← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 163

Sashe 69

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa mata muryarta na yin kamar zata yi rawa. Khairy ta karaso cikin falon tana musu kallon tuhuma domin jiki da fuskar Hajiya Kaltume ya nuna alamar ba lafiya ba, ga Ruma sai kuka take sosai.

“Lafiya?”

“Lafiya Kalau”

Hajiya ta amsa mata da sauri, Ruma ta tashi tana kuka ta nufi stairs, Khairy ta bita da kallo har ta haye sannan ta kalli Hajiya da hantar cikinta ke kadawa ta ce.

“Me ya faru take kuka?”

Abun ka da makiri kuma wanda karya bata yi ma wahala a take Hajiya ta juye abun domin bata son kowa ya ji.

“Munafurcin da Hurriya ta yi ne ya taba ta”

“Munafurci?”

A tsaye Hajiya Kaltume ta zubewa yarta komai da Namra ta fada har ma da wanda bata fada ba, daman ai ba zata bar miya haka nan ba sai ta kara mata gishi da magi.

“Wallahi kawai ki fadawa Appa shi zai yi maganinta idan ba haka ba, shi ma kansa sai ta hada shi da Hajiya, waya sani ma ko ta zugota ta zo tace ba ta yafe masa ba, ko kuma ta rantse sai ya sake ki, daman tana da haushin barin gidan nan da uwarta ta yi, shiyasa ni gaba daya fa bana kaunar yarinyar nan, ga iya jan hankalin maza na bala'i kamar wata rikakkar karuwa”

“Wannan kuma ba banza ba, ai kin san uwarta sai ta wanke ta bata sha, kamar yadda ta sha ta dauke hankalin Alhaji har ya aureta”

“Gaskiya ni ma i doubt wannan farin jini da jan hankalin ba banza ba ne, ba zai yuyi ace kowane namiji farar mace mai kyau yake so ba, to mu ayi yaya da mu bakake?”

Tana fada tana bata rai kamar ta ci magani.

“Ba farin ne kawai ba, har da asiri”

“Daga gani ma ba banza ba, Hajiya tafi ki fadawa Appa ya daukar mata mataki tun wuri”

Ta zauna saman kujera tana ta fushi kamar an mata wani abu, kamin ta shiga Gallary wayarta ta kamo hoton Hurriya ta kura ido tana son tantance abun da Adam ya gani a fuskarta da jikinta da ya nace sai ita, ga Fadeel ma ko a jiya da ya zo sai da ya nemi yin magana da ita.
Hajiya Kaltume da har lokacin a tsaye take ta juya ta nufi kofar dake gefen dinning wanda zata sadata da bangaren Appa, zuciyarta fal da tsoro na maganar Ruma, yanzu ba kisan ne abun da ke ranta ba, fallasar asirinta ne abun da yafi damunta, shekara uku amman Ruma ta kasa mantawa ta saka sakewa gaba daya ta canja tun a lokacin da wannan abun ya faru, idan kuma har zata rika sakin baki haka wata rana dole asirinta zai tonu, ita ta san har ga Allah bata ce a kashe Hamad ba, ba saka an dauke shi dan a kashe shi ba, hasalima ba shi aka je dauka ba, Hurriya ta ce a dauka, tsaitsayi ya biyo ta kan Hamad ashe da rabon ya bar mata baya da kura. Bata san ta isa bangaren Appa ba sai da ta ji ta bugi kofar shiga, a nan ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido ta dafe kanta da hannu daya.

_Kai wayyo Allah... Da na sani ban aikata wannan abun ba, da ma ta asiri na bi kamar yadda na yi ma Iyami, duk gajin hakuri ne ya ja min, yanzu ko yaran nan aka kama suka fadi sunana ai na shiga uku sunana zai bace a duniya, yarana su ji kunya musamman ma matan nan_

A ranta take ta sake sake rashin natsuwa da tashin hankali na kara kusantar ta, ta sauke ajiyar zuciya ya kai sau takwas sannan ta sauke hannunta ta murda kofar ta shiga, babu kowa falon dan haka ta nufi karamin falon Appa da ya fi yawan zama. Yana ganinta yayi saurin sauke wayar da yake ya yanke kiran murmushin dake fuskarsa ya bace.

“Hajiya”

Ta zauna kusa da shi tana fada.

“Na'am Alhaji a nan ake hutawa, Nafisa bata shigo ba?”

“Ina tunanin sai an jima kadan zata shigo”

Yayi saurin rejecting kiran dake shigo masa ya saka wayar silent ya aje ta a gafe.

“Toh bari na yi magana ta kamin ta shigo, wata kila ma ita ce take kiranka kasan sarauniya ce wani lokacin sai dai ta kira ta tambaya abun da kake so ta zo maka da shi, ba kamar mu da bama raina lada ba”

“Aa ba ita take kira ba, wani.... Sakatarenmu ne... ”

Ya amsa kamar marar gaskiya. Cikin rashin kuzari na abun da ya faru ta kora masa da bayanin abun da Hurriya ta yi har Hajiya Binta ta aiko musu da sako. A take Appa ya hade fuska ya bata rai sosai daman a yanzu baya ganin farin Hurriya sai bakinta.

“Wai yarinyar nan me take son zama ne?”

