← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 32

Sashe 24

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Yau su Eshan kwanan su uku kuma a yau zasu koma Abuja harda su Ammi dasu Yaya Faruk.

Koda abbi ya ji labarin abinda ya faru da Umma ya tausaya mata sosai sukuma yaran Umma koda aka kawo su ganin su Amira yasa suka basu hakuri akan duk abinda suke masu Umma ce ke sasu.

Ammi kuma ta ce zata riƙe su amana kamar ita ce ta haife su sosai hakan ya faran ta ran abbi.

Bayan sun isa Abuja wani ƙaton gidan Ammi taga ankai su tunda suka shiga gidan take ta mamaki ina Abbi ya sa wannan ƙaton gidan.

Bayan sun shiga gidan ya haɗu ga wasu manyan motoci kusan guda biyar kowa Abbi yake kallo da mamaki ganin suna kallon shi yasa ya ce su shiga ciki sai ya yi masu baya ni.

Suna shiga suka ga an jera masu manyan kolili na abinci ga katan katan na ruwa da lemuka ciki da mamaki Amira ta buɗe baki zatayi magana.

Abbi yace " kibari kici ki ƙoshi sai kuyi min tambayan."

Babu yanda suka iya haka suka haƙura.

Bayan sun gama cin abinci Kowa yayi wanka suka hutu dama su Eshan nan.

Falo suka fito suka zauna Abbi ya ce "nasan bakin ku da tambayoyi yanzu zan ba ma kowa amsar shi amma kafin nan bari na fara magana ta."

Abbi ya ce shekara biyar da suka wuce wani abokina me sai da motaci babbane kusa duk motocin da dasu shigo Najeria na shine wata rana yazo ya samin da shawara ya ce me zai hana na saka hannun jari mu haɗa hannu a kasuwan cin mu da naji tsoron kada ya ci amanata amma hakanan na yardda da farko na fara sa miliyan 10 gonaki na na sai da na bada wannan kuɗin sai gashi Allah ya sa mana albarka har ta kaiga nima na mallaki Company na na kai na amma babu wanda yasan nawa ne kowa ya bushi da kallo yace yan zu haka inda Company's guda uku akwai

Al hussin Company
Al Barka Company
Amira and Amir company.

Kowa ya bishi da kallon mamaki mutumin da keda wannan dukiya ya zauna a wata unguwa.

Abbi ya ce "wannan gidan da kuke gani ina da kamar su guda goma banda gonaki na da na maida yanzu wannan gidan ya dauko keys din gidan ya bama Ammi wannan gidan na mallaka maka shi halak malak a cikin moto cin can ki dauka guda ɗaya Faruk ɗaya Muhammad ɗaya Sadik ɗaya Fatima ɗaya ɗaya kuma a bar ma yara ɗayar kuma hidimar gida.

Saboda murna su rasa me zasu yi.

Daga nan su Eshan suka tafi gida anan Hafsat zata zauna.

Washa gari

Aka kawo kayan Sa ranar su Amira inda aka saka sati biyu.

Yau ne mahaifiyar Ahmed zata zo zasu dawo Abuja baki ɗaya.

Ahmed da Eshan sun koma bakin aiki inda aka basu masu kula da lafiyar su dan ana shirin ƙara masu girma.

Amaryar Daddyn Yusurah kam suna ta kula da cikin su sai hamdala Yusurah ta ma fi kowa son cikin tunda bata da ɗan uwa ita ƙadai ce.

Yau aka yi sati da rasuwar Ladidi yau an tashi zaman gaisuwa Amarya duk sai taji gidan wa Ni kala babu daɗi tana tunanin rayuwar da suka yi da Ladidi ta na nema ma ta gafarar Allah.

Maman Ahmad ta iso harda Ammi aka je dauko ta suna isa aripot jirgin su ya iso suna tsaye har aka fara fitowa Ammi na hango Mamen Ahmad da gudu ta tafi wajan ta itama ta taho da gudu tana sakin kayan hannun ta suka rungume juna suka saki kuka me cin rai amma kuma du sun burgi wasu sai da suka gama yan koke koken su suka tafi gidan Ammi

DAFIN ZUCIYA
THE HIDDEN OG THE TREASUER OF THE HEART

BY FATIMA BINTU HOSSEN

https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t

https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

Happy jumma 'atu Mubarak

Fri,agu2025
08:17
Hiameera43

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 55

Bayan sun isa gidan Ammi sai da tayi wanka ta huta san nan suka zauna cin abinci nan aka shiga firan yanda biki zai kaya shiri ne ake na musan man bikin da ba'a taɓa kalar sa ba.

Eshan ganin tunda suka zo bai ga Amira ba kuma bada ita akaje aripot ba ya sa ya cema Amir "ina Amira ta ke?"

Amir ya ce "sun je gidan wata yar uwar mu ita da su Aunty Fatima za'a yi masu gyran jiki."

Eshan ya ce "kasan gidan?"

Amir ya ce "eh amma ko mun je baza 'a bari mugan suba wai dokar ce."

Eshan ya ce "ai kam zan karya dokar tashi mu tafi."

Ahmed kam tunda yaga Mamen shi ko kallo Eshan bai ishe shi ba yana kananaɗe da Mamen shi yan zuma yana kwance ya dau ra kansa a cinyar ta ita kuma tana sha fa mashi sumar kanshi ya lumshe ido.

