← Book details Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 32

Sashe 12

Dafin Zuciya Part 1 Compelete Hausa Novel · about 8 min read

Mom tana jin anga wata ta fara shirin tafiya wajan boka Nijar dan ƙawar ta da zasu je tare ta dawo jiya dan haka tare zasu tafi.

Yusurah yan zu duk wata damuwar ta ta koma kan Aliyu Haydar gashi ita yanzu zaman Gidan ya ishe ta tana so itama tayi aure.

Gashi bata da wani wanda zatace tana so duk wa inda ke zuwa wajan ta bada aure suke zuwa ba wasu suna zuwane dan su lalata mata rayuwa suke zuwa ita kuma bazata iya barin a lalata mata rayuwa ba kamar yarda yan matan yan zu suke yi suna ganin shine wayewa.

Amira ganin kallon da yake matane yasata ta tashi zata shiga ɗaki Abdul yace haba Amira ba gaisuwa.

Ta tsaya ita bata juyi ita bata ci ga ba da tafiya ba dan wani kalan ciwo kanta ke mata.

Abbi yace "Amira ba magana ake maki ba?"

Zata fara magana ke nan ta faɗi tana riƙe da kanta tana am batan Ammi kizo ki duke ni wallahi Umma zata kashi ni.

Jin abinda take cewa yasa Abbi yin hamdala harda su Eshan din.

Abbi yace "Amira addu'a zaki yi ba wannan surutan ba."

Amira tace wallahi Abbi nagaji da wahalan nan ka mai damu wajin Ammin mu da yan uwan mu zan ci ga ba da zama a nan ba.

Amir ganin halin da ta shiga yasa shi ya taso ya kamata ya ce "Yaya kin manta kece kike ce wa wannan kaddarar muce meya sa bazaki yi haƙuri mu ida cinyewa kaddarar mu ba nasan Abin da cewo mu maida komai na mu ga Allah kamar kullum yarda muka saba."

Amira ta ƙara fashiwa da kuka ta kama Amir "tana cewa ban manta ba Amir na gaji da wahalan da mu ke sha a gidan Mahaifinmu an maida mu marasa gata bamuda galihu kana ganin Abbi Bai damu damu ba sai mu kwana mu wuni bamu ciba amma Abbi Bai taɓa tambayan mu ba? Tacigaba dacewa kana tunanin inda Ammi nan zamu shiga wannan halin.?

Amir yace "a'a ki yi haƙuri in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshi.'

Allah sarki idon shi yayi jajur kamar zasu yi aman wuta shima Abdul hakane dan shi baya da karfin zuciya abu kaɗan ke sa shi kuka wata kalar tsanar Ummace ta darsu a zukatan su.

Umma mutane sun fara cika asibiti wasu na waje wasu na cikin ɗakin Umma na zaune kan gadon kusa da Mama.

Mama ta farka ta fara tuna ma kansu asiri.

𝐃𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐙𝐔𝐂𝐈𝐘𝐀

✏️𝐵𝑌 𝐹𝐴𝑇𝐼𝑀𝐴 𝐵𝐼𝑁𝑇𝑈 𝐻𝑈𝑆𝑆𝐼𝑁✏️

https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8

https://whatsapp.com/channel/0029VbAho5W8V0tlD03a4Q1g

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

𝑃𝑎𝑔𝑒 31

✨✨✨

Abbi shima ya kasa jure halin da ya ga yaransa a ciki kawai sai yaje ya rungume su shima ya mai basu haƙuri.

Da ƙyar Amira tayi shuru, Abbi ya ce "kin gane kowa daga cikin nan."?

ta ɗaga kai "tace amma ita ya kai ta wajin Ammi."

"yace to in sha Allah bayan sallah zai kaisu"

"Eshan yace "to kanwata bari mu tafi kinga dare yayi yanzu zamu dawo gobe."

kai kawai ta ɗaga masu tana mamakin ya aka yi suka zo gidan su ita batan san me yake faruwaba."

Amir ya kama mata hannu suka shiga cikin ɗakin su tare da Mama mairo.

Suna shiga suka kwanta amma bacci yaki zuwar ma Amira da Amir.

Amir ya kalleta "yace Yaya tunda na ƙasa baccin bari nayi Alwala nayi nafila na gode ma Allah da yabaki lafiya cikin lokaci."

