← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 32

Sashe 10

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Ladidi yau an kwance ƙafa amma ance ta fara tafiya da sanda

Amma dan bala'i ganin babu kowa agidan Mijin su ya fita aiki ita kuma Amarya taje kunshi.

Haka yasa Ladidi ta kama hanyar gidan boka tana cikin tafiya tayi nisa cikin tunani har batasan tana Tsakiyar titi ba

Sai ji ta yi anyi sama da ita

Abbi tunda suka yi waya da Ammi sai hankalinsa ya ƙara tashi shi da kanshi yasan be ma Ammi adalci ba.

Abdul yana cikin damuwa dawowar Eshan dan harga Allah shi baya son yazo yaga halin da amira take ciki amma bai da yanda zaiyi.

Yana cikin tunanin sai ga kiran Eshan bayan ya ɗaga suka gaisa Eshan yake mai bayani game da aikin da ya hanashi dawowa.

Ladidi wani me adaidai ta sahu ne ya bigita kuma shi bada sani yayi ba yanata mata hon amma bata jiba.

Kuma birkin shi yaki yai aiki ganin ya bige wata mata yasa shi fitowa cikin tashin hankali.

Yace "ta hau ya kaita inda zata."

tace "takusa zuwa ya barshi."

Ladidi har ga Allah tana jin zafi Bama kamar ƙafarta da aka gyara amma baza ta iya fasa zuwa wajan boka ba

Amira tana cikin kuka Abdul ya shigo tana ganin shi ta kama kanta sai tayi kamar zata tuna wani abun sai ta ka sa.

Likitan da yake kula da ita ganin haka yace "idan tana wannan abun insha Allah zata iya dawo wa dai-dai a kowani lokaci."

Abbi bai san abinda yake faruwa ba dan yaji ya duba Umma da yaran ta ta tafi ko ta barsu.

Yana zuwa gidan yaga a kulle amma da alamar mutum a ciki gidan hakan yasa bugawa.

Ladidi tana tafiya tana hutawa har ta isa gidan boka,

Tana shiga yaita binta da wani mayen kallo,

Bayan sun gaisa yace "nasan me yake tafe dake amma ki sani wanan lokacin bani zan yi aiki da keba Aljani tugudidi ne zai yi amfani dake kuma ta baya zai ne meki."

Ladidi tayi shuru tana tunanin yanzu da Aljani zata kwanta anya zata iya kuwa.

Abin yana tsaye yaji ana cewa waye yace shine jin Muryar shi yasa yaran suka ɓude kofan ya shiga.

Abbi ya tambaye yaran ina Umma? cikin rashin tarbiya babban yace "baka koritaba kuma zakazo kana tambayan mu."

Akam Abbi ya Kama yaron da duka sai da yayi mai dukan tsiya sanan ya barshi.

Cikin ƙunar zuciya abbi ya fara magana ba zan dau rashin tarbiyar da uwar ku take koya makuba saina gyara maku zama.

Hankali Ammi fa ya kasa kwanciya ta yanke shawarar tafiya Abuja bada sanin kowa ba.

Please share and comment

BY FATIMA BINTU HUSSEIN✨✨✨

https://chat.whatsapp.com/Gvh8Kfitxaw0Qwme0hezcZ

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Page 26

Bisimilahi Rahamanur Rahimin

"Ladidi ganin tana so burin ta ya cika ya sa ta amincema Boka.

Abinda bata sa niba ba Al'jani ne zai sadu da itaba Boka ne zai sadu da ita.

Amira Kam ta ƙara zama abin tausayi dan yanzuma ko abinci bata ci saita ta fama da ita bata iya yin komai sai kuka.

Hakan ya ƙarasa Abbi da Amir cikin matsananciyar damuwa.

Umma tunda suke tafiya cikin dajin basuga kowa ba sunyi tafiya sosai kafin suka isa wata buka da ke saman wani tsauni..

Shi kuma wannan Bokan ƙa'idar shi shine a shiga da tsalan kwadi.

Suna shiga wani kalan ɗoyi ya bugi hancin su da sauri Umma ta tushi hancin ta saboda wannan warin.

Wata gigitarciyar tsawa aka daka masu ana cewa

"ku la ananu ku suwaye da zaku shigo Fadar Ƙanin Sheɗan kuna tushi hanci to ku koma inda kuka fito kun ɓatama Sarki rai."

Eshan koda suka gama waya da Abdul.

Mame ya kira ya "faɗa mata bazai samu zuwa gida sallah ba wani aiki ya riƙe shi Mame tayi mashi addu'a sosai daga nan suka yi sallama.

Ya kira Abba shima suka gaisa shima ya faɗa mashi abinda ya riƙe shi.

Yau har Farha sai da ya kira suka gaisa take tambayan shi Yaya yaushi zaka dawo yace sai bayan sallah zai dawo yana da aiki ne shiya sa.

Yana jin dadi a duk acin da yake cikin family nashi ko sukayi waya.

Abdul babu wanda yasa ni ya ba ma likitan da yake kula da amira

Ya bashi kuɗi da yawa "yace duk wani abu da za a buƙata ba sai an amshi kuɗi wanja abbi ba adinga aiki da kuɗin da ya bada idan basu isaba ayi mai magana amma yace baya son a faɗa ma kowa shi ya bada kuɗin.

Amarya ita kam tana mamakin hali kalar na kishiyarta itafa ta fara zarginta yaza a ce daga kwance ma mutum ƙafa yau ace ya fita tana cikin tunanin nan taji "Muryar Mijin su yana tambayanta ina Ladid ta tafi? tace "nima ban saniba yanzu ta dawo bata gantaba.

