← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 96

Sashe 19

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bangare daya rashin samun yanda yakeso a aynzu yasa idanuwansa suka dawo Kan 'yan matan gidan masu aiki yafara farautarsu Daya Baya Daya yana lalabewa duk da qyamarsu yakeyi Amma dai tinda Yana samun yanda yakeso sai yana manejinsu hakanan.

A qanqanin lokaci kusan Yan matan biyu masu aiki ya Maidasu kaman matansa Babu ranar da baya kusantarsu idan yayi yau da wannan gobe da dayar zeyi.

*****AmatulMaleek datafi duk matan dasuke gidan kyau Tim daga masu gidan har masu aiki itace maqale a zuciyarsa da idanuwansa,
Kyakkyawa ce hakama Mai aji da kamewa ce Sam saikayi sati nawa a cikin gidan batareda ka Sakata a idanuwanka ba Dan Babu abinda yake fiddota sai ayyukan da baa rasaba tinda karatu yanzu Baya barinta ma ayyuka tini maamah ta dauke mata iyakacinta karatu da hutawa sai ranakun datake gida take Saka hannu a wasu ayyukan gidan.

Ta bangare daya siyasan ASH TALBA ya dauko zafi gadan gadan sbd lokacin zabe Daya gabato sai gidan yakoma tsaronsa yanata qara ninkuwa Dan Babu abinda Ash ya hada da tsaro tareda kariyar familynsa.

Husnah Bata Nan tana porthcrt gurin Hutu tareda Haydar gun dangin mum dinsu wadda daga can kafin su dawo zasuje dubota.

Abdulhameed ma wannan Karan ya sake zuwa kauye Shima ya dubo dangin nasu mahaifin a karo na uku Dan haka daga AmatulMaleek sai maamah sai su mum Aisha.

Kwadayinsa Naufal ya fara bayyanarwa akan Amatu Dan haka maamah tafara shiga fargaba da shakku Amma dai Bata nuna komaiba ganin itama Amatun tafara shiga taka tsantsan dashi.

Mum dinsa ganin wadda yafara kaiwa hari baqin cikinta ya tsananta ta kallesa a lokacinda suke zaune palonta tace

"Wane irin Dabba kakeson zama ne Naufal akan mata?
Wace masifa da balai ne wannan ni Aishatu take bibiyata,
Nayi Dana sanin dawowarka ma Dana sani nabarka acan qasar Kayita abinda kaga dama idan yaso ranarda ASH yasan abinda kakeyi Saiya dakatar da duka kudinsa da aka Sakar Maka kana wannan ta'addancin alokacinne zaka gane me nake nufi daka nutsu mu samu gurin zama da gurbi a wannan dukiyar......

Magana ya Bude Baki zeyi ta katsesa cikin baqin ciki da takaici tana cewa

"Ka fitarda macen aure kawai kayi aure tinda bazaka iya kame kanka ba kayo mummunan gado harka zarta,
To wlh Bazan iyaba,idan ka lalatamun komai to tabbas saikaga yanda baka so Dan wlh Nima dubu Daya bazaka sake samu ta hanyataba tinda zuciyarka ta Dade da mutuwa a gurin mata."

"AmatulMaleek kuwa da wuri da gaggawa kayi saurin dauke idanuwanka akanta Dan duk kaje ka lalata musu ita to ko ni wlh Kila qarshen zamana a karkashin ASH yazo bare Kai Dan akan Asmau zai iya aikamu inda mukaqi jinin zuwa wato inda muka fito Dan haka Maza Maza ka cire kwadayinka akanta tinda ka riga ka gama lalata Yan aikin gidan Nan tas,
Kai ko qyama bakaji ne?
Bazaka iya hakuri ba bayan kwana bibbiyu kaje ka samu na wajen ba ka biyasu ka sauke buqatarka Amma ace Yan aiki ma nema kake,mtswwee.

Zafi zuciyarta keyi kaman zata fashe Dan tana cikin baqin cikin wannan muguwar kaddarar ta hada jini da hamis Da Danta ya dauko halinsa.

Fadanta da zafinta koyaushe Sosa ran Naufal sukeyi Shima sbd idan ta fada kalamanta Sam Babu alkhairi a cikinsu koyaushe Dan haka Bai iya cewa komaiba Shima ya miqe yabar palon Dan kuwa ayanzu yake Jin AmatulMaleek din a ransa ko aurenta ze iya yi Dan biyan buqatansa idanma har be samu yanda yakeso ba kenan
Idan Kuma mum din ta matsa akan maganar auren Amatun zai aura kawai kowana ya huta.

AmatulMaleek data gaji da kadaici sai kawai ta fara fita wasu lokutan zuwa guraren Shan iska musamman tinda Hutu sukeyi gashi ba kowa.

Ana cikin Hakan Barr Faisal turaki ya ganta a cikin gidan zuciyarsa ta kamu da kaunarta alokaci Daya duk da ya jima sosai da familyn TALBAs din Amma Bai taba ganinta sbd shine lawyer din Madame Abeeda Kuma shine babban 'dan Wani yayanta Dake porthcrt da maman babansa da maman Abeeda uwa daya Uba Daya suke Dan haka dadynsa yayan madame Abeeda ne,

A UK sukai zama taredasu Abeeda har suka rigasa dawowa Nigeria Amma Shima ya jima da dawowa kawai dai Baya zuwa Nan dinne sbd madame Abeedan Bata Nan hakama da Husnah kawai yake communicating Shima sbd Husnah dinne tafi nemansa koda yaushe har shaquwansu yayi qarfi sosai da sosai,