Amira ta kalle shi tace "wai me ya sameni ne?"

"Yace muje muyi nafila mu gode ma Allah da ya baki lafiya sai na baki labarin komai da ya faru."

Haka suka je suka yo Alwala suka yi nafila raka'a takwas sun daɗe sun Addu'a sanan suka tashi kowa ya hau kan katifar shi da Abbi ya sa an kawo masu katifu.

Suna kwanciya Amira "tace ina jinka.

Amir "yace tunda Umma ta buga maki katako kika suma bayani an kai ki asibiti akace kin manta komai naki muka shiga tashin hankali nan dai yaba ta labarin komai da ya faru a asibiti da yarda Abdul yai ta zuwa yana kula da ita har zuwa yanzu da suka zo gidan da yarda ta dawo daidai.

Mama Asabe tana jin su tayi kuka sosai amma su Amira basu san batayi bacci ba.

Mama Asabe a zuciyar ta tana tunanin wasu matan uban marasa imani haka su basu tunan yanda rayuwa zata iya juyawa ita abin da ya bata mamaki wai Ummace da wannan halin matar da idan ka ganta baza ka taɓa ce wa zata iya yin wannan abin ba.

Umma "tace haba Mama meye haka kiyi shuru mana."

Mama ta buge ta tana cewa "nice na kashe Alhaji nice nasa mota taje ta buge shi wajan bokan kan bishiya naje shine ya taimaka min wallahi nice nayi ma Hadiza asiri nice."

Yau take sallah kowa ya ɗau wanka da Babba da Yaro da mai tsafta da ƙazami.

Amira sun shirya cikin tsadaddun yan kantin da Abbi ya sai masu tare da yaran Umma dan suma yanzu sun fara son Yan uwan su bayan sun gama shirin suka tafi masalaci.

Eshan shida Abdul sun dau wankan su cikin wata bugagiyar shadda Wada ta amsa sunan ta shada fara ce kal an masu aiki kalar na sarauta har da malun malun kamshi kawai ke tashi humm ba a magana.

Abdul ya kalle Eshan yace "kamata yayi ace Amira ce ta fara ganin wannan wankan naka."

wata uwar harara ya makamai sai ji suka yi Farha nace wa "Yaya Abdul Auntyn muce Amirar dan Allah ka kaini wajan ta."

Eshan yace "baza kije ki dame ta ba dan beby ta bata son wahala Abba dake bakin ƙofa yana kallon su yace "Muhammad kaci gidan ku mara kunya."

Umma Mutanan dake ciki ɗakin suka ce kada ta damu ai ba a daukar maganan mara hankali wannan maganan ta ɓata mata rai jin ance ma Maman ta mara hankali.

Kowa yayi shuru yana sauraro abinda Mama ke cewa.

A lokacin wani ya shigo cikin ɗakin wanda yasa mutanan ɗakin tashi tsaye cikin tashin hankali.

𝑀𝑅𝑆 𝑊𝑅𝐼𝑇𝐸𝑅 𝒄𝒆
✨✨✨
DAFIN ZUCIYA

✏️By Fatima Binta Hussain✏️
https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 32

✨✨✨✨

Eshan jin abin da Abba ya ce ya sa shi yin ƙasa da kai ya na sosa ƙeya.

Farha tace "Ai kam sai na faɗa ma Mame ince ɗanta ya zurma love."

tana gama faɗa haka ta ruga ta shiga ɗakin Mami tana dariya.

Amira bayan kowa ya gama shiryawa suka fito suka kama hanyan masalaci suna tafiya suna kabbara.

𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉𝒖 𝑨𝒌𝒃𝒂𝒓 𝒌𝒂𝒃𝒊𝒓𝒂 𝒘𝒂𝒍 𝒉𝒂𝒎𝒅𝒖𝒍𝒊𝒍𝒂𝒉𝒊 𝒌𝒂𝒔𝒊𝒓𝒂 𝒘𝒂𝒔𝒖𝒃𝒖 𝒉𝒂𝒏𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉𝒊 𝒃𝒖𝒒𝒖 𝒓𝒂𝒕𝒂𝒏 𝒘𝒂 𝒂𝒔𝒊𝒓𝒂 𝒍𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉 𝒉𝒂𝒊𝒍𝒂 𝒂𝒏𝒕

𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉𝒖 𝒂𝒌𝒘𝒃𝒂𝒓 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉𝒖 𝑨𝒌𝒃𝒂𝒓 𝒘𝒂𝒍𝒊𝒍𝒂𝒉𝒍𝒂𝒉 𝒉𝒂𝒎 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉𝒖 𝑨𝒌𝒃𝒂𝒓 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉𝒖 𝒂𝒌𝒃𝒂𝒓 𝑳𝒂𝒊𝒍𝒂 𝒉𝒂𝒊𝒍𝒂𝒍𝒂.

