← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 32

Sashe 28

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

> Eshan tunda ya kama hannun Amira sai filin rawa shi ala dole sai ta yi rawa ganin wannan abu da Eshan keyi ya sa idon kowa ya dawo kan su yana zuwa ya ce a canza masu waƙa asaka masu waƙar amarya ta Ali jita aka sakar masu kiɗi ya kama hannun Amira dole sai tayi rawa ita kuma kunya take ji dan bazata iya ba ana cikin haka sai ga Mame ta zo zataje ta taho da baƙi ganin Eshan filin rawa ya dage rawa yake amma kamar wani wanda yake bada huru wa sojoji da gudu Mame ta ƙara sa ta yi mashi dun du tana ce wa "me yasa baka ne moni ba?"

Eshan ya ce "sorry Mame na wallahi hankalina yana nan shiya sa."

Fita tayi daga filin taji ta sako Ahmad da Abdul da Haidar suka shiga filin rawa aka sakar masu kiɗa mazan dai kam sai rawa suke sai Mame ga nin yanda suke rawar sukuma sauraran mutanan wajan suka fasa ihu wanda wasa sauran mutane cikin gida suka fito suga me ke faruwa.

Ai ganin abin da ke faruwa waje ya ƙara ruɗewa nan fa gida ya koma gidan rawa da gudu Mame taje ta kamo Ammi Ammi na ɗaƙi tare da ƴan uwan ta kawai sai gani su ka yi an kamata anyi waje da ita hankali a tashi duk suka fito ganin filin gidan ya ce ga anguna ana ta rawa kai tsaye Mame ta wuce da Ammi filin rawa Ammi na figi hannun ta amma sai da suka kai ta haka ta tsaya cikin fili bata komai nan aka shiga hutuna da videos kamar ba gobe Abbi da yayan baban Hafsah ne suka shigo ganin abin da ake yi suka koma waje suna dariya sai ko shiga gidan ta ƙofar baya.

> Haka dai akai ta shiriri ta daga baya kuma aka fara shirin tafiya dennah War da za'a yi ƙarfe 08:00pm dan su fara shirya wa haka dai ake ta taro cikin farin ciki da kwanciyar hankali

Mariya tana zaune a tsakar gida wani yaro ya zo ya ce "an ce Mariya ta zo."

Mariya ta ce " kage ka ce banan."

Amarya ce ta fito ta ce "jika ce tana zuwa."

Mariya ta kalle ta ta kwaɓe fuska ta ce "Ni Wallahi Mama da kin barni."

Da yake yanzu mama suke ce mata.

Ta ce ta tashi taje haka ta tashi badan ranta ya so ba ta saka hijabi ta fita.

Wani ne ya fito daga mota zasu kama kusan ɗaya da Malam Sa'idu yana mata murmushi ya ce "nasan za ki yi mamakin ganin na ko?"

Mariya ta ce "bawon Allah me ke tafe da kai?"

Ya ce "sunan Alh Tukur Ni babban ɗan kasuwa ne kuma da aure nike don ki idan kin amince bana so a dauƙe dogon lokaci."

Mariya ta ce "gaskiya Ni bazan yi aure ba Ni naga ma aure."

Dariya yayi ya ce "kar ki ce wallahi ba da wani abu nazo gare ki ba zan je gidan abokina ranar na ganki kin fi zaki je wani shago ko da na tambaye abokina Ya bani labarin halin da kika shiga kuma wallahi ina son ki ina da yara biyar mahaifiyar su ta rasu so ban ƙara aure ba sai yanzu idan kin amince."

Shuru Mariya tayi kafin ta ce "shi kenan zanyi shawara."

Ya bata wani kati ya ce "idan kinyi shawarar ga kati na nan ki kira Ni ki faɗa min."

Ta ce "to."

Ya dauko kuɗi ya bata taƙi amsa yayi yayi ta amsa taƙi hakan ya sa yaji yaƙara son ta a zuciya daga nan suka yi sallama ta koma gida tana zuwa ta faɗa ma Mama abinda ya wakana tsakanin ta da Alhaji Tukur.

Mama ta ce "ke ya kika gani kina son sa?"

Mariya ta ce "gaskiya ban yanke shawara ba ni da nace bazan ƙara aure ba."

Dariya Mama tayi

DAFIN ZUCIYA

THE HIDDEN OF THE TREASURE OF THE HEART

By hiameera43

https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunsuanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

Thursday, September 4 2025

08:56am

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 57

Dariya Mama tayi ta ce "haba ya zaki ce baza ki ƙara aure ba ai aure shine mutumcin ƴa Mace."

Numfasawa Mariya ta yi ta ce "Tom Mama Allah ya zaɓa min abin da yafi alƙairi."

Mama ta amsa da "amin."

Karfe 08:00pm aka zo da manyan motoci aka fara daukar masu get pass dan komai a kan tsari su kayi shi sai da aka tabbatar da kowa ya gama shiga moto suka fara yin gaba kafin motar anguna ta ƙara sa mota ce sabowa dal da ita baƙa ce motar baka ganin komai na cikin ta Eshan ya fito daga ciki ya sa baƙar sut da sai rigar ciki fara ga wani glass da ya sa gaskiya ya haɗu sosai.

