← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 32

Sashe 9

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Abbi ji yayi kamar ya fasa kuka shima ko ya samu sauƙin abin da ke mai yawo a zuciya.

Yana isa aka daurata kan gadon marasa lafiya a kawuce da ita in da za'a bata taimakon gaggawa.

Yusurah yauma zaune take kamar kullum tana abin da ta saba tunanin wanda bai ma san tana yi ba gashi kullum sai ta tura mai messages kusan sau uku a rana tun tana turawa ta ɓoye number har ta koma da nomal number ga shi bai mai do mata da amasa.

Ammie tana cin abinci taji gabanta ya faɗi ta dafa ƙirji tace "ya Allah me yake shirin faruwa da ni ne?

Wannan wace kalar ƙaddarace kullum hankalinta a tashi' tana roƙon Allah ya bata ikon cinye ƙaddarar ta.

Umma ko mai ta tuna sai kawai tayi murmushi ta tashi ta haɗa kayanta tace ma Yaranta "idan sun ga dare Abbi Bai dawoba su rufe gidan da yake Yaran sun ɗan
girma dan ɗayan ya kusa Amir da to suka amsa mata suna kuka tace kar su damu za ta dawo.

Har Umma ta fara tafiya ta tuna kwana biyu basu haɗu da Ladidi ba ta koma ta tafi gidan su Ladidi ta na zuwa ta yi sallama kamar ta Allah Amarya ta gani a waje tana shanya suka gaisa Nan ta tamabaye?

Ladidi Amarya tace "tana ɗaki ba ta da lafiya "subuhanal" in ji Umma tana shiga cikin ɗakin.

Asibiti.Likitoci sun samu numfashin Amira ya dawo amma wani tashin hankali ta manta komai da kowa ta koma kamar jaririya hankalin likitoci a tashe suka fito suka faɗa ma Abbi shi kan shi sai da yayi kuka sosai Amir kam faɗuwa yayi ganin yar uwarshi ba ta gane shi ba.

Wani ne Dr Habib ya ɗau ke shi cike da tausaya
wa ya tafi office dinshi dashi.

Ladidi tana ganin Umma ta hau washi baki ta na cewa "yau ke ce a gidan nan sanu da zuwa" Turuss Umma tayi ganin Ladidi a zaune ƙafa duk bandeji.

Abdul yana zuwa unguwar ya kira wanda yayi musu bincike yace "ko ka san asibitin suka tafi."

Abbas yace "bari na kira Abbi yakira Abbi." ya faɗa masu sunan asibitin suka tafi suna zuwa Abbi yayi masu iso.

Bayan sun shiga ɗakin Abdul ya kalle Amira cike da tausayawa yace "Amira ya jikin?"

jin shuru kallona yayi kafin yayi magana Abbi yace "ta samu matsalan kwakwalwa." saboda ruɗewa sai da Abdul ya tashi tsaye.

Kuma a dai -dai nan kiran "Eshan ya shigo wayan shi.

DAFIN ZUCIYA

✏️By Fatima Binta Hussain✏️

https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Yan' uwa fatan anyi Jumma'a lafiya Allah ya maimaitamana kar a mana ta da salatin Annabi Allah ya amsa ibadunmu Amin

Bisimilahi Rahamanur Rahimin

Page 23

Umma ta ida shiga ɗakin Ladidi Umma tace "me zan gani haka me ya faru?"

Ladid tace "ke dai zauna kisha labari." Umma ta zauna Ladidi ta faɗa mata duk abinda ya faru.

Umma tace "kan bala'i kuma kika barta."

Ladidi tace to ai ina nan zan dau fansa dan walahi bazan hakura ba."

Ammie zuwa yanzu hankalin ta ya kasa kwanciya dan tabbas da abinda yake faruwa da yaranta dan hankalinta ya kasa kwanciya ta yanke shawaran kiran abbi taji lafiyar yaran ta?

