← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 96

Sashe 17

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tashi bazanci abincin dakaiba Kaci a gurin Abdul"

Abdulhameed Daya Fi kowa sanin yanda Amatu take a zuciyar Haydar da gasken gaske cewa yayi

"Karma yazo mun Nan bazanci tareda Shiba anjima kadan shiryawa zakuyi kece Zaki fara cemun munafuki Dan haka ku qarata can Yana zuwa Nan fasa masa hannu zanyi"

Hakan Daya fada yasa Amatu jifansa da mugun kallo itama tana cewa

"To koma gurin maamah Kaci Dan bazan ci da kaiba na fasa"

Maamah ma cewa tayi ta gama ita Kam Dan haka sedai ya dawo gurin Amah din tasa.

Marairaice fuska da idanuwa yayi Yana cewa

"Anty Amahn Haydar Talba"

Hakan Daya fada ya sata dariya Bata shirya ba Dan haka dole ta barsa sukaci abincin Yana sake bayyana musu yanda Amatu take a zuciyarsa da gaske Amma duk suna dariya kawai sbd sanin wasa yakeyi dakuma kaunar datake tsakaninsa da Amatun datafi ta kowa.

Harsuka gama kusan tayata cin abincin kawai yayi bawani abin kirki yaci ba suka fito ya rakata takai komai kitchen suka dawo ya rakata har kofan shigewa daki ta shige ya juya zuwa lokacin yasan kowa ya hallara a dining room, Kai tsaye can ya nufa Yana zuwa ya Tararda kowa a dakin shi kadaine Baya Nan Kuma Allah yasa Basu faraba zamansu kenan Dan haka cikin Nutsuwa ya qaraso Shima tareda kallan Naufal yace

"Yaya Naufal barka da fitowa,
Mum Aisha Ina wuni?ya gajiya?

Husnah kuwa kallanta kawai yayi tareda jefa mata kiss na kumata daga inda yake kafin ya zauna Kofar palon Dad dinsu ta Bude wadda take kawosa dining room din daga palonsa na farko Dan haka dukkaninsu kallan kofar suka juya sukai ahankali kafin qamshinsa ya huro musu cikin gurin Yana gauraya gun gaba Daya.

Sanye yake cikin Ash wandon Fendi fa farar rugby shirt sai black Lorenzo slippers marasa nauyi da tsadan gaske,

Idanuwa Naufal ya zubawa ASH TALBA Wanda ya kasance tamkar Wani madubi a idanuwansa da zuciyarsa,
ASH TALBA namiji ne Daya amsa sunan Maza ba muna Maza ba,
Namiji ne da kallo Daya zama masa kasan namiji ka kalla Tako wanne bangaren,
Babu Wanda ze kallesa yace shine ya haifi matashin saurayin Dake gabansa Haydar Talba,
Namiji ne da ko shi dayake amsa sunan matashi me lokacinsa zai rissina masa sbd ko karfinsu bazaa hada ba tinda daga karfin jiki harna zuci,harna Imani,harna komaiba ita dukiya da kwarjini tareda wata irin nutsuwa da aji bama zai hada kansa da the grt ASH TALBA ba da ake fada,
Tako Ina Ash namiji ne tsayayye da babu abinda yake masa shamaki.

Lafiyayyar fatarsa data ke daukan idanuwansu ya kalla ganin wato shi Hutu da jiqa cikin arziki da nutsuwa Wani abu ne na daban da idan Allah yayika cikinsu basa boyuwa,
Ya rasa Menene ya Saka akoda yaushe ASH TALBA da komai nasa daban ne,
Komai nasa unique ne,
Duk abubuwan tsadar rayuwar su Naufal yake Siya Amma haryanxu inda ASH yabi ya wuce ma yafi qarfin gwajinsa,
Duk shekarun Nan Babu abinda yake ran mahaifiyarsa bayan ya zama tamkar the grt ASH TALBA,shi kansa babban burinsa ne ya zama kamar Ash Talba Amma bayajin Hakan zai iya yiyuwa Dan kuwa izza da asalin kwarjini da haiban tareda kamewansa duk a jininsa suke hakama shi arziki irin wannan na Ash din Allah ne kawai zai baka irinsa ka samu zamowa.

Duk Izgilancinsa da nasa zafin Kai a gaban Ash Jin yake ya zube qasa warwas shiyasa Baya iya ko kallan cikin idanuwansa duk tsanani kuwa,
Ita kanta mum Aisha datake 'yar uwarsa kwarjinsa durqusar da ita yake a gabansa Dan haka take gujewa tsayuwa a gabansa a duk lokacinda zata zartar da hukuncinta acan cikin gida Dan Bata iya kallansa a fuska ta aikata abinda take aikatawan.

Gaba dayansu dauke idanuwansu daga kansa sukai har ya iso a natse ya zauna tareda dagowa ya Kalli Naufal da shine ya fara gaidashi Yana masa barka da fitowa.

Fararen idanuwansa masu kwarjini ya saukar akan Naufal din da nutsuwa harma da kulawa yace

"Yaya gajiya?

Murya a natse Naufal ya amsa Yana sake gaidasa tareda sake jajanta masa jikin aunt Abeeda harma da mata adduar fatan samun lafiya.

Amsawa yayi a natse Yana kallan abincin da Husnah take serving nasa a taqaice yace

"Ya Isa"

Tambayan Naufal din yafara yi sama sama akan komai na karatunsa Daya kammalo Shima Yana basa amsa a natse cikin Kamala Dan dole idan zakayi magana da ASH din ka nutsu.