A bangaren Husnah Faisal turaki ba iya Dan uwanta take kallansa ba,
So ne take masa me tsananin gasken da kusan ko familyn mum Abeedan sun sani,so ne me tsananin gaske gaba Daya ma she's obsessed,
Bata iya boye sonsa duk da tsakaninsa da ita baitaba fada mata so hakama yasan yanda take tsananin sonsa sedai bayajin zai iya takura kansa ya aureta batareda yana sontaba,Hakan zai cutatar da ita yakuma cutatar dashi Amma Sam ta kasa gane Hakan shikuwa a matsayinsa na dan Boko sosai da sanin YANCI ya gama ratsashi bayajin zai iya auren damuwa da takura tareda cutatar da juna Dan kuwa Yanda yake Sonta na tsakani da Allah har zuciyarsa ta Yan uwanta bayason ya aureta su lalata rayuwarsu gaba Daya ya zabi tsayawa kan raayinsa duk maganar da iyayensu da Yan uwansa keyi ya tsaya akan Hakan.

Ayau Kuma Daya zo duk da Husnah batanan yazo ne sbd aiki Daya dawo dashi Abuja da zama Dan haka yashigo su gaisa dasu mum Aisha harma da Naufal dayake mutuminsa.

Sosai yayi mamakin ganin AmatulMaleek wadda yake Jin sunan a bakin Husnah tin shekaru...

AmatulMaleek dinne tayi serving nasa duk Wani abin motsa Baki tareda gaidasa cikin nutsuwa ta juya ta fice daga babban palon gidan Takoma daki Dan dama fita zatayi zata wankin Kai.

Mum Aisha da lokaci Daya taso fahimtar Barr Faisal akan kallan Dayabi AmatulMaleek dashi take taji Babu ma abinda zata so a yanzu Daya wuce barr din ya aure AmatulMaleek din tabar gidan kafin Naufal ya janyo musu abinda zai riguzasu akan kwadayinsa da Amatun Dan tasan tinda ya qwallafa Rai akanta sai Allah idan zai hadiye wannan tsinannen kwanadayin nasa Dan haka zama ta gyara tafara yin bayanin waye AmatulMaleek din a gidan tareda yabon halayenta.
#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

18
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

************
Shiru kawai Faisal turaki yayi Dan kuwa shi a tsarinsa shine yake karantar abinda yakeda raayi akansa da kansa Baya daukan bayani ko yabawar Wani Dan haka duka bayananta Babu Wanda ya damesa hakama Babu Wanda zai qara masa Sonta ko Rage masa Dan haka shiru kawai yayi harya gama ya fita ya wuce tinani da yawa ne akansa.

AmatulMaleek da bama zatace Ta Kalli fuskarsaba bare riqe kamanninsa tini ta manta da Wani baqon da Akai ta kama alamuran gabanta.

Shikuwa kwana biyu ya sake zuwa gidan dayake Shima yasan maamah wannan Karan da ita yayi fira sosai har Amatun ma Saida suka gaisa ya Dan jata fira gameda karatunta sbd law take karanta itama.

Yanda ya ringa fahimtar da ita wasu abubuwan gameda course din ya sata Dan sakin jiki tana fahimtarsa Wanda har dare Yana gidan Saida yayi dinner tareda jamaar gidan kafin ya tafi.

Dayake me saukin Kaine shi da sanyin hali kaman Amatu tini suka fara fahimtar juna Yana Bude mata sani akan karatunta da Daman tana Neman me zaunawa da ita suyi karatun yanda ya kamata sbd a school Batada qawaye.

Karatuta dayazo Daya da nata shine ya Basu Daman fara kusanci da juna da yawan waya batareda tasan Menene abinda yake zuciyarsa akanta ba,

Maamah data fara fahimtar sosai son Amatun Faisal turakin keyi sai Hakan ya Bata nutsuwa sbd Bata taba sanin Husnah Faisal dinne a ranta ba sbdz Bata taba fada mata ba su mum Aisha ne kawai suka sani da sauran dangin Abeeda.

Dan haka ita idan har Amatun zata auri Faisal turaki hankalinta zai kwanta da yanzu yake a Dan tashe da lura da Naufal ma Amatu yakeso.

Hutunsa Amatu ya qare Dan haka su Husnah Basu dawoba a satin sai kusan bayan sati biyu sbd basa qasar suna Greece tareda Dad dinsu gurin Madame Abeeda.

Amatu tayi mamakin ganin Faisal turaki a university dinsu Ashe Nan ya dawo da aiki sosai tayi farin cikin Hakan Dan kuwa ba qaramin taimaka mata Hakan zeyiba.

Shi kansa yayi mamakin farin cikinta shiyasa ma Bai fada mata ba tin Farko,
Sabuwar shaquwa suka sake samu ta Hakan Dan wasu lokutan shine yake dawo da ita gida.

A satin dasu Husnah suka zasu dawo a satin ya sanar da AmatulMaleek son da yake mata tareda Neman damanta na Neman aurenta idan sun sake fahimtar juna.

Da farko mamakinsa tayi sbd Kai tsayensa daya sata Jin nauyinsa tinda baa taba furta mata ana Sonta ba bayan Haydar da kullum yake fada mata yana sonsa sosai takuma San shi nasa wasa da Kuma kaunar Dake tsakaninsu ne.

Kunya ta hanata amsa masa Amma Shima yaga alamar ya samu karbuwan Dan haka sai hankalinsa ya kwanta sosai ya tashi daga matsayin Dan uwa dayake ya koma na masoyi Kuma mijinta inshallah.

Bata fadawa maamah ba saida suka kwana biyu maamah taga yanayinsa ya sauya daga yanda yake gaidata da sauran abubuwan.
Chapter 19 · 0% Book details