Abdul ganin yarda hankalin shi yatashi kuma ga kira yana shigo wa wayan shi ya kasa ɗaga yasa likita ya kamshi ya zaunar da shi ga kiran Eshan yana ta shigowa ya kasa ɗagawa ganin kiran na yawa yasa ya kashi wayan.

Umma tace "nima ina cikin yar damuwa bada yawaba amma zan kawo karshin komai."

Ladidi tace "me ya faru?"

Umma tace wancan shigiyar yarinyar ce Kalil yace ya ganta da wani wajan sana'a." nan Umma tafaɗa ma Ladid abin da ya faru.

Ladidi tace "ai dama ta mutu kowa ya huta."

Umma tace "ai ko a haka taji jiki."

Ladidi tace "to yanzu tafiya zakiyi?"

Umma tace "zan tafi can garin mu wajan bokan ruwa can zanji aikin shi kamar yan kan wuƙa wajan shi zanje ya min maganin kowa har shi kanshi Abbin zai gane.

Eshan hankalin shi ya kasa kwanciya don bai taɓa kiran Abdul yayi mai haka ba anya ba da abin da yake faruwa ba?

Yana cikin wanan tunani
Ahmad ya shago offic din shi ya na ta sallama bai jiba sai da Ahmad ya taɓashi nan ya ɗago ya kale shi yace "Abokina ina cikin damuwa bansan me ya same Amira ba."

Amira ya maimaita cike da mamaki yana kallon Abokin shin yace "wacece Amira kuma nidai ban san ka da wata mace ba?"

Eshan yace "dama nace maka idan nadawo zan baka labari."

Ahmad "yace inajin ka."

nan Eshan ya kwashi komai ya faɗa mashi Ahmad ma yayi mamaki sosai kuma yaji tausayin Amira da Amir.

Amira Kam ta rasa gane wace ce ita? dan ko sunan ta bazata iya tunawa ba ita gani take bata san kowa ba amma tana ƙoƙarin tuna wani abun sai ta kasa.

Mom tana ta murna saura kwana goma a gama azumi ko ta samu taje wajan boka dan tana jin haushi yanda yusurah ma bata damu da ita ba da ta fara mata magana sai ta fara mata wa'azi gashi kuma tace ita yanzu bata son Eshan ita kuma Mom ta dage dole sai Yusurah ta aure shi ko zatayi yawo bakaya.

Amir bayan ya farka daga bacci Dr Habib yasa shi yaci abinci yashi magani.

Amir yace "Ni wajan yaya za je." fin Amira Dr Habib ya rakashi yana shiga ya ruga wajin Amira ta Kama kanta kamar zata yi magana.

*DAFIN ZUCIYA*

Bisimilahi Rahamanur Rahimin

Page 24

★★★

Umma sun rabu da Ladidi akan idan ta ta samu sauƙi za taje wajen bokan da kanta.

Daga nan Umma na fita daga gidan Ladidi kai tsaye inda zata hau motar garinsu ta nufa.

Abbi kam hankalin sa ya kasa kwanciya gashi ya rasa yanda zai yi ya faɗa ma Ammi idan ta sani wani hali zata shiga? wanne kallo kuma zata yi masa.?

Abdul kuwa dan ya kwantar ma da Eshan hankalinsa yasa shi ya ƙira shi ƙira ɗaya ya ɗaga. Yana ɗagawa ya fara tambayan shi ina Amira wani hali take ciki?

Abdul yace "kwantar da hankalin ka tana lafiya ta samu bacci"

Ajiyar zuciya Eshan yayi yace"
"To ya ƙarfin jiki?."

Wani ɗan numfashi Abdul yayi kafin yace "Alhamdulilahi taji sauƙi sosai So ka kwantar da hankalinka In Sha ALLAH babu abinda zai faru."

Aliyu Haydar yau dai haka nan yaji yana son yau ya maida amsa yana so ya san wacece wannan meyasa takiyi yi mai wanan message?.

