← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 96

Sashe 85

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunta ya kama ahankali tareda hadewa da nasa tafin hannuwansu suka Hadu bayan tsawon lokaci da suka dauka batareda ganin juna ba ko jin juna.

Ajiyan zuciya me sanyi ya sauke Yana Maida idanuwansa akan cikin Dayake kasa gasgata shine ubansa,
Shine zai haifi Yaya da macen da tinaninta kawai ke dakatar da duniyarsa gabaki daya bare kallanta da idan tai masa yake Jin itace dalilin duk Wani farin cikin rayuwarsa.

Hannunsa Daya ya daga Ya Dora akan cikin take Wani numfashi me qarfin gaske ya kufce masa kowannen kofan zuciyarsa na budewa wasu sabbin feelings suna shiga suna narkashi.

Shafa cikin ya sake yi ahankali Yana kallansa sbd mamakin ganin cikina a cikin LA dinsa dayake Tina lokacin farko Daya fara ganinta a baby ya dauketa cikin zanin haihuwanta Bai dauka itace zata basa feelings da farin cikin ganin yayansa a cikinta ba sbd lokacinda Abeeda take da cikin Haydar nesanta kanta tayi dashi ta koma porthcrt gaba Daya sbd batason ya ganta da ciki kamanninta wai zasu Sauya batason ya ganta da kammanin masu ciki Dake kumbura komai Dan haka Sam bai samu dama ta kasancewa da 'dansa lokacinda yake cikin ciki ba,hakama Bai samu Daman sanin dandano da dumin matarsa lokacinda takeda ciki ba.

Gaba daya Jin kansa yayi kaman sabon matashin saurayi Dan haka ya Jima sosai kafin ya fito suka tafi gida da Mr Jameel Dan wanka da sauya kayan jikinsa ba Farha kawai suka bari wadda itama hankalinta ya kwanta da samun cikin Amatun baiyi komaiba.

Haydar da Abdulhameed sun dawowa gida Haydar rufe kansa yayi a daki
Abdul yayita son magana dashi Amma Sam baya buqatan kowa a yanzu kansa yakeson ya sake,
Abinda yafi masa ciwo shine yanda Amatun ta iya boye masa aurenta da cikinta bayan basa boyewa juna komai.

Abdulhameed ganin Haydar din yaqi sauraronsa ya sakashi qyalesa ya tafi gurinsu kawu Dake bq Dan su gaisa.

Dawowan ASH mansion din ya Saka mum Aisha,maamah da Husnah shiga sabuwan sanyin jiki da fargaba.

Ga Abdulhameed ma Sam yaqi zuwa gurin maamah din bare taji lafiyan Amatun Dan Shima abin nasu ya ishesa ya rasa yaushe mahaifiyarsu ta Dena kaunar yayanta da Kwanciyar hankalinsu tareda rashin sanin inda tawakkalinta da hakuri da Nutsuwarta duk suka tafi tsoro ma yakeyi idan ba maganin Husnah takesha ba itama matsalan ke Neman tabata.

Gaisawa dasu kawu Abdul yayi ya zayyana musu abinda yake faruwa ba duka ba kawai dai iya qin amsar auren da maamah tayi sun gigita rayuwar Amatun gaba Daya gashinan yanzu tana asibiti ta kusa rasa cikin dayake jikinta.

Shiru dukkaninsu sukai cikin baqin mamakin duniya daya kashesu.
Kawu bello cikin mamaki yace

"Wato Asmau ciwon rashin tinani ya sameta kenan shine tazo ta zauna muka gaisa lafiya lafiya ta rufemu mu gama gaisuwa mu koma Se kawai ta kashe auren na da muka Hana kanmu zama muka Hana kanmu tsayi gurin yawon malamai a sake tsuqe mana shi karya balle Ashe muna zaune ganinta kawai zamuyi da Amatun ta kaso auren,cabdijm."