Eshan ne ya zo ya finciko shi ya ɗaka mai duka ya na cewa "ƙaton banza kazo ka haye ta a haka za'a yi maka aure amma har yan zu baka girma ba."

Hararar shi Ahmad ya yi ya ce "wai na cikin masai ke ce ma na waje ya taka kashi yo kai akwai ma Wanda ya kai ka taɓara."

Murmushi Eshan yayi ya ce "ai ni yanzu nayi hankali tunda na kusa ajiyi iyali."

Mame ce ta shi ga taɓa hannu ta dauƙi wani kofi ta jifi Eshan da shi tana cewa "wai kai dan uban ka baka da kunya? ko ina ka koyo wannan rashin kunya a gaban surukar ka ka saki baki kama ta kwaso zance."

Kunnuwan shi ya kama ya na cewa "Please Mamen mu dan Allah kiyi haƙuri na dai na."

Ammi dake kallon su tana murmushi ta ce "ai Ni na saba da wannan taɓargazar ta shi tun ina jin kunya yan zu na daina."

Dariya Mame tayi ta ce "kin san halin yan fari."

Abdul ne ya yi sallama ya shi go suka amsa kai tsaye wajan su Ammi yaje suka gaisa san nan ya kalle Eshan ya ce "Malam lafiya ka kirani?"

Marai raice fuska Eshan yayi yana cewa "unguwa zaku raka ni."

Ahmed ya ce " to ba'a zuwa."

Eshan ya ce "kada kaje idan baka je ba kai kayi ma kanka."

Abdul ya ce "to ba sai ka faɗa ma mutane inda za'a je ba."

"Wajan su Amira zamu je muje yanda za'a gudanar da shirin biki muji idan da abinda suke buƙata."

Mame ta ce "sai da ku kira su a waya dan ko kunje baza ku gan su ba na faɗa maku."

Amira saboda gyaran jikin su me gyran jiki aka dauko daga Nijar gyara ake masu bana wasa ba ko fita waje basa yi komai sai dai ayi masu a ɗaki idan ka gansu za ka yi tunanin an chanza su ne su ukun da yake harda Farha Aunty Fatima ce taje har gidan su ta ruƙi Mami akan za'a haɗa dasu Amira ayi masu gyran jiki baki ɗaya.

Yaran Umma koda aka faɗa masu halin da mahaifiyar su take ciki sunbyi kuka Sosai da daga baya basu saki jikin su da Ammi ba suna tunani zata yi masu abinda Umma tayi masu Amira amma sai suka ga ba haka ba domin Ammi kula take da su sosai da sosai hankan ne ya sa suka son ta suka dauke ta kamar itace ta haifisu,

Wannan abu da Ammi tayi baƙara min ƙaramin daɗi yayi ma Abbi ba hakan yasa yake jin kome Ammi ta ke so indai bai fi ƙarfin shiba zayayi mata.

Bayan sati ɗaya

Mariya ɗiyar Ladidi ce kwance a wani asibiti an kawo to ashe bayan rasuwar Mahaifiyar ta wani Alhaji ne ta bi ƙasar waje wai zata rakashi holiday Babu wanda ya sa ni ta bi shi suka tafi ashi babu wata ƙasar waje da zasu ji suna shiga mota za su je aripot ya hura mata wani abu nan da nan ta fara barci ganin tayi bacci ya kai ta wani gida ya mayar da ita matar shi ta karfi da yaji sai da ya gama lalata mata rayuwa gashi ya shafa mata cutar ƙarya garkuwar jikin ɗan adam HIV,

Ganin bata cikin haiyacin ta yasa wani daga cikin yaran shi ya kawo ta asibiti ya bada kuɗi masu yawa a yi mata komai shi kuma ya gudu.

Yanzu ta farka ganin ta a wani ɓakon waje inda bata san ko ina ne ba ita tunanin ta ma ko mutuwa tayi ne ma tana cikin wannan tunanin wata likita ta shigo ta kalle ta ta ce "sannu ya jikin."

Ta ce "da sauƙi."

Likitar ta ce "ina ke maki ciwo?"

Ta ce "kaina ne kawai."

Likitar ta ce "to alhamdulilahi yan zu ina family na ki?.

Kuka ta fashe da shi tana cewa "suna nan amma ina tsoron koma wa wajan su nasan idan naje Baba yaji abin da ya faru kashi ne zai yi."

Likitar ta ce "subuhanal me yayi zafi haka?"

Mariya ta ce "inda kin san abinda na aiki ta ke kan ki baza ki kulani ba yanzu."

Likitar ta ce "kin man ta karin maganar da ake ce wa "ciwon ƴa mace na ƴa mace ne ki faɗamin in Sha Allah nayi maki alƙawarin zan sa san taki da iyayen ki."

Kuka ta fashi da shi.

Eshan duk yan da ya so yaga Amira abin ya gagara har ce ma me gyran yayi ta bari ya gan ta zai bata kuɗi masu yawa amma fafar matar nan ta hana haka ya gaji ya yi hakuri sai dai suyi video Call.

Mame ce ta shirya zata je giɗan wata yar uwar ta da za ta aurar da ɗiya rana ɗaya dana su Ahmed shene zata je tayi mata Allah sa alkairi ta dau wankan ta tayi kyau baza kace ita ce ta haifi Ahmad ba.
Chapter 24 · 0% Book details