← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 32

Sashe 27

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma ta batulu abokin haidar me suna Muhusin ne ya sa mata ido ya hana ta sakat ita kam ta BATULU ganin hakan yasa take ta maka mashi harara harda su murguɗa baki.

> Wanan abun da tayi mai makon yaji haushi sai yaje wata kalar soyayyar ta me ratsa zuciya ta shige shi.

She Kam Adam ya kasa haƙura sai da yazo ya samu pending na zaune tana shan fura ya ƙara so da sallama dama pending tun da taga yana kallon ta take addu'a Allah ya sa yace yana son ta da ita wan kan shi ya cize ta.

> Cikin jan aji pending ta amsa mashi ya ce "am idan babu matsala ina son mu zama abokai?"

> Sai da pending ta yamutsa fuka san nan ta ce "friend fa kace? ya zu mu zama friend kana namiji ni kuma mace."

Dariya ya yi ya ce "Please ki bani number ki."

Ta amasa wayar sa ta saka mashi.

> Can na hango ta batulu sun haɗe da Muhsin ana ta shan love

Komai ya kan kankama an shiga cikin abinda da ya tara mutane dumu dumu

Abin mamaki anguna shigar shi ƙalar ɗaya amare ma haka idan kaga yanda suka haɗe kan su sai kayi tunani sun daɗe tare da junna dan shi Haidar halin su kusan ɗaya ne da Eshan.

Taro iya taro su anguna da amare har filin wajin sukaje wai zasuyi kewon shanaye abin dai sai son barka a haka taro ya tashi lafiya kowa ya kama gaban shi.

Umma yau aka fito da ita domin a saurare ta a kuma yanke mata hukunci ita ma.

Bayan an fito da ita alƙali ya ce "ko zamu iya sanin dalilin ku na aikata abin da kuka yi keda mahaifiyar ki?''

> Umma ta ce "eh" nan ta shiga basu labarin irin yanda Mama take tilasta mata akan wasu abubuwan kuma ita ce tayi mata dole akan zuwa wajan bokaye da na nuna mata babu kyau sai tace zata tsine min hankali na ya tashi hakan ya sa na bi umarnin ta ina son mahaifina sosai amma mama ta saka min tsanar sa da yan uwana ana haka na samu miji nayi aure shekara ta biyar inda yara biyu auren ya mutu bayan ƴan shekaru na ƙara samun wani mijin nayi aure yana da yara da mata amma haka mama ta saka min tsanar su wanda ya sa mijin mu ya saki uwar ƴa'ƴan shi ni kuma ya kora ta da yaran ta na ce ina son kana nan ciki ba dan ta so ba saboda mahaifin su ya sa ta ba da yaran nikuma tun da muka koma sabon gida Mama take ta sani na cutar da yaran nan Umma ta shiga basu labarin abin da tayi masu Amira tunda ga farkon abin da ya faru.

Shi kan shi alƙali sai da ya zubar da hawaye jin kalar wannan rashi imani kowa da ke cikin koton hankalin su ya tashi labarin yaran ya tsaya masu arai.

> Alƙali ya ce "ko zamu iya ganin yaran da mahaifin su?"

Umma ta ce "wallahi ban sani ba Ni yanzu kunyar su nikeje sai dai na bada number mahaifin su a kira."

Umma ta bada numbern Abbi aka kira Abbi yana tare da abokan shi harda wainda suka zo daga ƙasar waje da yake za'a yi taron buɗe wani Company na motoci.

> Cikin natsuwa Abbi ya ɗaga kiran da aka yi ma shi ya yi sallama aka amsa daga ɗayan bangaren aka ce "suna na Malam Aminu alƙalin babbar koton musulunci ta Zamfara."

Abbi ma ya faɗa mashi sunan shi da koton da yeke aiki.

> Alƙali ya ce "ma sha Allah kace duk mune idan an gama Shari'ar nan zamu yi magana aikan aikin mu idan babu matsala?"

> Abbi ya ce "babu matsala kar ka damu."

Nan alƙali ya shiga kora mashi bayani kamar yanda Umma tayi ma shi kuma alƙali ya sheda ma Abbi suna son ganin Amira da Amir don aji ta bakin su.

> Abbi ya numfasa ya ce "gaskiya ba za'a samu ganin su ba saboda Amira jibi ne bikin ta ana hidimar biki to idan sun zo me zasu yi anan?"

Alƙali ya ce "shike nan amma ko ta waya ne a haɗa mu da su saboda muna son za'a yi masu Shari'a ne."

Abbi ya ce " a'a ba sai an yi Shari'a ba ki barta da halin ta kawai kuma ina fatan saƙon sakin ta ya iso ma to?"

Hankalin Umma a tashi ta ce " na shiga uku yanzu saki na kayi?"

Abbi ya ce "ni babu ruwana ku yanke mata hukuncin da ya dace da ita."

Bayan an gama waya da Abbi aka yanke ma Umma hukun cin zama gidan yari na shekara goma kuma babu beli.

