← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 32

Sashe 19

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Ba mame ba har Ahmad sai da ya kalle shi da mamaki dan shi bai san da wata maganan taransupar ba hassali ma idan yayi mashi maganan su ne ma sai ya ce a'a nan yafi besan dalilin da yasa ya chanza shawara ba.

Washi gari

Babu wanda ya san da Farha za'a yi tafiyar ba sai da suka ganta da akwatin ta hakan ya sa kowa ya kalle ta da mamaki.

Eshan ya ce "Malama ina zaki?"

Kallon shi tayi san nan ta ce "ai ƙafa ta ƙafan Yaya Abdul."

Dariya Abdul ya yi ya ce "yawa beby na dama kamar kin san zan yi kewarki."

Eshan ya maka mai harara san nan ya ce " ita kuma Mame a barta dawa?"

Daga bayan su suka je Mame na cewa "babu komai ku yi tafiyar ku ban damu ba nima sai mu sha ƙauna da mijina."

kunyar duniya ta kama su babu wanda ya iya wata magana duk suka shiga mota suka yi mata sallama daman sun riga sun yi da Abba hakan ta sa suna fita kai tsaye kai tsaye suka wace gidan Abbi.

San da suka isa kowa ya shirya babu wani bata lokaci suka firfito da kayan su.

Inda Amira da Farha da Hafsat suka shiga motan Eshan Amira ce a gaba sai su Hafsat a baya idan Abbi da Abdul suka shiga motan Ahmad da Amir suka kama hanyar Katsina ta dukko ɗakin ƙara kunya gare mu ba tsaoro ba

TO SU ESHAN SAI DA MUCE ALLAH YA KAIKU LAFIYA

DAFIN ZUCIYA

BY FATIMA BINTU HUSSEN

https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajir

ILIMIN HASKE NE SANAN KUMA JAHILICI DAHU NE TUNANI ME KYAU BAIWA NE RASHIN TUNANI KUMA CIWO NE KYUTATAWA A KULLUM ARZIKI NE ITA KUWA ROWA MUSIBA CE ZAMAN LAFIYA A KULLUM WALWALA NE SHE KO RASHIN ZAMAN LAFIYA KUN CI NE ITAFA IBADA GUZURI CE RASHIN YIN IBADAR KUWA AZABA NE

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 47

Amira tunda suka fita Abuja gabanta ke faɗuwa ta rasa dalili she kanshi Eshan ya lura da haka.

Hafsat ce ma suke ta fira da Farha.

Can motar su Ahmad ma fira suke Abbi Ya na ta yi masu addu'a suna ta fira.

Abdul ne ya ce ma Abbi "Dan Allah Abbi ko zamu iya sanin wani abu game da Hafsat?"

Ahmad jin tambayan da Abdul ya yi ma Abbi ya sa yayi ƙasa da kan shi yana jin kunya.

Abbi ya ce "gaskiya abinda zan faɗa maku shine bata da wata matsala san nan ta na tarbiya da hankali. kuma mahaifinta mutumin kirki ne."

Sosai Ahmad ya ji daɗin jin yanda ake ta yabon Hafsat.

Abdul ne ya ce "ma sha Allah gaskiya mun ji daɗi yanda ka ke ya ba wa da tarbiyan ta."

Abdul ne ya ce "daman Ahmad ne ya ganta kuma ya na son ta."

Sosai Abbi ya yi murana dan ya tabbata Shema Ahmad mutumin kirki ne

FUNTUWA

Ammi ce a kicin ta dafa wannan ta dafa wance murna ta ishe ta gani take komai kamar a mafarki wai yau ita ce zata ga Amira da Amir bugu da ƙari kuma harda wasu ƙarin mutane da suka samu..

Umma bayan an kaisu gidan gyran hali an kulle su sai suka yi sa'a aka haɗa su ɗaki ɗaya.

Suna zaune Umma ta kalle Mama ta ce "gaskiya ni na yi dana sanin biye maki. Kuma idan aka zo zama na gaba zan faɗi gaskiyar komai duk abinda za'a min sai dai ayi min kuma da na fita daga nan kai tsaye zan kuma gidan mijina na gyara zaman mu mu rungume yaran mu."

Mama ce ta kalle ta ta ce "hummm Ummul kairi nima kai na nayi dana sani."

Yusurah yau aka kawo kuɗin auren ta da Haidar sosai tayi murnar daga ka ganta kasan tana cikin farin ciki da wal wala.

Mommy jikin ta ya yi sauƙi sai da muce Alhamdulilah dan an basu sallama sun dawo gida.

Ladidi ce zaune gaban Yayan ta ta na kuka bayan Malam Sa'idu ya gama mashi bayanin abinda ta ai kata sosai ya yi baƙin ciki yaji inama ace Ladidi ba yar uwar shi ba ce ina ma ace baizo duniyar nan ba ya rasa me zai yi kawai sai ya fashi da kuka.

JAN HANKALI YAKE YAR UWATA YA KAI ƊAN UWANA MEYE AMFANIN WANNAN RAYUWRAR KAZO KANA ABIN DA ALLAH YA HARAM TA AMMA MUN DAUKE SHI SHENE ABIN YI A WAJAN MU ABIN DA ALLAH YA UMARCE MU DA MUYI MUN WATSAR BAMU TSORON MU BAR MA YARAN MU

Yayan Ladidi ya ma rasa me zai yi kawai sai ya kamata da dukan ta yake ya na surutai alman ya fita daga haiyacin shi.

Malam Sa'idu ganin duka banayi bane ya kama shi ya na shafa bayan shi cikin lalashin ya ce "duka ba shi bane in har dai muna so muji wanda ya yi mata ciki to sai dai mu bita a hankali."

