← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 32

Sashe 13

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

By Fatima Binta Hussain

https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Bisimilahi Rahamanur Rahimin

Page 33

Eshan sun tafi gidan su Amira su uku dashi da Abdul sai Farha.

Suna zuwa suka iske Amir yafito zai saiyo ruwa ya tsaya suka gaisa ya rakasu har ciki gida dama Abbi yana nan amma Abokansa sun tafi suka shiga ɗakin Abbi suka gaisa Abbin yasa aka kawo masu abinci da ruwa da lemuka suka zauna suka kwashi gara.

Farha ce tace to "wai ina auntyn ban gantaba".

Ladidi tunda tashiga ɗaki bata ƙara fituwa ba tana ta fama da azaban cewo gashi tana so ta koma wajin boka.

Mom yau ta bar gidan ta tafi gidan ƙawarta warda zasu yi tafiya tare.

Yusurah yau zasu haɗu da Aliyu Haidar jiya ya tura mata message yace yana so su haɗu.

Umma ta kamo hanya zata dawo Abuja sun ma kusa isowa ta kira Abbi ta faɗa mashi suna hanya sun kusa isowa.

Shi kuma Abbi ya shirya ma dawowar ta dan yanzu dai-dai yake da ita.

Aliyu Haydar Allah sarki ma harkurci mawadaci fanshon Baban shi ya fito yaje ya amsa ya sai ma su gida babba wanda harda sashin shi dan idan yayi aure nan gidan zai tare da matar shi ya saya masu kayan abinci kayan sawa duk wani abu na ɓuƙata ya sai masu.

Harda ragowa dayaba ma Mama kuɗi tace ya saya mota ko ya rage wasu wahal wahalun yaji shida Abokin Uzaifa suka sayo muta kirar Mercedes Benz.

Amira tana zaune a ɗaki tana kwaliya zasu fita unguwa itada ƙawarta Hafsat sunyi kyau sosai Amir ne ya shugo ɗakin yace "idan kin gama ga su Yaya Eshan cen sun zo harda wata".

Amira tace "to yaushe suka zo ai bansani".

yace "to idan kin gama suna falon Abbi".

Amir na fita Hafsat tace "kace yau nazo da sa'a zan haɗu da wanan Yayan naki".

Amira tace "ai kam dai zaki ganshi".

Hafsat tace "anya Amira ba son ki yake ba"?

Amira tace "a'a wani kalan so kuma no badai niba ba sona yake ba haɗuwar jini ne".

Hafsat tace "haka kike gani ko tace haɗuwar jini na zama soyyaiya haka zalika abota tana zama soyyaiya so bawani abu bane dan yace yana sonki".

Amira dai bata yarda ba daga haka suka fito zuwa falon Abbi.

Ladidi babu abin da take yi sai shiga ruwan zafi ta yanke shawarar gwara ta koma Asibiti ko zata samu wani Likitan ya duba ta dan tana ganin bayanin wancan ƙarya ne kuma magunguna da ya bata basu mata komai sai ƙara mata azaba.

Amira da salama ta shiga falon tana salama su duka suka amsa mata salama shi kam gogan sai photo daya ke ta mata babu wanda ya sani.

Farha sai kallon su take hakan taji sun birgeta ta tashi ta isa wajan su tana ce "barka yan uwa ya kuke"? Amira tace "muna lafiya fatan kema hak"? Farha tace "lafiya sunan Farha". Hafasi tace "ita Amira ni kuma Hafsat".

Suka ƙarasa ciki Amira tace "Yaya Abdul ina wuni ya Sallah"?

Yace "alhamdulilah ƙanwata"

Hafsat ma ta gaishe shi.

Sanan ta kalle Eshan "tace Yaya fatan kayi sallah lafiya"?

Ya maka mata harara yace "haka ake gaisuwa ko"?

Amira tace to "ina wuni anyi sallah lafiya"? ganin yanda take maganan tana turu ɗan ƙaramin bakin ta ya sa yace me "kuma aka yi daga nace ba haka ake gaisuwa ba"?

Tace bakomai yace "ina zaku ji tace unguwa yace ban yarda ba babu inda zakiji"?🙄🙄🙄

DAFIN ZUCIYA

✍️By Fatima Binta Hussain✍️

https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM

https://whatsapp.com/channel/0029VbAho5W8V0tlD03a4Q1g

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 34

Amira jin Eshan yace baza ta ba yasa ta haɗe fuska tana cewa "Yaya Abdul ka ganshi ko"

Abdul sai dariya yake yi yace "haushi yaji ganin munzu zakice mana wai zaku je unguwa so ayi haƙuri da zuwa unguwan yau".

Farha tace "saka min friend a gaba akam sai munje ku tashi mu tafi"

Wani wawan kallo Eshan yayi mata yace "to ga hanya ku tafi idan ban fasa ma mutum baki ba"

Amira jin abinda yace ya sa ta fashe da kuka tana bubuga ƙafa.

me Amir zaiyi inaba dariya ba.

Hafsat tace "ikon Allah wai dama haka kike yi ma mutane wannan iskancin ko to walahi zan yi maganin ki"

Farha tace kuzo "muyi photo kawai tunda ya hana mu fita sai mu rungumi sorry dan wallahi tunda yace haka ba zai barmuba."

Suna fita Abdul yace "haba Bro bai kamata ace tun yanzu ka fara nuna mata haka ba kama ta yayi kabi komai a hankali please".

"Ya ƙarashi maganan kamar zai yi kuka"

Eshan yace "wallahi na kasa control din kai na ne amma shikenan".

