← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 163

Sashe 52

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

After fitar Namra Hurriya ta nufi gurin da turaren yake ta kai hannu ta dauka ta bude kamin ta shinshina kamshinsa Khairi ta turo kofar dakin ta shigo a kufule, waya a hannunta ba tare da ta ce komai ba ta mikawa Hurriya wayar. Sai da Hurriya ta fara kallon wayar sannan ta kalleta. Khairi ta daka mata tsawa.

“Ki karba mana”

Ta karba da sauri ta kai kunnenta ba tare da sanin waye ba.

“Hurriya i wanted to talk to you so badly duk wani abun da kika ji akaina karya ne, kawai Khairi tana fadar son ranta ne”

Hurriya kallon Khairi kawai take wayar a kunnenta ta kasa cewa komai.

“Hello... Are you there”

Ta sauke wayar ta mikawa Khairi ba tare da tace komai ba, Khairi ta karbi wayar ta kai kunnenta.

“Bata son magana da kai ya kamata ka gane mana”

“Yeah that's because you told I'm a bad person, dazun nan babu kalar maganar da bata fada min ba a gaban mutane kuma duk laifinki ne”

“Ta ina abun kuma ya zama laifina Adam? Ni ban fadi wata magana marar kyau akanka ba, idan ma zan bata ka ko na zage ka ai kamar na yi ma kaina ne”

Cikin fushi ya tsinke kiran ba tare da ya sake cewa komai ba, ita kuma ta kalli Hurriya daman kowa da wanda ya raina.

“Cikin mutane kika ci masa mutumci? Kuma kika ce masa na ce yana shaye shaye?”

“Ni ban ce kin ce ba”

“Amman dai kin masa cin mutunci a gaban mutane ko?”

Ta yi shiru, a take Khairi ta kai mata duka a baki daman tana da haushinta, tana ganin saboda ita Yayanta yaya mata duka ya ci mutuncinta a gaban friends dinta, yanzu kuma saboda ita Adam ya kira yana fada mata magana son ransa.

“Haba Yaya Khairi”

“Au haba ne? Ni banza kika saka aka yi min duka? Munafuka yar kasan wuta, haka kawai kika ja min cin mutunci da duka a gaban jama'a”

Ta kai mata duka a fuska, Hurriya ta matsa baya ganin tana son yi mata illa.

“Wallahi tallahi sai na miki fiye da abun da kika min Hurriya, sai na dandana miki bakinciki”

Hurriya dai bata ce mata komai ba sai kallonta take, Khairi ta yi kwafa ta juya ta fita daga dakin, sai kuma ta dawo da sauri ta nuna da yatsa.

“Sauran kuma ki fadawa Yaya Adam ya kira na kawo miki waya, ki ga yadda zan taka wuyanki wannan kassan na jikinki duk sai na karya su”

Ta yi kwafa a karo na biyu sannan ta fice, Hurriya ta zauna bakin gadonta tana taba bakinta dake mata zugi...

“Allah ya saka min in one way or the other”

Ta fada idonta na cika da hawaye, sai da ta gama taba bakin sannan ta tashi ta dauko pen ta dubuta account dinta ta fice daga dakin, kofar dakin Namra ta fara turawa ganin bata ciki ya saka ta aje mata takardar a kan gadonta juyo ta fito. Dakinta ta sake komawa ta dauki littafin da Gwaggo ta bata na addu'o'in ta sauko, Garden ta nufa sai da ta zauna sannan ta bude ta fara karanta addu'o'in yamma.

HAJIYA KALTUME.

A waya ta labartawa Malaminta abun da ya faru, tana hada masa da magiya tare da alkawarin yi masa duk abun da yake so matukar ya taimaka mata Maama ta samu kan mijinta.

“Haba Malam kai da ka ra kwafar min da Alhaji, kuma ga Iyami ma sai labari za ace wannan ya gagareka”

“Ba gagarata yayi ba Hajiya, wato yaron nan iyayensa suna tsaye akansa, duk lokacin da zamu yi aiki ba ma samunsa ko da ma ya kama zaki ga abin ya bi ruwa, amman duk da haka zamu kokarta zam sake yi masa aiki mai karfi”

“Dan Allah a taimaka Wallahi yanzu ba ni da tashin hankali sai na yarinyar nan, kasan yadda uwa take jin idan ta aurar yarta a gidan tashin hankali, burina ace tana zaune da mijinta lafiya kamar yadda nake da nawa”

“Karki damu zamu yi haka, yau da daren nan akwai wuridin da zan yi mata, komai zai wuce”

“Toh shikenan zan sako mata na goro yanzu a account in Shaa Allah”

“Hajiya kenan toh sai na ga sakonki”

Daga haka suka yi sallama, bata aje wayar ba ta kira aminiyarta, sai da ta fara shimfida mata halin da suka sami Maama sannan na Malam ya biyo baya.

