← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 32

Sashe 30

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

Alhamdulilah Allah na gode maka da ka bani ikon cigaba da rubuta wanan littafin ya Allah ka bani ikon gamawa lafiya ina me miƙa godiya ga wainda ku ka ƙarfafa sani gaba akan na ida wanan litattafin na gode sosai Allah ya saka da alheri

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 58

Ali jika SANNU SANNU NU NE NA KAMAU DA SOYAYYA NAYI BACCI TSAKAR DARE NA KAN JUYA.

Bayan sun gama sai pending da Adam Suka fito aka sakar masu waƙar UMAR M SHARIF wardda ake cewa LAMBA.

San nan aka zo kan amarya da ango Eshan da Amira suka fito aka saka masu waƙar SADAKI NA BIYA SADIKIN TA A SADAKIN AKWAI GIDA AKWAI MOTO ƳAN MATA IN KIKA SONE KIN HUTA.

Bayan sungama aka kira Haidar da Yusurah aka saka masu waƙar NURA M INUWA LOKACIN KI NE YAYI AMARYA YAR AMANA ZOKI JE KI ZAUNA DA MIJI AURE IBADA.

Bayan sun gama aka kira Ahmed da Hafsat aka saka masu waƙar KE NA SAKA BANGON LITTAFINA WANDA YAKE DAUKE DA DUK LABARINA AUREN KI KARSHEN LISAFINA INA NA RASA KI RANAN AN RUFE BABINA KUN JI SAI KU SHEDA RAYUWA NA BADA.

san nan Abdul da Farha aka saka masu waƙar Adam a zango SOYAYYA DAƊI IDAN HAR DAKE ZANA INBA KE WA ZANA KALLA A BAYAN RAI.

Daga nan aka yi abinda ya kamata aka rufe taro da addu'a san nan kowa ya koma mota kamar yanda aka zo suna tafiya Amira ta ce "yanzu ya zan yi da wannan abin kunyar da kaja min ya zan kalle mutane."

Murmushi yayi ya ce "tun da baki san yanda za'a yi ba kawai mutafi gidan mu kin ga an huta kaiki gobe sai dai kawai mozo ayi walima ko."

Harara ta maka mashi daga nan bata ƙara cewa komai ba har suka isa ƙofar gida amma ya hana ta ta fita sai da ya kama bakin ta ya sha me isar shi san nan ya sake abin ya haɗe ma Amira duk kunyar da yasa ta taji bai ishe ta ba sai ya haɗa ta da wata.

Ta samu dai ya beɗe motar wai shi zai dauke ta ya kai ta har cikin daƙi akam da gudu tabi ta ƙofar baya ta shige tana shiga ta bi ta inda baza'a ganta ba ta shige ɗakin su tana shiga ta iske wasu ƙawayen na ta duk sun dawo bata kula kowa ba ta shige bayi tayi wanka ta sanya kayan bacci tana fitowa Hafsah ta shigo tunda suka saka ga tayi wanka suka saka ta a gaba wai ta faɗa masu wankan me tayi.

Banza tayi masu itama Hafsat tana zuwa ta shige wanka dan da ka gansu kasan sun sha wahala.

Amira tana gama shirin ta tazo ta kwanta sai ga Aunty Fatima ta shigo ta ce " Abbi yana kiran ku shida Baba ina Hafsah?"

Suka ce tana wanka itama Amirar yanzu ta ta fito ta kwanta Aunty Fatima ta fara ta shin ta Amma tana ji tayi shuru dan ita wallahi bata san yanda zata yi da wannan abin kunyar ba.

Auntu Fatima ta ce "ban son iskanci kina jina kikayi shuru."

Sai lokacin ta ce "nifa Aunty bazan iya zuwa ba kunya nike ji."

Aunty Fatima ta ce "kunyar uban me kike ji?"

Aunty Fatima ta San abinda AMIRA ke yi ma wa amma dan ta ƙure ta yasa ta tambaye ta.

Shuru Amira tayi.

Hafsat ce ta fito da ga tolet Aunty Fatima ta ce mata "Abbi da Baba suna kiran ku ki shirya mu tafi kirji Hafsat ta dafe ta ce mun shiga ukun mu da wani ido zamu kalle su bayan abin kunyar da muka yi ita Hafsah ma bata san ta faɗa wannan maganar ba.

Aunty Fatiam ta ce "me kuma ku kayi?"

Sai lokacin ta dawo haiyya cinta cikin jin kunya ta fara kame kame wallahi babu komai subutar baki ne.

Dariya suka kwashi da ita jin abin da ta ce.

Haka dai ta Shirya suka saka manya manyan hijabai suka tafi Aunty Fatima ta kama masu hannu san da suka shiga falon sunga mutane da yawa ga Ammi ga Mame ga Abbi ga Baban Hafsah ga yar uwar Mamar ta ga Yaya Faruk da san yanzu ya dawo dalilin da yasa ba'a yi bikin shiba tafiya ce ta kama shi zuwa wani aiki sai yanzu ya samu ya dawo.

Da sallama suka shiga suka zauna suka gaida mutanan falon san nan Abbi ya ce ma "Baba ya buɗe taro da addu'a."

Bayan an beɗe taro da Addu'a nan aka shiga yi masu nashi me tsuma zuciya daga nan suka yi masu Addu'a kowa ya watse.