Ladidi yau tafito tana tafiya tana gwale ƙafafu zata fita daga gida, taji Malam nace wa "wai ke kam lafiyar ki qalu kudai ƙafar bata warke bani"?

cikin masifa tace "ina ruwan ka tunda aka kwance min ƙafan kataɓa tamabaya ta jiki sai yanzu dan gulma zaka zo ka tambayeni".

Malam yace "dan na tambaya ai banyi laifi ba kuma ai ba zama gidan kike ba kullum ki can yawo".

tace "anyi din" yace "yanzu kama zanyi maganin ki idan kika fita a bakin auren ki".

tace "kan bala'i yau ni kake ce ma haka? to wallahi zan yi maganin ka ni dai ko"?

tana ida sa maganan ya daga hannu ya kwasa mata mari san nan yace "ni kike ce ma haka ko to zan gani cikin ni dake waye mijin kece mijin ko nine ya kama ta yana ja ya kaita ɗakin ta ya tura ta yasa key ya rufe ɗakin yayi tafiyar shi".

Aliyu Haydar ya tura ma Yusurah message akan baza su samu haɗawa ba tafiya ta kamashi.

Koda Yusurah taga message din bata ji daɗi tace mashi bakomai.

Amira suna cikin photo suka ji sallaman Umma gaban ta yayi mugun faɗuwa.

Umma na shigowa taga su Amira nata photos tayi kamar bata gansu ba ya shigi falon Abbi.

bako sallama ta shiga ɗakin ganin su Eshan yasa "tace kukuma daga ina?

su kuma sun gane Umma ne saboda tana shigowa yanayin Amir ya chanza.

Suka yi mata banza babu wanda yayi mata magana.

Sai da ta ƙara tambaya?

sanan Eshan yace "kina da matsala damune"??

Umma tace kai "uban waye kai da zaka yimin rashin kunya"???

Yace to "fira nazo wajan matata".

A sukwane Umma tace "wacece matar taka"?

yace "akwai wata da ta wuce Amira"?

Umma bata ƙara magana ba tawo waje da gudu ganin ta fito da gudu yasa suka biyo bayan ta.

tana fito wa tayo kan Amira ta kama dukan ta.

Akuma lokacin ne Abba ya shigo ganin abinda Umma keyi yasa yayi kanta tana ɗago wa kwashi ta da mari.

Umma tace " ni ka mara saboda wainan yan iskan".

Abbi yace "na mare kin sanan yace ko kallon banza kika sake yi ma yarana saina sai na dauki a kanki.

Umma ta kalle Eshan tace "kada na ƙara ganin ga gidan nan tunda ba gidan ubanka bani".

Wani shigin murmushi yayi kafin yace "ai kam zuwa gidanan yanzu na fara idan kinga na dai na zuwa gidanan an daura mana aure da matata ta tare a gidana

End of book one

BOOK TWO

DAFIN ZUCIYA

By Fatima Binta Hussain

https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM

https://whatsapp.com/channel/0029VbAho5W8V0tlD03a4Q1g

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 35

Amira ai bata san lokacin da tayi ɗakin su da gudu ba shi kenan ta ta ƙare she kenan wannan me kan gwandan yaja mata tabbas abinda Hafsat ta faɗa gaskiya ne.

tana cikin tunanin nan sai ga Hafsat ta shigo tana cewa "hhhhh ai ruwa baya tsamin banza, yanzu sai mu fara shirin biki dan nasan Abbi ya riga da ya bashi."

Amira tayi shuru tana jinta.

a waje kam jin abinda Eshan yace yasa Abbi yin hamdala tabbas duk da baisan halin yaron ba yasan zai kula mai da yarinya kuma zai sa ayi mai bin ciki a kan shi.

Umma ce ta yanke mai tunani tana cewa "ai kam ita da aure sai dai taga wasu nayi amma bata ba aure."

Abbi ya kalle yace "yanzu dan Allah bakiji kaunya ba?? wuce ki shiga ciki kuma tunda ke ba Allah bace baki isa ki hana abinda ya ƙaddara zai faru ba haka zalika baki isa ki isa ki hana abinda zai faru ba so duk abinda zaki yi kiyi."

Tun ranar da yan uwansu suka barta asibiti ita da Umma babu wanda ya ƙara zuwa gashi ta ishi mutanan asibiti.

Mansur ne yaje asibitin yana zuwa yaga Mama a wulaƙance babu me kula da ita yana cikin ɗakin wani Likita ya shigo yace "dama muna jiran yan uwanta su zo su dauke ta ta damu mutane gashi ba biyan kuɗin asibiti ake ba."

da mamaki Mansur ya kalle Likitan yace "ba akwai me kula da ita ba ina ta tafi??

Likitan yace "maybe ta gaje ne shiyasa tayi tafiyan ta amma mun kwana biyu bamu ganta ba."

Munsur waya ya ɗuko ya kira Umma yace " tana ina yazo asibiti bata nan??"

Umma tace "eh na koma gidan mijina saboda ni bazan iya wannan jinyan ba."

ciki da mamaki yake saurraron ta kafin yace "owk ai naga mahaifiyar kice bata waniba idan kin barta a wulaƙance wannan kuma matsalar kice."

Umma tace kaga "Malam a kam me zaka tasani a gaba kana min wannan faɗan naga mahaifiya tace bata wani ba."

wani Murmushi yayi kafin yace "zan sa a da ita ban komai ba sobada ina so komai ya faru tana cikin hankalin ta kin ga idan komai ya dai daita iya so sai ta koma yawo a titi."
Chapter 13 · 0% Book details