← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 32

Sashe 23

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Amma wani abin mamaki wannan mutumin yana gani na naga ya tashi hankalin shi yayi mugun tashi yana nuna ni da hannu ya na ce we wannan ita ce warda kike so ayi aiki akan ta to ki sani babu wanda ya isa ya taɓa wannan yarinyar donmi akwai wani haske a tattare da ita duk wanda yace zai cutar da ita akan shi abin zai ƙare ya ƙara sa maganar ciki tsawa,

sosai hankalin Umma ya tashi jin abinda boka ya ce hakan ya sa ta ce to tunda ni aikin ba zai yi a kaina ba to sai a maida shi kan uban su shida ma namijin na san yanda zan yi dashi na san shi idan ya girma zai yimin amfani haka tasa boka yayi aiki akan ka ya bada wani abu ya ce tazo ƙasan gadon ka ta sa ta ka kwanta zaka manta damu duk abin da tace shi zaka yi muna fitowa tayi min kashe di tace ida taji wannan maganar ta fita to sai ta kashi ne."

Ta nufa fasa ta ce "tun ranar da muka dawo tayi maka wannan abun tun daga ranar naga ka daina kula mu baka damu damuba babu ruwan ka idan munci abinci ko ba mu ciba sutarar mu duk ta kwashi komai na mu haka ta mai damu ma ra sa galihu bamu da ƴan cin kan mu wata rana ƙawarta Ladidi tazo naji tana bata labarin yanda aka yi ta raba ku da irin aikin alfashar da suka da farko abbi ka fara da tsar mu wanda daga baya ta kaiga kun rabu hankali na ya ƙara tashi sosai,

Gashi banda wanda zan faɗa mawa kowa gudun mu yake na rasa inda zan sa kaina rana zafi inuwa ƙuna gashi a lokacin Amir ba wani wayo ne da shiba watara na munje islamiyya wani malamin mu yana mana karatu ya ce idan mutum yana da damuwa ya tashi da daddare yana Sallah ya faɗa ma Allah damuwar shi In sha Allah zai samu sauƙi kuma Allah zai amsa hakan yasa kullum sai na dinga tashin Amir munayi yin sallah muna roƙan Allah ya fitar damu halin da muke ciki tun Amir baya son tashi har ta kaiga wani lokacin she yake tashi mu wata rana bamu san dalili ba Umma ta hana mu zuwa makaranta ta koma daura mana tallah azaba ta ƙara mana yawa wanda duk abinda ake baka iya yin komai akai wani lokacin har dukan mu kake amma bana damuwa saboda nasan ba'a hankalin ka kake ba wata rana muna zaune kazo kace mu shirya zaka kaimu makarantar boko ta kalle Abbi tana cewa "ka tuna?"

Abbi ya ce "tabbas na tuna."

Amira ta ci ga ba da cewa bayan ka kai mu makarantar wata rana munyi ma Malamin mu laifi ya ce ba zamu koma gida ba sai kowa ya ga ma tafiya hakan yasa bamu dawo gida da wuri ba ina dawo wa Umma ta kamani da duka tana cewa na tafi yawon iskanci sai ta karyani ta bugamin wani ƙaton ƙarfi a ƙafa,

Kowa hawaye yake Eshan yakasa tsare ta da idanu.

Ta ci ga ba da cewa tun san da ta buga min wannan abin ƙafata naji kamar bata jikina kwana na uku a ɗaƙi ban iya taka ƙafar ta kumbura Sosai Umma ganin yan da ƙafata ta koma hakan ya sa tace maka ai na ɗine.

Saosai Amira ta faɗa masu irin azabtar War da Umma tayi masu har zuwan sanda Abbi ya fara dawo wa dai dai da sanda Umma tabuga mata abu akai wanda hakan yasa ta man ta komai da haɗuwar su da su Eshan har zuwa yanzu.

Amira na kaiwa karshen maganar Wasu daga ciki suka fashi da kuka har da su Farha Ammi kam ta sanƙare jin abinda Umma tayi masu dama ita tasan Abbi bazai masu ha ka ba yaya Faruk ma saida yayi kuka.

Abbi ne ya tashi ya tafiya ƙama ƙafar Amir da Amira Yana kuka yana cewa "su yafe mashi dan Allah."

Yaya Faruk ne yazo ya kama shi yana cewa "haba Abbi ƙaddara ce tana kan kowa mun san bayin kain ka bane ka dauka wannan abin a matsayin ƙadddar ka kowa da ƙalar tasa ƙadddar wata ƙaddarar zata zo maka da sauƙi wata kuma akasin haka yanzu da kayi haƙuri Baga shi ka cinye jarabawar kaba ta wannan bangaren gashi duk wani abu da ake ɓoyewa ya fito."

Yana gama maganar abbi ya rungume shi san nan ya koma wajan Ammi yana cewa "dan Allah A'isha ki yafeni wallahi ina sonki."

Ammi ta ce "nima na sani nasan cewa ƙaddara ce."

Babu ɓata lokaci Abbi yace ma Ammi "ta yardda a maida auren su ita kam tace sai tayi shawara."

Abbi ya dauƙi wayar shi ya kira Mansur yace ya haɗa shi da Babansa bayan ya haɗa su ka gaisa cikin girma mawa Abbi ya ce yana so a faɗa ma Umma ya sake ta.

Koda Baba yaji abinda Abbi ya ce bai wani tada hankalin shi ba ya ce "Allah yasa hakane ya fi alkairi."