Mariya basu yi ƙarya ba sun yi abinda suke da shi shin ka fa ce aka yi jallof taji kayan haɗe ga uban kifi da aka sa gasu karas kabeji kokunba sai ruwan ruba da lemuka a ɗakin Malam aka shirya masu komai anayin sallar mangarib Alhaji Tukur ya kira Mariya ya ce "suna waje."

Sai da ta ƙara faisa turare san nan taje ta faɗa ma Mama dama Baba bai kaiga dawo wa masalaci ba.

Taje tayo masu iso su uku ne ta kaisu ɗakin Baba san nan ta basu waje su ci abinci sun ci abincin babu laifi kuma sun ya ba.

Ba su daɗe da gama cin abincin ba sai ga Malam Sa'idu ya dawo cikin girma mawa su gaisa da juna.

San nan Alhaji Tukur ya ke faɗa ma Malam Sa'idu abinda ya kawo shi kuma shi da gaske da aure yake son ta bai so ma a wuce sati biyu ba'a yi bikin ba.

Baba ya yi na'am da hakan kuma ya ji daɗi amma ya ce "su bashi lokaci nan da jibi zai ne me su."

Washe gari

Ƙarfe tara an haɗu wajen walima a cikin gidan za'a yi an sa kujeru ko ina itama Farha an kawo ta nan da yan wasu ƴan uwan su duk sun zo za'a haɗu ayi walimar anan.

Malam sakina Abdullahi aka dauko ita ce zata yi wa'azin an yi walima iya walima anyi abinda ya kamata kun sai dai Malama sakina Abdullahi akwai ilimi sosai ta san yanda zata koyar da abu cikin ilmantar wa nishaɗan tarwa sai kusan karfe 11:00am aka gama.

Daga nan kuma aka fara shirin kai amare gidan su.

Umma duk tayi baƙi ta fita haiyacin ta kamar ba ita ba tana shan wahala sosai babban tashin hankalin ta shi wainda saboda su ta jefa kanta cikin wannan halin suna can suna farin ciki ita kuma Tata rayuwar ta wulaƙan ta dama idan duniya zata koya maka ilimi ba a kiran ka zata yi ta faɗa maka ba a aika ce za ta aika ta maka ka gani Allah ka raba mu da kishi kalar wannan ya Allah ka raba mu da kishin da zai kaimu ga hallaka.

Can gidan su Umma kam yan dai hankalin su ya kwanta kamar ba gidan ba yanzu matan gidan sun haɗe kan su gwanin ban sha'awa sun zama abin koye ga kowa ga shi Mansur ya sai masu babban gida a cikin gari za su koma yau ne Baban su Ya ke faɗa masu bikin Amira basu ji daɗi sun so ace sun sani amma duk da haka Mansur da Baba za su je suyi masu murna yau a jirgi za su tafi.

Malam Sa'idu bincike ya sa aka yi ma shi akan Alhaji Tukur kuma ya samu saka makonme kyau dan kowa shedar kirki ya ke ba shi sosai Malam Sa'idu ya ji daɗin haka ya kira Alhaji Takura ya ce "ya ba shi dama ya turo da magabatan shi."

Sosai Alhaji Tukur ya ji daɗi ko da ya faɗa ma yaran shi suna ta murna za'a kawo masu sabuwar Mama har manyan ma sun ji daɗi dan abin na damun su ace mahaifin su bashi da mata.

Mansur ƙarfe 01:30pm
Jirgin su ya sauka a Abuja dama sun kira Abbi sun faɗa mashi suna zuwa suka iske mota ta zo daukar su suka shiga kai tsaye sai gidan Abbi tunda suka du shi unguwar suke mamaki dan su a sanin su ba shida kuɗin da zai zauna a kalar wninan unguwan sai da suka ga gidan Abbi su ƙara shiga mamaki sun samu tarba ta mamaki sosai Abbi ya karramasu bayan sun gaisa suka yi mashi jajen abinda ya faru suka ba shi haƙuri akan suma basa a haiyacin su duk abinda ya faru Abbi ya ji labari dan haka bai damuba sauka shiga firar su anan ne Abbi ke basu labari kasuwan cin shi sun yi mashi alasa alkairi daga nan yaya Faruk ya shigo suna gaisawa Mansur ya bishi suna tafiya suna fira dama sun san junna sun yi makaranta ɗaya daganan suka haɗe da su Eshan akai ta fira.

Karfe huɗu nayi suka tafi aka fara shirin zuwa daukar amare.

Dare yayi Abbi ya ce "su Mansur su kwana su bari gobe sai su wuce."

Hafsat da Amira sun yi kyua cikin lufayar su aka kama su za a kaisu falon Abbi za'a yi masu faɗa tunda daman motoci sun zo suna jira.

Sosai suke kuka ana masu faɗa da aka zo fita da su suka riƙe Ammi suna itama Ammi kuka take kamar irin idan suka rabun nan baza su ƙara haɗuwa ba da kyar aka raba su da junna aka sa kowar ce a Mota.

Eshan da Ahmad da Abdul unguwar su ɗaya amma tsakanin su da Haidar ba bu wani Ni sa mai yawa.

Kai tsaye aka wuce da su gidan su Farha wajan Mame sosai mame taji daɗin ganin an kawo su ta rungume su tayi masu nasiha sosai san nan aka ce sai an kai Farha ta gaida su Ammi haka suka taho suka ƙara dawo wa amma koda suka dawo su Amira basu shiga ba Farha ce kawai aka shiga da ita ta je ta gaida su.
Chapter 30 · 0% Book details