Kawu ashiru kuwa rasa abin fada yayi sbd baqin cikin Asmaun da mamakinta Daya siqesa.

Kawu yusufa kuwa kallan Abdul yayi Yana cewa

"To ai shikenan tawa kanta Dan kuwa wlh kafarmu kafarta ba zaman da zata ci gaba da yi anan din,Banda rudun iska Daya shafeta a gidan sirikinta kamata yayi ace har mantawa ma ariga yi da tana gidan sbd kullen da zata ringa yiwa kanta ta zauna guri Daya Amma shine sbd samun guri har yawo takeyi koina a gidan hardasu dambe akan cikin siriki,
To zanga uban dazai Hana a Haifa cikin tinda sune sukai mata cikin."

Shiru Abdulhameed yayi maganganunsu suna Dan Sosa zuciyarsa sedai Kuma Yana fatan akawo karshen matsalar tinda maamah su kawun ne kawai suke fada ta zaunu a gurinta sai Kuma ASH.

A cikin gidan kuwa a Palo suka zauna shiru kowa na jiran shigowan ASH Amma shiru sbd ta palonsa n qasa ya Haye zuwa samansa batareda sunsan ma ya shige din ba.

Wanka yayi da ruwan dumi toilet din na gaurayuwa da qamshin tsadaddiyar Aesop liquid soap dinsa me tsada da sanyin qamshi.

Yana gamawa ya fito daure da towel jikinsa na tsiyayar ruwan da kusan ke qarawa murdaddiyar jikinsa daukan hankalin Wanda ya Gani.

Goge jikinsa yayi da towel yana tsaye gaban mirror ya shirya tareda barin gurin ya Saka Fendi sweatsets ya fito sallan magrib da aka kira.

A gurin sallah su kawu suka samu ganinsa Shima sai alokacin yasan d zuwan nasu ya gaisa dasu sukai sallah
Bayan sun fito Kai tsaye palonsa na baqi da suka fara sauka ya Isa dasu suka zauna anan suka sake gaisawa dashi suna masa gaisuwa a tsananin girmamawa.

Bayan sun gama miqa gaisuwarsu ta rasuwar Abeeda kawu bello ne yafara jeho maganar jikin Amatu Yana mata sannu da fatan samun lafiya kafin suka sanar dashi sunji komai daga bakin Abdulhameed.

Fada sosai kawu bello da kawu yusufa sukai duk Yana sauraronsu har suka gama sai alokacin ya qara sanin wasu abubuwan na tashin hankalin da suke zubawa a gidan ya hada da Wanda yaji a bakin Farha yau din komai da komai.
bayyanarda tafiyar da zasuyi da maamah sukai daga qarshe.

Sai da sukai shiru ya Kalli Mr Jameel dayake shigowa yace ya kira masa kowa duk suzo Yana nemansu.

Mr Jameel na ficewa ASH din ya Kalli su kawun Daya bayan Daya kowannensu yasha shaddarsa ta Roba da hulunansu da baimasan wane kalar Karin ne dasu ba Dan ta kawu yusufa kaman shape din jirgin kwale kwale.

Uzaifa ya juya Yana kalla Wanda Shima yake jikin shaddar robar green Shar da ba hula akansa Dan haka qananun gashin kansa Mai kama da gonar Aya yake bayyane.

Kawu bello yafara kalla bayan ya sauke numfashi ahankali Baya buqatan tashin hankalin dazai taba L.A ko lafiyan dansa dayake cikinta Dan haka Kai tsaye ya sanar dashi hukuncinsa da sauran bayanan abinda yake buqatan daga garesu.

Daga kawu bello har kawu ashiru da uzaifa kusan gaba dayansu Wani girmamman farin ciki me tsananin dadi ne ya rufesu Dan kuwa abune Daya samesu batareda tsammani ba.

