? Jiranki fa ake”

Ta bude idon da sauri, ta bude drawer madubin ta saka takardar ta rufe sannan ta mike tsaye ta share hawayenta ta dauki mayafin abayarta ta shafa a saman kanta sannan ta nufi kofar fita da saurinta. Tana bude kofar Momy na bude tata kofar da kan kace kwabo Hurriya ta sauko idonta kasa ta tsaya jikin kofar har sai da Momy ta sauka sannan ta sauko ta fice daga bangaren. Tun kamin ta isa bangaren ta fahimci kowa ya gama tafi domin babu mota ko daya a bangaren Hajiya Kaltume, cikin zullumi ta karasa ta shiga falon sai ta ga ko'ina wayan babu kowa. To daman waye zai tsaya jiranta ita banza a banza.

“Yauwa yar abaya daman a komai ai ke ce baya, kowa ya tafi ke kina can boye yanzu zaki fara karyar baki san sun tafi ba, daman ina bakinciki zai barki ki tafi abun yan'uwa? Hassada ai ta gama cinye ki”

Ta dago tana duba Hajiya Kaltume dake saukowa tana jefar Hurriya da duk kalmar data fado bakinta. Hurriya ta rike hannayenta kana kallon fuskarta zaka san kalaman Hajiya Kaltume ba su mata dadi ba, sai dai ta saba jin wadanda suka fi su ma daga bakinta ko na yayanta babu abun da yake sabo a gareta yanzu, ɗacin kuma ta barwa zuciyarta. Ta juya jiki babu gwari da zimmar ficewa sai aka turo kofar falon, kyakkyawan bakin saurayin nan mai matukar cikar kamala da mazantaka ya shigo falo fuskarsa dauke da murmushi bakinsa kuma kunshe da sallama. A take Hajiya Kaltume ta washe baki.

“Maraba da Fadeel yanzu ake tafe?”

“Eh ina wuni Hajiya?”

“Lafiya kalau ya aikin?”

“Alhamdulillah”

Har ya zauna Hurriya dake tsaye yake kallo, be dauke idonsa ba har sai da ta mika masa gaisuwa da muryarta mai matukar sanyi, so innocent.

“Ina wuni”

Kamar daman gaisuwar yake jira sai ya dauke idonta after ya amsa ya kalli Hajiya Kaltume.

“Hajiya ce tace na zo na dauki Khairi wai ko bata samu mota ba?”

Hajiya Kaltume ta dan yi shiru kamar mai tunani kamin ta karasa saukowa ta amsa masa.

“Eh... Amman ta samu daga baya, sai dai ko idan zaka ka leka ne”

“No daman akwai inda zan je kawai saboda Hajiya ta matsa ne ya saka na zo na kaita, amman tun da ta samu shi ke nan ai”

Ya mike tsaye, Hurriya ta dan kalleshi tana jin kamar tace masa ya aikata ya kaita, kuma bata isa ba domin Hajiya Kaltume na tsaye a falon, ko da ma ace bata gurin abu ne mai wahala Hurriya ta iya rokon abu.

“Ba zaka tsaya ka sha ko ruwa ba? Hurriya kawo masa ruwa mana”

“No tafiya zan yi ai”

“Sai fa ka sha zauna mana sa nan da gurin Hajiya Fatee ai duk gidanku ne, kunya kuma na miye?”

Baya son musa mata dan haka ya zauna yana murmushi kamar yadda ita ma take murmushin. Hurriya ta nufi hanyar kitchen bata jima ba ta fito rike da gorar ruwa da cup tana kokarin ajewa ya mika hannu ya karbi gorar ya bar mata cup din, kamar ya san burin da take da shi a zuciyarta sai ya tambaye ta.

“Ke miyasa baki je ba? Ko baki samu motar ba ne?”

Ta daga masa kai a hankali kamar wadda bata son motsi.

“Muje na sauke ki”

Ta juya zata kalli Hajiya sai ta jiyo Hajiyar na fadar.