Kai tsaye cikin gidan su Amira ya shiga yana zuwa ya hango zu bakin get ita da wasu da basu kai ga tafiya itama Amira baƙar doguwar riga ce a jikin ta fetat sai mayafe me raga raga fari suma yan matan amarya suka sa siket tome sai t shat fara gaskiya shigar tayi masu kyau sosai yana zuwa ya kama mata hannuta suka ci ga ba da tafiya suna zuwa wajan moto wani soja ya buɗe mashi sai da ya fara saka Amira ciki san nan ya shiga yana shiga ya dan na wani madani sai ga wani labile ya sauko motar ta koma kamar wani ɗan ƙara min falo.

Ahmed ma tunda ya ga Eshan ya shiga ya fito da Amira shima sai ya shiga ya fito da Hafsat suka shiga motar su shekuma a can zasu haɗe a bakin holl din da aka kama.

Eshan bayan ya saki labile Amira ya jawo jikin shi ya rungume ta wata ajiyar zuciya ya sake har sai da ta ɗago da kai tana kallon shi sai kawai taga hawaye a fuskar shi cikin tashin hankali ta ke ceashi.

"Yau ba ranar baƙin ciki ba ce farin ciki ya kamata kayi dan Allah ka bar wannan kukan nima zan yi."

Dariya yayi ya ce "kukan farin ciki niki yau buri na ya ciki na mallake ki ya Allah ka bani ikon sauke nauyin da ya hau kaina yana addu'a yana hawaye."

Ita Amira kuka ta fara yi ya jawo ta yana lallashi ya ce "ki Ni ba kuka na ce ki yi ba Ni farin ciki ne yayi min yawa."

Ita ma Amira ta ce " ina ga nawa farin cikin ya fi naka."

Ya ce "Allah ko taya zan gane da gaske kike?"

Ya faɗa yana haɗe bakin su waje ɗaya.

Wani irin bugu kirjin Amira ya yi jin ta a wani yana yi da ba ta taɓa shiga jikin ta na rawa ta shiga ƙoƙarin kwatar kanta amma ina ya ƙi bata dama baki ɗaya.

Sai da ya shanye janbakin ta duka san nan ya ɗago ya na kallon ta ganin yan da tayi zuru zuru kamar beran da ya faɗa ruwa haka ta koma.

Dariya yayi ya ce "me kika yi wani kamar baki lafiya babu abinda ya faru fa haka zamu yi dake?"

Jin tambayar da yayi mata taji kamar ta ɓace dan kunya ta lura angon nata kwata kwata babu kunya a tare da shi.

Hafsat suna shiga moto Ahmad ya kamo ya rungume a barshi shima Hafsat tun da taji ya rungume ta jikin ta yayi san yi sosai cewa ta ke "dan Allah ka cikani kaina ke ciwo."

Dariya yayi dan ya gane lagon ta ya ce "zan sake ki amma sai kin min kiss."

Idanu ta gwalalo ta ce "Please kayi haƙuri bazan iya ba."

Ya ce "tunda ba za kiyi ba Ni kuma bari nayi."

Kafin tayi wani motsi ya haɗe bakin su waje ɗaya Hafsah harda kukan ta ganin abin nashi ba na ƙare wa bane dan ta gama kamar baya a cikin haiyacin sa.

Abdul shima amaryar Farha suna cikin moto ya kamo ta ya rungume ya na ce wa "alhamdulilahi yau na zama angon Farha ta."

Farha da babu kunya ta biyo halin Yayan ta ta ce " nima alhamdulilahi da na zama matar Yaya Abdul."

Ai kafin ta ƙara magana ya jawo ta wai tazo ta kwanta a cinyarsa ita kam bata san wayo ya yi mata ba tana kwanciya ya juya da ita ya kwantar da ita akan set ɗin motar ha sauko daga kasa yana kallon ta ita kam gani haka yasa ta sa hannu ta refe fuskar ta hannun ta tana turu baki ai kam kamar ta zuga shi ya kama bakin kamar wa samu wani sweet yana sha yana ƙoƙarin tura hannun shi cikin rigar ta yaji motar ta tsaya alamar an iso inda zasu je.

Yusurah bayan an sata a mota ita haka suka taho tana jikin shi yana ta shafa ta itama sai da ya shanye mata janbakin bakin ta.

Sona iso wa dama angama yan da komai zai tafi a tsare masu anko maza da mata sune suka zo suka sa layi za'a sa amare a tsak iya.

Eshan da kyar ya samu ya dai dai ta natsuwar shi dan yana gama fita haiyacin shi Amira ji take baza ta iya fita ko ina ba tana gani kamar kowa zaiga abinda ya faru.

Su Ahmed ne farko fitowa amma da ka gansu zaka gane da abinda ya faru saboda yanda suka yana yin su ya chanza.

Suna fitowo aka fara daukar su photona ana masu videos Dan sun dace da juna sosai da Sosai bama kamar da Ahmad ya saƙalo hannun shi ta ƙugun Hafsat suna fitowa aka buɗe masu suka shiga daga tsakiya.

San nan sai Haidar da Yusurah suma sun dace Sosai suna zuwa suka tsaya bayan su Hafsat.

Daga su Haidar sai su Abdul shima suka fito suka tsaya bayan su Haidar.

Ana ta jiran su Eshan su fito aka ji shuru sau da aka je aka bubuga glass din motar.
Chapter 28 · 0% Book details