Shigowar su mr Jameel dasu mum Aisha na bayansa ne harma dasu Abdul da Haydar ya Saka su kawu gaba dayansu zubawa kofar idanuwansu cikin tsananin farin ciki suna Dan washe Baki tareda boye murnarsu.

Zama dukkaninsu sukai kowa jikinsa na jiqewa da zufa musamman mum Aisha da Husnah harka da maamah,
Abdul da Haydar kuwa basusan meye dalilin Kiran ba tukuna.

Kallan inda su maamah suke Daya bayan Daya kafin ya tsayar da kallansa kan Husnah wadda take sake tsinkewa.

Bakinsa a natse ya Yana dauke kallansa daga kansu yace

"Dukkaninku ku shirya gobe za'a daurawa kowaccenku aure Kuma a goben zaku wuce.

Maamah ya kalla yace

"Malam bello yace ze mayar da aurensa na Kuma amince masa da Hakan,
Malam ashiru kuwa na basa auren Aisha,'dansa uzaifa Kuma auren Husnah,
Kowa ya shirya duka gobe ana daurawa zaku wuce.
Kowa ta tashi ya tafi shikenan.
##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

75
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

*************
Maamah ce take hawaye suka tsinke mata tana rufe idanuwanta zuciyarta na daukan nauyi me girma,

Mum Aisha kuwa gushewa hankalinta ya fara yi na seconds tareda jinta gaba Daya kafin ta ji ta Dan ji jinta ya dawo ta Kalli ASH din da dukkanin karfin ganinta hannuwanta na daukan rawar datafi rawar tela murya a rikice tace

"Auren addinin islama Wanda nasani???

Wani kallon Daya Sakata rikicewa ASH yayi mata da idanuwansa da har lokacin Basu koma daidaiba..
Rudewa tayi take tana rikicewa a rude ta fito daga bayan Maamah datake zaune bakinta na rawa hakama jikinta tace

"Ka yimun Rai ka dubi Allah ka dubi Annabi ka dubi maraicina Banda uwa Banda Uba Se Kai se Naufal,
Kaine uwata Kaine ubana wlh na tuba nabi Allah na bika ta tattara tashin hankali duk na aje Amma Dan Allah Karka auramun aure da girmana yanzu Kuma a kauyenda mota ma Bata shiga wlh rayuwata mutuwa zatai,haukacewa ma zanyi,Dan Allah kayi hakuri Karka min auren dole da girmana na tuba,Dan Allah kayi hakuri.....

Tsit palon yayi maamah ma hawayen takeyi tana sharewa kai a qasa Dan ita bama zata iya magana ba Dan Iya ganin mugun Abu yau shi take Gani sirikinta zai mata aure kaman na dole,tayaya ma zata rokesa tace Dan Allah karya mata auren? innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Husnah kuwa Bata motsaba sbd Bata dauka ita Husnah din ake nufi sbd kwata kwata ma Babu abinda ya hadata da auren kowa yanzu bare,

Abdulhameed ne da Haydar suka shiga tashin hankalin hukuncin Husnah da maamah kawai da basason ta koma kauye Dan haka Haydar ya juyo Yana kallan Dad din nasu zaiyi magana ASH ya daga masa hannu kadan alaman bayason Jin komai.

Su kawu kuwa washe Baki suka hau yi suna sauke kansu qasa kawu ashiru sai kallan mum Aisha yakeyi yanajin shi gaba Daya ma Sonta ya kamasa a gurin.

Uzaifa ma Husnah ya zubawa jajayen idanuwansa masu girma kaman yalo ya taso saman manja
gaba dayama Jin yayi yawunsa na tsinkewa kaman zasu zubo masa da kallanta kawai,
Baitaba tinanin zai taba samun mata irinta ba koma a mafarkin duniyar aljanu aka Kaisa kuwa.

Ganin irin kallan da uzaifa kewa Husnah yasaka Haydar kasa shiru cikin tsananin damuwa da tashin hankali yace
Chapter 85 · 0% Book details