“Oh wannan yaro dai ya zama butulu, an yi aure lafiya lafiya ashe mugu ne”

“Ai ni da na san haka yake Wallahi ba zan yarda ta aure shi, daman can ni be wani kwanta min ba”

“To yaran zamani ne ko kin hana ta ai ba zata hanu ba saboda tana son shi, kuma wani ba za a gane halinsa ba sai an yi auren ba”

“Amman dai Malam yace min zai yi aiki yanzu”

“Ai haka yafi, ni wasu mamaki suke ba ni fa ki duba ko yarinyar nan Afrah yadda aiki be kamata, da yana kamata da yanzu ta bar gidan nan amman sai kashe kudi nake a banza ko gezau”

“Shi ma yace iyayensa suna tsaye a kansa, amman duk da haka na san ba zai gagara ba, karki so ganin yadda Maama ta lalace kamar marar lafiya saboda babu kwanciyar hankali a gidan miji”

“Ai kam dole a tashi mata tsaye, ni ma na kiransa domin ina jin alamar motsi a cikina”

Hajiya Kaltume ta zare ido kamar kawarta na gabanta

“Motsi kuma?”

“Wallahi, na fada masa sai yace na bashi lokaci zai bincika yake ga me kenan a jiya na fara jin abun”

“Haba Hajiya Fatee kuma kike magana kamar kina kalau? Ai zama be gan mu ba, kira shi yanzu nan idan ma zuwa ya kamata yayi sai ya zo ayi abun da ya dace, an samu danne abu shekara uku yanzu kuma ace Labari ya canja, ai yanzu ne zamu fi shiga tashin hankali ma fiye da baya”

“Ni ma ai hankalin nawa ba a kwance yake ba, ina jiran na ji daga gareshi ne”

“Muna aje waya yanzu nan ki kira shi, har sai kin jira ya kira ai mai nema bi yake, kira shi yanzu nan”

“Toh Hajiya”

Hajiya Fatee ta katse kiran, ta shiga contact dinta ta nemo number sa da ta yi saving da Yaya Malam saboda badda kama. Fuskarta shimfide da damuwa ta kara wayar a kunne, sai dai har kiran ya katse ba daga ba, ta sake kiransa ya sake katsewa ba daga ba sai a na biyar a lokacin da hankalinta yayi kololuwar tashi. Yana daga kiran sai da ta sauke ajiyar zuciya tana jin wata rahma na sauko mata.

“Salamu alaikum Malam ina ta kira baka daga wayata ba lafiya”

“Toh Hajiya gani dai Alhamdulillah”

Tana kokarin karantar damuwar dake son aika mata ta sautin muryarsa ta ce.

“Ba lafiya ba Malam, me ya faru? Akwai wata matsala ne?”

“Babba ba karama ba, shi ya hana ni daukar wayarki, ni kaina ina cikin tashin hankali”

Ta mike tsaye sai kuma ta koma ta zauna.

“Malam fada min me ya faru”

Malam yayi shiru kamar baya gurin can kuma ya numfasa ya ce.

“Wato Hajiya cikin nan ne ya sake tashi”

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, garin ya Malam? Ya aka yi haka ta faru”

“Ni kaina abun ya ba ni mamaki, shiyasa na ce ki ba ni dama na yi bincike kuma da na yi bincike na gane yadda matsalar take, sai dai maganinta ne da wuya”

“Kamar ya Malam na shiga uku”

Ta mike tsaye again ta fara safa da marwa tana kuka da babu hawaye mai cike da tashin hankali.

“Ba ki shiga uku ba, indai zaki iya domin wannan mafitar da na samu na sha wahala kam amman kuma karshe ce”

“Malam fada min kai tsaye dan Allah ka saka ni cikin rudani”

“Wato Aljannun da muka saka suka yi aikin nan, su suka warware shi, kuma suka waiwayo suna bukatar wani abu a gurinki mai girma....”

Hajiya Fatee bata san lokacin da gumi ya karyo mata ba, ta ji kamar ta dora hannu akai.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

𝐏𝐚𝐠𝐞 1️⃣3⃣

“Fada min Malam na ji idan abun da zan iya ne, kana ta kara jefani cikin tashin hankali”

“Wato Hajiya maganar ce da nauyi, sai dai ya zama dole a fada, Hajiya Aljannuna nan suna bukatar kwanciya dake”

Hajiya Fatee ta dora hannu saman kai ta matsa baya.

“Ni kuma? Ina Aljanni ina mutum Malam”
Chapter 52 · 0% Book details