Rana ba ta karya sai dai uwar ɗiya taji kunya yau take jumma'atu babba rana jumma'a me ciki da farin ciki ga wainan family ana ta shirn tafiya daurin aure wanda za'a daura karfe 02:30pm babban masallacin cantural moqus Abuja.

> Daure aure ne wanda ya haɗa manyan mutane tun daga kan sojoji yan siyasa ma su kuɗi kai ku san masu kuɗi ta talakawa ko wa na shirin halartar wannan gagari rimin bikin ƴan gata.

Bayan sallar juma'a aka sanar da daurin aure

An daura auren AISHA MUHAMMAD USAMN AMIRA

TARE DA MIJIN TA MUHAMMAD ESHAN ABUBAKAR AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYAR

YAN ZU KUMA ZA'A DAURA AUREN

ALIYU HAIDAR MUSA

TARE DA DA MATAR SHI YUSURAH BASHIR

AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYAR

DAGA NA SU YUSURA AKA DAURA NA

ABDULLAHI ABDULLAHI TARE DA MATAR SHI

FATIMA ABUBAKAR FARHA

AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYAR

SANAN AKA DAURA NA

AHMED UMAR

TARE DA MATAR SHI HAFSAT IBRAHIM
AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYAR

Ya Allah zo kaga murna wajan anguna duk daurin auren nan da ake Eshan yana nan yana yin video ana gama daura wa ya tura ma Amira san nan ya tura mata message ya ce ta kunna data ya tura mata da wani abu.

> Suna fito daga Masallaci suka ga jirin sojojin wai sai sun yi masu fart haka suka saka anguna a tsakiya suna masu fart abin ya burge kowa kuma ya ƙayatar daga nan aka shiga photo na.

Amira suna zaune ita da Hafsat suna ta kuka ga ƙawayen su zagaye su wayar Amira na hannun pending taga

DAFIN ZUCIYA

By Fatima Binta Hussain

MRS NASIR

https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

Alhamdulilah Allah na gode maka da ka bani ikon cigaba da rubuta wannan littafin ya Allah ka bani ikon gamawa lafiya ina me miƙa godiya ga wainda ku ka ƙarfafa sani gaba akan na ida wanan litattafin na gode sosai Allah ya saka da alheri

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 56

> Tana shiga ta buɗe video din gashi ƙarar wayar ya kai ƙarshe tana kunna wa taji ana ce wa an daura auren ta ai hannun ta ya fara karkara da saure nabila ta amshi wayar ta saka su tsakiya ta kunna suna ji daga nan suka koma kallon photona pending da ta batulu ne suka samu pepar suna yagawa suna masu liƙi suna yi waƙar SUN ZAMA DAUKO HULA SUN ZAMA DAUKO WANDO Dai dai lokacin Aka shigo da Farha da Yusurah dama sun haɗa kan su tere za su yi komai nan fa ɗaki ya hargitse ƙawayen su suka saka su gaba suka dame su da surutu.

Su Eshan ana gama fart Suka fara zuwa gidan su suka gaishe da mami da Abba san nan suka wuce gidan Abbi tunda ga nesa suka ji kiɗa na tashi suna ta huwa suna ƙara jin sauti kawai sai gani suka yi Eshan ya fara tiƙar rawa.

> Ahmed ne ya ce "yau mun bani wai kai baka da man kaine? A ko ina sai ka nuna halin ka ko."

Wasu daga cikin abokan su suka tayi mashi video wasu kuma na taya shi wani ya ce ma Ahmad "Kaga Malam yau ranar mu ce yau ranar farin ciki ce."

Kowa sai kallon Eshan suke dan ya burge mutane wasu daga cikin matan dake waje kusan ko wacce ta mutu kan shi ganin kamar ba zaiyi faɗa ba ya sa wata ta tashi zata tin kare shi wani soja ya daka mata tsawar da ta kidimar da ita tara sa in da zata yi hakan ya sa suma sauran ku kama kan su dan sunga ruwa ba sa'ar kwando ba ne.

Suna shiga get din Suka hango a shi su ta batulu ne suka samu speaker masu mugun ƙara suka saki kiɗan nan suke ta rawa kamar ba gobe ga amare zaune kan kujera suna kallon su.

> Suna hango angona da abokan su suka ƙara kiɗan waƙara har wani dum dum kaje ji a kunnan ka suna zuwa wajan su ka fara yi masu liƙe abokan angona wasu mara sa kunya da ga ciki suka shiga ana rawa can na hango pending da Adam sunyi nasu gefen suna rawa.

Sukuma angunan ganin duk abokan su sun shiga filin rawa ya sa kowa ya tafi gun amaryar shi.

> Amira na zaune da wasu suna fira kawai sai taje an kama hannun ta ana ja tana ɗagowa taga gogan dama tasan babu me wannan aikin sai shi.

Haidar ma wajen Yusurah ya tafi Ahmad kuma wajen Hafsah dama tunda Farha ta hango Abdul yayo inda suke ta tashi ta ƙara sa wajan sa.
Chapter 27 · 0% Book details