“Toh ka gani dai idan baka daukar mata mataki ba, sai ta lalace kuma nan gaba ba a san me zata yi ba, kai kanka idan baka dauki mataki ba sai ta hada ka da Hajiya, kara tun wuri ka rabata da gidan Hajiya ka maida ita can gurin uwarta ko kuma ka dawo da ita nan din, domin ni dai ina jin tsoron shairin yarinyar nan, kara nan tana karkashin kulawarka zaka saka mata ido”

“Bana bukatar Hurriya a gidana”

Appa ya fada a fusace.

“To ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, in ji kishiyar konanniya, hakuri zaka yi tun da hannunka baya rubewa ka yanke ka yar kar dai ta zauna gurin uwarta ko gidan nan, nan din ma zai fi saboda Hajiya zata iya cewa ba zata zauna gurin uwarta ba, kuma idan ma ta zauna can zata iya sulalawa ta koma gidan Hajiyar ba tare da saninka, kara tana gabanka kana ganinta, albashi ka samu ko masinja ne cikin ma'aikanta ka aura masa ita mu huta...”

Uffan Appa be sake cewa ba ya bata rai sosai, domin sam maganar da Hajiya ta fada masa na abun da Hurriya ta yi be masa dadi ba

𝐊𝐇𝐀𝐃𝐄𝐄𝐉𝐀 𝐂𝐀𝐍𝐃𝐘

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

𝐏𝐚𝐠𝐞 2⃣1️⃣

Appa be raba dayan biyu ba Momy ta turo kofar dalon ta shigo, yadda ta tararda Appa da Hajiya Kaltume a kujera daya ya saka ta daure fuska ta fara wani kallo na uku saura kwata.

“Miye haka Alhaji? Ina ce yau dai girkina ne, ko kuma irin abun da ake yi ma Iyami shi za'ayi min?”

Hajiya Kaltume ta tabe baki, har ta juyar da fuska sai kuma ta juyo ta kalli Momy.

“Magana ce ta kawo ni, maganar da zata taimake ke ki ta taimake ni kuma ta taimaki wanda muke neman aljanna karkashin kafarsa, magana ce akan Hurriya kuma yarki aka aiko da sakon shi nake fadawa Alhaji”

Momy dake tsaye ta dauke kai domin haka be gamsar da ita ba, cikinsu babu wanda yake son ganin abokin zamansa a bangaren mijinsa idan ba girkinsu ba ne, sai dai Iyami suna mata haka, su kam shiga su yi magana da Appa ko da tana ciki wani lokacin har sai Appa da kansa ya nuna musu baya so, ita kuma tana kiyaye yin haka idan ba girkinta ba ne.

“Toh tun da kin fada ai sai ki kama hanya ko kuma maganat bata kare ba ne”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi kamar ba ita ba.

“Nafisa... Hajiya Nafisa... Ya fa kamata ace mun aje kishi a yanzu, ya kamata ace mun san girma ya kama mu a yanzu, ni idan ma kina son kwanan idan girkina ya zagayo ai sai na yafe miki, ni dai ina neman mafita ne acikin lamarin nan, domin Hurriya ba ni kadai ta sako a gaba ba har da ke.. Da kuma mahaifinta, wata kila nan gaba kadan idan tana zaune a gidan Hajiya zata iya sakawa ta tsine mana gaba daya, ko kuma ta cilastawa Alhaji rabuwa da mu”

Appa yayi karaf ya ce.

“Aa Hajiya ai tana da hankali da tunani, ba zata yi haka ba”

“Baka da tabbaci kai kanka idan aka fada maka Hurriya zata aikata abun da zai saka ka koreta a gidan nan zaka yarda? Amman da yake butuluce kamar uwarta ai gashi nan ta je ta zage ka a wani gurin ta saka makota suna maka kallon azzalumi, nan gaba kadan kuma baka san abun da zai biyo daga gurin Hajiya ba, kasan dai yadda take son Hurriya take daukar shawararta”

Sai a lokacin Momy ta kai zaune, bayan Hajiya Kaltume ta gama rattaba bayannanta.

“Ni abun da nake gani kawai ka yi hakuri ka dawo da ita gidan nan, idan ba haka ba ma zata iya lalacewa”

Momy ta dubi Hajiya Kaltume ta ce.

“To miye amfanin korarta da Alhaji yayi? Ai sai ta dawo ta cigaba daga inda ta tsaya tana hada mutane”

“To ai mun san halinta yanzu, ko da ta fada ba zamu yarda kuma dole a ja mata kunne”

“To sai dai idan bangarenki zata zauna, ni dai na gaji da zamanta a gurina, balle kuma yanzu”

“Aa ni da take kallon a matsayin makiyiyarta, ta ina ma zata yarda ta zauna a gurina”

Appa ya gyara zama ya kallesu one after the other ya ce

“Kar wanda ya sake bani shawara ko zabin gurin da Hurriya zata zauna, idan har zan dawo da ita cikin gidan nan a inda nake son ta zauna zata zauna, daga gidan har ku da yayanku a karkashin ikona kuke, musamman ke Nafisa na lura da bakinki ba shi da linzami akan irin wannan maganar, kai tsaye kike furtawa, na yi miki kashedi amman baki ji ba, wata kila sai kin ga zahiri... ”

Da mamaki Momy ta kalleshi bakinta a sake ta ce.
Chapter 69 · 0% Book details