Malam yace "ance an ganta ta fita tayi bayan unguwar nan.

Ita dai amarya tace bata sani ba amma duk inda taje zata dawo.

Umma jin abin da aka ce yasa ta faɗin yanzu dan Allah duk tafiyar nan da muka yi sai a ce wani sarki yayi fushi ai ba ayi masu adalci ba wasu gigitatun maruka taji an sauke mata aka ci ga ba da cewa maza ku fita daga nan kada ku ƙara zuwa nan.

Suna fita Mama cikin fushi "tace ai gashinan garin iyayin ki kinja mana gashinan ai mun rasa da marmu yanzu sai dai mukoma wajan dayan bokan.

Ladidi haka ta cire kayanta ta shiga ɗakin da Boka ya nuna mata.

Har ta shiga ta tuna buka yace idan ta shiga ta kwanta kan katifa kuma ta rufe idan ta san kada taga Al'jani idan ta bari ta kanshi zata mutu.

Boka yana ganin ta shiga ya kwashi da wata dariya yana ce wa ya ƙi banza ya cire kayan shi ya shiga haka ya nemi Ladidi ta baya.

(Waiyazubillah)

Suna gama al'fashar Boka yayi sauri ya fita ya maida kayan shi ita Ladidi sai da taci kokan ta me isar ta sanan ta mayar da kayan ta ta fito,

Tana fitowa taga Boka sai wata fara'a ya ke mata yace 'yanzu kada ki sake zuwa sai nan da sati ɗaya lokacin anyi sallah.

Badan taso ba tafita dan ta so ace ayau za ayima ta aikin ta a gama ama sai wani nan da sati ɗaya.

Amira idanta buɗe tana kalon POP Amir ya shigo tana ganin shi tace kainta ya fara juyawa su Abdul dake ɗakin sunata ta kallon ta cikin tausayawa can sukaji da ƙarfi tace Amir!!!

BY FATIMA BINTU HUSSEIN✨✨✨

https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Page 27

Bisimilahi Rahamanur Rahimin

Umma haka suka kama hanyar gida akan bayan sallah sai su koma.

Umma suna cikin tafiya cikin' dajin nan ba gida gaba ba gida baya suka fara jin harbi nan hankalinsu ya tashi,

Ko ba a faɗa masu ba sun san yan bindiga ne suka shigo gari.

Umma ta kalle Mama" tace mun bani ya zamu yi.?

mama "tace ma Umma su gudu kafin su ƙaraso dajin suka sun fita dajin'

Sun kusa fita dajin aka harbi Mama a kai cikin tashin hankali "Umma take kiran ta ganin ba ta da mafita gashi suna ƙara matsowa kosa dasu yasa Umma ta dauki Mama tana ta nishi.

A haka har Allah ya bata iko ta fito bakin titi lokacin mutane sun ji harbi sun fara ɓuyewa.

Da kyar Wani mai mota ya taimaka ma Umma yasa mama cikin Mota.

jininta yana ta zuba ita Umma ta ɗankwali ta daure wajan dan jinin ya ke zuba.

a haka suka isa asibiti suna zuwa aka amshi ta amma ganin abin babba ne yasa suka ƙi amsar ta dole sai da yan sanda.

shikuma "mutumin da ya kawoso yace ba zai iya ba da taimaka masu yayi zai tafi gida kafin yan' bindiga su ƙarasa shigowa cikin gari.

nan fa hankalin mutanan asibiti ya tashi jin an ambaci yan' bindiga.

Abdul jin Amira ta kira sunan Amir yasa suka isa inda take.

Likita" tace Alhamdulilah ta fara tuna wani abun yanzu a hankali za tai ta tunawa."

Amir yace "Amira." ta ɗago ta kalle shi Likita tace "kin san shi?.

Tayi shuru kamar mai tunani can kuma ta kama hanun Amir ta zaunar da shi kusa da ita.

Likita ta ƙara tambayan ta waye shi?.

Sai tayi shiru Likita tace "kar a dameta a hankali za tai ta tunawa har ta dawo dai-dai amma yana da kyau a samo mata wani abu mai mahimmanci a rayuwarta She ma zai bada gudum muwa wajan da wo wan ta dai-dai."

Abbi cike da jin haushin kalar tarbiyar yaran Umma haka ya dafa abinci yasa masu sukaci yace sutafi su kwan ta su refe ɗakin danshi ba a nan zai ƙwana ba suna so suce baza su iya kwana su kaɗai ba suna tsoron Abbi.

Abbi Kam Bai wani damu da halin da suka shiga ba yasa ma falon kwaɗo yayi masu addu'a ya fita.

ƙafan waje ma sai da yasa mata ƙwado sanan ya kama hanyar asibiti.

Yayi mamakin ganin Abdul da suka gaisa Abbi "ya ke tambayan shi bai gane shi ba?.

Abdul "ya faɗa mashi komai tun daga zuwan su da Eshan.

Abbi yayi mamaki sosai dan bai taɓa sani ba sai yanzu yake tabbatar wa da su Amira suna cikin wani hali ace har wani zai zo wajan ta bata taɓa bashi labari ba.

Gaskiya yayi sake da har yaranshi suka shiga wannan halin wasu abubuwan ma bai san suna faruwa ba kuma yasan a matsayin shi na mahaifinsu shi Yaka ma ta ya basu kulawa tunda mahaifiyarsu bata kusa.

Yasa inda suna tare da mahaifiyar su ko ƴan uwansu komai ya faru zasu faɗa ma wani da ga cikin su.

Abbi yace "Ma sha Allah to ina shi Eshan din?"
Chapter 10 · 0% Book details