Suna tafiya suna yi har suka isa masallaci suka samu waje suka zauna suna jin huɗuba kafin a gabatar da sallar edi.

Umma ita ma ganin wanda ya shigo ne ya tada mata hankali cikin fitar hankali tace "Mansur!"

Shi kam wanda aka kira da Mansur wani Murmushin gifan baki yayi yace "tabbas ban mutu ba kuma shima Baba bai mutu ba."

Duk yarda Umma da take son ta ɓoye abin da ke san fita daga zuciyar ta tace "Allah me iko mu ai munyi tunanin kun mutu jin ance ba a ga gawar ku ba".?

Yace "kema bakiji me ki ka ce ba cewa ki ka yi ance."

Yaci gaba da cewa "anso a hallaka rayuwar mu nida mahaifina amma Allah bai yi."

Yace "mutane na bani mamaki da suke man tawa da Allah kada ku manta koda duk mutanan duniya zasu haɗu dan su wulaƙan taka wlh idan Allah bai yarda ba bazaka taɓa wulaƙan taba haka zalika koda mutanan duniya zasu taru dansu azurtaka idan Allah bai nufa ba baza ka taɓa zama ba".

Kowa da ke ɗakin jikin shi yayi sanyi banda Umma da tayi zuru zuru da ita..

Mama kam haukan ta ƙaruwa yayi ma ganin dara yayi yasa duk kowa ya tashi ya tafi aka bar Umma kaɗai da Mama.

Umma ta yanke shawaran kiran Abbi ta bashi haƙuri dan ita baza ta zauna da Mama tana masu tune tune gwara ta tafi idan komai ya daidai ta ta dawo.

Eshan daga masalaci suka koma gida zawa yamma zasu ji wajin Amira yace "Farha ta shirya za aji da ita."

Mom ita kowa na murnar sallah amma ita bata ita take ba.

Ladidi ko masalaci bata samu damar zuwa ba saboda ciwo ya ishe ta.

Ganin kowa ya tafi masalaci yasa ita kuma ta tafi asibiti.

Abbi bayan sun dawo masalaci Abokansa sun zo gida dama haka suke yi duk shekara gidan Abbi ake zuwa daga masalaci sai anci ansha yau ma hakan ta kasance suna cikin cin abinci yaga kiran Umma ganin kiran ta ya bashi mamaki me ta kira tayi mashi.

Bayan ya ɗaga wayan suka gaisa ta bashi haƙuri akan abinda ya faru da nuna ladama akai.

Ganin haka yasa Abbi yace "ta shirya ta dawo gobe".

Umma ita tunda tayi mai daɗin baki ya haƙura bazata kai gobe ba a yau
zata bar garinsu.

Ladidi wani Likita ba musulmi bane ba tayi mai bayanin abin da ke damun ta Likitan ya kalle ta da mamaki dan jin bayanin da tayi mashi.

Yace mata wata cuta ce ake kamuwa da ita ta hanyar yin jima'i ta baya da kuma cututuka yace idan bata bi a hankali ba gabanta zai iya ruɓe wa.

Sosai hankali ta ya tashi jin abin da yace nan ya bata shawarwari da abubuwan da zata yi.

Sanda ta dawo gida suma Duk sun dawo daga masalaci.

Tashiga gidan da salama Amarya dake zuba ma ɓaki abinci tace "a'a ina kika shiga ne inata jiranki kidawo mu yi aiki gashi har na gama".

Ladidi tace ta "biya gidan wata ƙawarta ne".

Amarya tace "kodai kinji asibiti"

jin hakan yasa gaban Ladidi faɗuwa.

By Fatima Bintu hussin

DAFIN ZUCIYA
Chapter 12 · 0% Book details