Daga nan kuma suka ci ga ba da fira kamar sun saba amma idan ka kalle su zaka fahinci akwai damuwa aƙasan zuciyar su.

Abbi wani zazzaɓi ne ya kama shi nan yakama rawar sanyi cikin tashin hankali suka dauƙe shi suka tafi asibiti suna zuwa aka ce jinin shi ya hau kuma zuciyar shi na ciwo sosai hankalin su ya ƙara tashi sun san ba komai ne ya jefa shi wannan halin ba abinda Amira ta faɗa ne.

Yusurah koda suka shiga shopping din amma taƙi daukar komai sai da shi Haidar yake dauka ganin abin ya fara zama hauka yasa ta da Katar da shi dan harda su akwati sarƙa atamfofi lass shadda pant pat Babu kunya yake ta dauka wasu abubuwan kamar wanda zai haɗa lefe bayan ya gama siya aka sa masu a but ɗin mota sanan suka kama hanyar gidan su Yusurah suna tafiya suna fira.

Yusurah ta ce "gaskiya wainan kayan sunyi yawa rage wasu kasa a lefe don idan Daddy yaga wainan uban kayan zaiyi faɗa kuma zai sa amaida su."

Dariya ya yi yace "idan yayi magana kice mijin kine ya Baki."

Harara ta watsa mashi tace "tunda ce maka aka yi bani da kunya da za ka ce na ce haka."

Dariya yayi yace "to shekenan sai ki rage."

Ladidi bayan an fito da ita CS ana ta jira ta farka abu shuru har kusan awa uku bata farka ba ganin shurun yayi yawa yasa a ka kira babban likita yana zuwa ya duba ta yace "sai dai kuyi haƙuri Allah yayi mata rasu wa."

Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji un KULU NAFSIN ZAIKATUL MUT.

Hankalin su ya tashi kowa ce wa yake "inalilllahi wainna ilaihi ra'ji." hankalin yaya yafi na kowa tashi san gani yake kamar shine ya kashe ta saboda duka da yayi mata.

Malam ne yai ta kwantar mashi da hankali yana cewa "ya daina cewa haka Allah ya ruba tanan aljalin ta yake."

Aka yi ciki ciki aka amshi gawar daga asibi kai tsaye gidan Malam aka wuce da gawar.

Amarya ganin gawar ladidi yasa hankalin ta ya tashi kamar ta hauka ce haka ta koma dan mutuwar ta shige ta sosai.

Nan aka yi ma marigayiya Ladidi wanka aka yi janiza aka kai ta gidan ta na gaskiya.

Sai bayan andawo jana'iza sai ga ɗiyar Ladidi Mariya ta dawo daga yawon ta bata san ma an yi rasuwar ba koda akafaɗa mata rasuwar bata wani damuba sai cewa tayi ma ita ta sani.

Nan mutane akai ta zaginta ita kam ko a jikin ta.

Bokan dake masu Ladidi aiki yan cikin wannan ɗutsan yana haɗa tsaface tsafan ce wata ta kama a cikin wajan kafin ya fito watar tagama cin jikin shi.

Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm wannan wani kalar bala'i ne ka mutu kana saɓa ma Allah ya kada kasa muyi mummunar ƙarshe ya Allah kasa mu mutu muna bauta maka.

Wasu mutane ne zasu je gona suka ga gawar Boka dayake kusan kowa ya san shi sunyi ko kore shi daga garin abin ya gagara hakan yasa suka yi murna suka zo cikin gari aka faɗa ma mutane suka zo babu wankan gawa babu komai suka yi rami su rufe shi.

Abbi da kayr jikinshi ya dawo dai dai bugun zuciyar shi ya sai tu san nan suka samu hankalin su ya kwanta duk suna waji daga Ammi sai Abbine a ɗakin da wannan damar Abbi ya ƙara roƙan ammi akan tayi hakuri ta koma gidan shi dam ɗazu kunyar su Eshan ne ya hana ta ce ta amince ta ce mashi ai ita yarda sosai yaji daɗi dan haka ya kira yayan Ammi ya faɗa mashi babu ɓata lokaci ya ce da asuba za a maida auren.

A daren aka sallami Abbi daga asibiti suka wuce gidan yaya Faruk bayan sun aje su Ammi a gida .

Washa gari sunje sallar asuba kasa sanar da daurin aure jin auren da aka daura yayi mugun basu mamaki dan basa da masaniya aka anan sukai ta murna har suna tsokanar Abbi.

Gidan yari Umma sun fita suna aiki kawai aka ga ta fasa ƙara ta yanke jiki ta faɗi haka aka dauke ta aka kaita asibiti amma an duba ba a ga abinda ke damunta kuma gashi tana hauka abinda basu sani ba duka asirin da Umma tayi ma mutane ne ya koma kanta ya haukatar da ita.

Abokin Abbi kam tunda asuba suka kamu hanya she dasu kalil.

Monday KOTO

Yau ta kama za'a koma koto bayan anji koto aka gabatar da shedu inda aka gane su Umma babu gaskiya aka yanke ma Mama daurin rai da rai inda ita kuma Umma aka kaita gidan mahukata idan ta samu lafiya a yanke mata nata hukuncin.

Mutanan gidan duk da haka sunji babu daɗi amma dole sai ana yanke ma irin su hukun ci idan ana barin su haka ba'a yanke masu hukunci za aita samun ɓata gari.

Yau ne aka kawo kayan Sa rana Yusurah inda babu ɓata lokaci aka saka sati biyu.
Chapter 23 · 0% Book details