Yusurah tana zaune taji shigowan saƙo tana dubawa taga number Aliyu Haidar ce Dan haka gaban ta yana faɗuwa ta duba taga an rubuta wacece ke? Meye dalilin ki na ƙirana?...

Wani murmushi Yusurah ta saki tare da gyara kwanciyar ta ta rubuta masa zaka sani ne amma ba yanzu ba.

Umma ta isa Garin Zamfara lafiya kai tsaye gidan su ta wuce.

Tana zuwa mahaifiyarta ta tmbayeta me yake faruwa ta ganta haka?

Daya ke Umman halin Mahaifiyar ta ta ɗauko bata ɓata loƙaci ba ta faɗa ma ta abinda ya faru.

mai makon tayi mata nasiha sai ta ƙara zugata.

Amira tana so ta tuna wani abu amma ta ka sa.

Amir ce wa yake "Dan Allah ƴar Uwata karki ce kin man tani karkice baki san ni ba." Haka yake ta sambatu kamar wanda baya cikin haiyacin shi.

Ganin hakan yasa Dr Habib yazo ya kama shi ya fita dashi yana bashi haƙuri.

Amira suna fita ta fashe da kuka tana tausayin kanta bata san me ya same ta ba amma ita tanajin ta manta wasu abubuwa masu mahimmanci a cikin rayuwarta.

Abbi Yana cikin tunanin ta yanda zai sanar ma Ammi dai-dai loƙacin ƙiran Ammin ke shigowa wayarsa Wani kalan muguwar buga yaji zuciyarsa tayi masa kasa ɗaga ƙiran ya yi.

Ammi kam ganin bai ɗaga ƙiran ba yasa ta ƙara ɗaga hankalinta, hakan yana nuna mata cewar da abinda yake faruwa kenan lallai akwai abinda yake faruwa kenan.

Sai da tayi ƙira uku kafin Abbi ya ɗaga jiki a matuƙar sanyaye.

Ammi na ganin ya ɗaga ƙiran ta fesar da wani numfashi kafin a hankali tace "Ya yara na fatan suna lafiya dan haka kawai naji jikina na bani da abinda yake faruwa dasu ka faɗa min suna lafiya ko akasin hakan?"

Ɗan sharce gumin daya feso masa Abbi yayi kafin yayi ƙarfin halin furta. "Haba Aisha babu ko gaisuwa sai a kama tambayan yara kuma?"

Sai loƙacin Ammin ta tuna da cewar basu gaisa ba duk da Abbi Yana ɓoye damuwan shi sai da Ammi ta gane tace "Ina yarana?" Haka kawai Abbi ya samu kanshi da ce ma ta suna lafiya kai tsaye tace "Ka haɗani dasu to!" Kai tsaye yace da ita "Bana gida idan na koma zan haɗa ku"

Haka suka yi sallama ba don Ammi ta yarda da abinda Abbi ya faɗa mata ba.

Eshan wani mafarki yayi wanda ya tada mai hankali a firgice ya tashi bakinsa ɗauke da addu'a sai kawai ya tashi ya shiga bayi ya yi alwala ya dawo ya tada sallah, sai da yayi raka'a takwas sanan ya dakata kafin yayi addu'a sosai wanda wayan cin addu'ar akan Amira ce yayi ta.

Ladidi kuwa tana ta samun sauƙi a hankali gobe za a kwance ƙafar ma .

Amarya kam tana abinda ya dace dan ita tace bata yi yi ma Ladidi abin da take mata ba idan tayi abinci tana bata.

Eshan bayan ya gama sallah ya koma ya kwanta amma bacci ya ka sa zuwa.

*BY Fatima Binta Hussain ☑️*

DAFIN ZUCIYA

✏️By Fatima Binta Hussain✏️

https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Page 25
✨✨✨

Eshan tunda safe ya ya shirya koma wa Abuja.

Ogan shi ya kirashi yace yayi hakuri da tafia akwai wani aiki mai mahimmanci babu yadda ya iya haka ya haƙura.
Chapter 9 · 0% Book details