Yaya jin maganan Malam Sa'idu sai jikin shi ya yi sanyi.

Eshan ganin shurun Amira ba me ƙare wa bane ya sa ya ce "me yake damun ki?"

"Babu komai."

Ta bashi amsa.

Farha ce ta ce "sister ya da wannan rayuwar kin yi mana shuru kamar ruwa ya cinye ke kodai Ya Eshan ne yai miki wani abin?"

Murmushi ta yi ta ce "ba bu komai ina tunanin wani hali zanga Ammi."

Farha ta ce "in Sha Allah lafiya lau za mu ga Ammi karki sa ma kan ki damuwa."

Daga haka suka ci ga ba da fira.

Ammi ta na can gida ya cika da mutane kowa ya na taya ta murnar dawo War yaran ta.

Zamfara

Gidan su Umma duk wanda ka kalle fuskan shi zaka fahimci ya na da damuwa shi kan shi Mansur ya shiga damuwa.

Abbi kam ya ma manta da wata Umma can dan yasan idan ta gaji zata dawo da kanta.

Haidar ne zaune a gaban Mama suna fira akan kuɗi aikin da aka kai na yusurah.

Mama ta ce "gaskiya wainan mutane suna da kirki duba kaga kalar tarbar da aka yi ma yan uwanka."

Murmushi ya yi ya ce "nima nayi mamaki Mama."

Hafsat kam chat suke da Ahmad ya ce mata "ko zata dawo motar su yana so ya ganta?"

Hafsat ta ce "so kake ace bani da kunya ko?"

Eshan ganin motar Abdul ta wuce ta su ya sa ya fisgi motar shima da mugun gudu dan ya san da biyu Abdul ya yi haka.

Abbi ganin Eshan ya wuce su da mugun gudu ya sa ya tambaya "lafiya kam naga Muhammad yana wannan gudun?"

Ahmad ne ya ce "ai shi wani lokacin haka yake gudu sosai."

Abbi ya ce "Allah ya kyuta ni kam sai nayi mashi faɗa ya dai na wannan gudun."

Ladidi cikin daka tsawa Yaya ya ce "ina tambayan ki waya yi maki ciki?"

Ladidi ta ce "abin da zan faɗa maku kan ku bazai iya dauka ba shi yasa bazan iya faɗa maku ba."

Yaya ya na mamakin taurin kai kalar nata dama har yanzu tana da wannan kafiyan.

WELCOME TO FUNTUWA

Amira ganin wannan sanbol ya ƙara sata cikin faɗuwar gaba har sai da ta ambaci sunan Allah.

Amir kam murna yake har da cewa i miss You wallahi nayi kewar garin nan.

Eshan waya ya kira Abdul ya ce "yazo yayi gaba tunda suna tare da Abbi kuma shi ya san gidan."

Abdul ya shiga gaban Eshan Abbi na nuna masu hanyan.

Sanda suka isa kofar gidan ya yi daidai da isowar Yaya Muhammad daga makaranta ya samu hutu ya dawo.

Amira na cikin mota ta hango shi zai shiga gida ta kwala mai kira.

A ɗari uku da sitin ya juyu dan bazai taɓa manta Muryar yar uwarshi ba kuma abin son shi abokiyar faɗan shi.

Sororo yabi motan ta kallo har san da suka gama paking Amira ce ta fita da gudu tayi wajan shi shi kuma Yaya Muhammad ganin gaske ita ce ya sa yayi watsi da kayan shi ya taho yayi kan ta shima.

Amir kama ya na fita ko kallon Su Yaya Muhammad be yi ba ya ruga da gudu yayi cikin gidan yana kiran "Ammi" Ammi ina kika shiga gani?

Ammi na ɗaki jin Muryar Amir ta fito da gudu tayo kan shi kafin ta ƙara sa taja ta tsaya tana kallon Amir ganin kamar bashi ba ya rame ya fita haniya cin shi a hakan ma wai sun samu sauƙin rayuwa.

Amir ne ya ce "Ammi baki murna da ganin mu ko?"

Jin tambayan da yayi mata ya sa ta ƙara sa wajan shi dan dan da ta tsaya shima sai ya tsaya ƙara.

Da gudu Ammi ta ƙara sa ta rungume shi tana sakin kuka me cin rai.

Amira ganin mutane sun zagaye su anata kallon su yasa ta kama hannun Yaya Muhammad suka shiga ciki ganin Ammi da Amir rungume suna kuka itama ta ƙara sa ta rungume su tana kuka.

Eshan ya na can ya kumbura ganin wani ya rungume Amira ya na ta huce.

Yaya Muhammad ganin Ammi ta ma manta da baƙin da ke waje ya ce ma Ammi "bari nace ma wainda suke tare su shigo."

Abbi tunda suka iso hankali shi ya tashi ya ma kasa fita daga motan Addu'a kawai yake Allah ya kawo mai sauki akan tambayoyin da Ammi za tayi mashi

DAFIN ZUCIYA

By Fatima Binta Hussain

MRS NASIR

https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

Alhamdulilah Allah na gode maka da ka bani ikon cigaba da rubuta wanan littafin ya Allah ka bani ikon gamawa lafiya ina me miƙa godiya ga wainda ku ka ƙarfafa sani gaba akan na ida wanan litattafin na gode sosai Allah ya saka da alheri

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 48

Abbi tunda suka iso hankalin shi ya tashi yama kasa fita daga motan Addu'a kawai yake Allah ya kawo mai mafita dan ya san zai sha tambaya wajan Ammi.
Chapter 19 · 0% Book details