Abincin suka fara ci Babu me magana hakama kowa da kusan abinda yake ransa tsakanin mum Aisha da Naufal Wanda yakoma Wani irin kamilallen mutum,
Itama mum Aisha gaba Daya a jiqe take da zufa kada Naufal yayi abinda zai fara batasa a idanuwan ASH.
#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

16
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

***************
Ash dinne yafara gamawa ya dauki tissue ya goge bakinsa tareda miqewa yabar dining din kafin Haydar da Shima ba Wani yunwa yakeji ba tinda yaci a gurin Amah dinsa.

Bayan Dad dinsa yabi Wanda yaji Haydar din biye dashi har zuwa palonsa ya zauna ahankali akan 2 seater ta Turkish luxury sofas Dake palon sun gama daukan sanyin ac da qamshinsa da kusan komai na palon ya dauka.
Wayarsa Dake gefensa ajiye ya Kai dogon hannunsa fari tas ya dauka Yana cireta daga flight mode ya mayar ya ajiye tareda dagowa ya Kalli Haydar din Daya zauna kusa dashi Yana cewa

"Dad maganar AmatulMaleek din maamah Da karatunta Dana fada maka ne,
Ta gama school din tin kusan last year Amma haryanxu Bata qara gaba ba."

Numfashi Dad din ya sauke tareda dauke kallansa kan Haydar daya marairaice sbd yasan Babu abinda suke tambaya gurin Dad dinsu Bai musu ba sbd sune kadai hasken idanuwansa a yanzu.

Idan Bada Haydar din ya tinatar dashi ba Sam mantawa yakeyi bayan Abdul da kusan koyaushe suke tareda Haydar cewan Asmau nada wata 'yar sbd baitaba ganinta ba tin tana jaririya Daya taba ganinta haryanxu baitaba ganinta ba shiyasa ya manta da Yaya biyu ne da Asmau,
Amma a yanzu tinda Haydar ya tinatar dashi zaai mata komai na karatu a inda Husnah take inshallah.

Kallan Haydar daya gama Saka sakewa da jiran abinda Dad din nasa zai fada yake,burinsa da tsananin fatan buqatansa ta kasance yayi Yana tabbatarda mahimmancin maganar karatun yarinyar a gun Haydar din sbd Babu abinda ya taba buqatama da har sai yazo ya tambayesa sai ayanzu Dan haka ya sake kallansa cikeda kulawa da kauna me qarfin gaske yace

"Kaje Jameel zai mata komai inshallah zata ci gaba tareda Husnah"

Wani irin murmushin farin ciki da sanyin dayake zuciyarsa be ya bayyana kan fuskarsa ya qaraso ya rungume Dad din ahankali Yana cewa

"Thank you Dad"

Da mamakinsa ya Sakar masa tsadadden murmushinsa Yana dafa bayansa tareda nanata masa yafada mata tayi karatu sbd karatu ake makarantar sosai.

Gyada Kai Haydar yayi cikin farin cikin Yana cewa

"Dad zatayi,zatayi karatu sosai,kaima zakayi alfahari da karatunta inshallah"

Gyada kawai dad din yayi Yana duba wayarsa data kawo haske alaman shigowan kira.

Ficewa Haydar yayi cikeda farin ciki,
Surprising din Amah yakeso yayi Dan haka bazai fada mata yanzu ba.

Bayan ficewar Haydar daga palon wayarsa ya dauka ahankali cikin nutsuwa yakai kunnensa tareda amsa sallamar Wanda yayi Kiran Yana bin bayan Haydar da kallo harya fice.

Mum Aisha ma duk sunbar dining din kowa ya nufi bedroom dinsa Naufal kuwa Yana komawa fita yaso yi Amma rashin layin dazaiyi waya ya Sakasa fasawa dole ya shige da wuri.

Washe gari da safe kusan kowa fita yakeyi masu zuwa school da masu zuwa aiki Dan haka daga Amatu sai mamah da masu aikine a gidan yawanci da safe sai yanzu tinda mum Aisha sun dawo.

Amatu ce ta shiryawa mum Aisha da Naufal breakfast ta Jere musu a palon mum Aisha din sbd abincin dare ne kawai kusan Yan gidan sukeci gaba Daya atare sbd ASH da dare kawai yake zaunawa acikinsu cin abinci sai breakfast Wanda shikuma daga shi sai iya yayansa yake yinsa wannan shine qaidarsa sbd Yana son time dinsa na safe da yayansa kawai.

Bayan tagama shirya musu abincin Naufal ne ya shigo palon lokacin mum Aisha din Bata fitoba,

Sanye yake da designers qananun kaya blue Bai Wani Kalli Amatun ba Dan gargadi da iyakar da mum tai masa da duk wata macen Dake gidan Dan haka Koda ta gaidasa amsawa kawai yayi Yana zaunawa sama sama yayi breakfast din ya fice Yana ce mata idan mum ta fito ta sanar mata ya fita.

Ok" kawai ta furta masa batareda itama ta juyo ta kallesa ba daga gyaran palon datakeyi Hakan ya Sakasa dakatawa ya juyo Yana qure kallansa akanta sbd mamakin basarwanta da rashin basa mahimmanci.

Fararen yatsun hannuwanta masu tsayi da kyau ya zubawa hannu tana rufe zip din throw pillow data Dan Bude ta gyara na kujerun palon.

Gangarawa yayi da idanuwansa kan wuyanta da Shima fatarsa take fara tas kaman 'yar Hutu,
Akan kirjinta ya dawo da idanuwansa Ya kalla yanajin zuciyarsa na harbawa da qarfi.

Motsin juyowarta ya sakashi Maida idanuwansa kan kyakkyawar fuskarta yana juyawa yabar palon zuciyarsa na shiga wasi wasi.

Batasan duk abinda ya tsaya yayi din ba Dan haka aiknta taci gaba da yi harta gama mum Bata fito ba dan haka ta tattara ta ficewarta.
Chapter 17 · 0% Book details