“Aa haba ka tafi kawai gurin aikinka, ai bata yi niyar zuwa ba ne, shiyasa ta boya sai da kowa ya watse sannan ta fito”

Kalma daya bata isa ta musa ba a cikin kalaman Hajiya Kaltume, dan haka bata ce komai ba ta sauke kanta kasa.

“Ko maybe bata son shiga mutane ne, na lura she's different, can i drop you?”

Ya karasa da son ya ji amsarta sai ta daga masa kai ba tare da ta kalleshi ko ta kalli Hajiya ba, domin har ga Allah tana son zuwa birthday party din na Khari da ta hade da graduation dinta.

“Hajiya na gode zan ajeta sai na wuce”

“Toh Allah ya kai ka lafiya”

Ya wuce gaba, Hurriya ta bi bayansa har lokacin kanta na kasa, Hajiya Kaltume na watsa mata harara kamar ta fisgota ta yi ta duka haka take ji. Suna ficewa ta tashi ta nufi stairs duk yadda ta so yin sauri bata iyawa saboda jikinta baya barinta ta wala yadda take so. Tana isa bakin kofar dakinta ta kai hannu ta tura kofar dakin zata shiga sai ta ji kamar an turata haka ta tafi suuuuu ta fadi kasa ridd rub da ciki.

“Subhanallahi”

Ta fada sannan ta yunkura ta tashi zaune tana jan kafa ta isa bakin gadonta ta zauna ta daga zane ta duba kafar dake mata mugun ciwo.

“Ya haka abu dai kamar an turo ni”

Ta latsa cinyarta dake cike da tsokar nama tana runtse ido saboda zafin da yake mata. Karar wayarta ne ya dago hankalinta ta kai dubanta gurin da wayar take Hajiya Fatee ce a line hannu ta kai ta dauka ta danna picking ta saka a hands-free ta aje wayar saman gado.

HURRIYA POV.

Tun da suka fita daga gidan idonta na gurin titi da motocin dake ta zirga zirga, Fadeel ma be ce mata komai ba kwarjininta ya cika masa ido ta yadda har ya kasa tambayarta gurin da zai kaita. Kallonta ma sai yayi da gaske yake yi, shi ma kasa kasa, yayi kanwa ta hudu da ita amman ya samu kansa da jin nauyinta, maybe because tana so Innocent ne kuma saboda tana kyau ne irin mai cika idon nan da haifar da natsuwa, or maybe kuma saboda tana karama ne she's too young yaja ta da hira. Ganin suna ta dawowa the same road da suke tafiya ya saka ta dago ta kalleta sai yayi mata dan murmushi kadan.

“Ban san even center din da za'ayi party ba”

“K_Candy Event Center”

Muryar ta fito between her two soft lips.

“Okay....”

Ya cigaba da tukin, after like ten minutes ya sake yin magana ba tare da ya kalleta ba.

“Yaushe za'ayi naki birthday”

Ta yi shiru kamar bata ji shi ba.

“Ko an yi?”

“Ba ayi ba, amman ya wuce”

“How old are you?”

Uffan bata ce masa ba har suka isa gurin ya faka motarsa ta bude zata fita sannan ta ce.

“19...”

Ya bita da kallo har ta fice.

“Thank You”

Ta rufe masa motar a hankali sannan ta nufi hanyar shiga tana tafiya kamar mai tausayin kasa.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

𝐏𝐚𝐠𝐞 8⃣

Tana isa gurin masu aikin tsaron kofar suka tareta.

“Ina zuwa?”

“Ciki”

“Ina katinki?”

Sai a lokacin ta tuna ta ji Khairi da kawayenta suna maganar gate pass amman bata maida hankali ta karba ba ganin ita din ta gida ce.

“Yayata ce take yin biki ciki, ba na bukatar gate pass”

“Gaskiya ba zaki ita wucewa ciki ba sai da gate pass”
Chapter 42 · 0% Book details