← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 96

Sashe 28

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amatu dai an daura mata aure da Me girma ASH TALBA Kuma wlh ko ciwo kika kwanta Se ta tafi Abuja ayau dinnan gwara ki daure ki danne ku tafi sbd Dake ya buqaci komawa ASH din,Idan Kuma kika kwanta ciwo saiki zauna anan jinyar aurenda bakiso dinba atafi ayi zamansa.,
Abdul Maza kamata ta miqe ku nemo ruwa a zuba mata zata qarasa dawowa daidai ku fara shiri.

Amatu Dake jikin Abdul har lokacin ya kalla Kai tsaye ya Kalli amaryarsa da matar kawu ashiru datakewa Amatun firfita yace ku zuba mata ruwa itama farfadowa zatayi ana jiransu komawa zasuyi.

Kan Husnah Dake fidda numfashi daqyar ya Maida kallansa yace

"Itama ciwon zuciyar ne da ita???
Ku kamata itama a Dan yayyafa mata ruwa ta dawo daidai.

Maamah duk yanda take cikin matsanancin halin tashin hankali da mummunan shock da rawar jiki sosai Saida maganganun kawu bellon suka Sakata Bude idanuwanta dasukai jajir batareda ta iya kallan kowaba a cikinsu sbd kirjinta Daya riqe Bata iya ko dogon motsi bare iya magana sai kawai wasu irin hawaye masu tsananin zafi da radadi suka gangaro idanuwanta.

Kawu ashiru ne yace

"Eh kiyi kukan farin ciki Allah ya cika Miki burinki yau an aurar da Amatun,
Allah ya Basu zaman lafiya karki lalata mana farin cikin aurar da 'yarmu da mukai ayau din"

AmatulMaleek kuwa ruwa kawu bello Dayaga su saratu na sanyar zuba mata ruwan ta farfado kada ta firgici da tashin hankali ya aikata suga samu da rashi lokaci Daya da kansa ya debo ruwa zuba mata Yana ambatar sunanta cikin kulawa Yana cewa

"Abdulhameed Maza tayar da ita zaune kada ruwan ya shigar mata hanci"

Tayar da ita Abdul yayi zaune har lokacin Bata dawo hayyacinta ba tadai farfado ne kawai.

Shiru su kawu sukai suna kallanta cikin kulawar da ayau sukaji sunai mata me qarfi.

Kawu ashiru ne ya zauna kan tabarbar Da Amatun ke Akai Yana tattare babban tigarsa guri Daya yana kokarin fara jero bayanai ganin maamah da Amatun suna jinsa.

Kafin fara maganarsa babban yayansu Daya yashiga Mallam Shima gurin ya samu ya zauna sbd baisan abinda yake faruwaba Yana kauyen kusa dasu acan yake kasuwanci sai yayi wata Bai dawoba sai yau din cikin qanqanin lokaci kafin daurin auren akaje aka sanar dashi abinda yake faruwa a gigice Shima ya iso kada su bello da zalamarsu su cinye komai sedai Koda yaxo an daura auren tini Amma Jin Wanda aka daura dashi ya sakashi zubewa gaban ASH din a waje Yana zunduma Godia da Allah ya Sanya alkhairi harda hawayen cewan da Dan uwansu na duniya yau dayayi farin cikin ganin Yan uwansa sun aurar da 'yarsa ga mutumin arziki.

Daqyar yagama gaisuwar ya nufi cikin gidan dayasan ana can ana kasafin sadakin Amatun Daya kusan kunce zariyar wandonsa sbd mamaki da farin ciki.

Zama yayi gefen kawu ashiru Yana gaisawa dasu sama sama Ya amshe zancen ashiru Dayake kokarin farawa na nasihar aure ga Amatun da uwarta datake da niyar daga hankalin auren.

Ganin hawayen da maamah ke tsiyaya bata iya magana ya Saka Mallam cewa

"Asama'u yanzu auren kikewa kuka?
Auren ne bakyaso kokuw mijin da aka daura dashi ne bakyaso?

Cikin mawuyacin hali da radadin zuci me girman gaske ta Bude Baki daqyar ta iya fizgo Kalmar "Babu aure tsakanin ASH TALBA mijin Abeeda da Amatu sbd bazan taba iya karban wannan auren.......

Cikin takaici me tsanani da zafin zuciya kawu bello ya katseta da cewa

"Uban waye ya haramta auren yarinyar data Riga ta zama mata mijinta...

Mallam da zuciya Shima ta siqesa dan idan maamah tace zata cigaba da maimaita maganar rusa auren a shirye yake da jefeta ta kurmance ta yanda bama zata iya maganarba bare harsu riqa jin wannan bayanin nata dayake Shirin musu ta leqo ta koma.

Kawu ashiru kuwa da baimaga dalilin tsayawa saurarontaba wa'azinsa yaci gaba da yiwa Amatu akan zaman aure wadda Babu abinda kunnuwanta ke ji mata dif take.
##MAMUH#
#ASH TALBA
#AMATULMALEEK TALBA
#HUSNAH TALBA
#ABEEDA TALBA
#HAYDAR TALBA
#NAUFAL TALBA

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

26
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

***************
Kawu bello gaba Daya Jin yakeyi ya qagara su tashi su fara Shirin fiddo kayansu su fito sbd ASH din yace yau zasu koma Abujan ko yolan bazasu kwana ba.

Maamah kasa dauka zuciyarta tayi da lamarin gaba Daya Dan haka jikinta yafara Neman rikicewa dole su kawu suka harhada sukaita kanta dole akace a kamota a fito dasu itada Amatun su harma da Husnah suka fito tafiya.

A mota Daya aka Saka maamah da Amatun wadda itama har lokacin bat dawo daidaiba dole Abdul motarsu ya shiga sbd suna buqatansa dukkaninsu.

Husnah mota Daya ta shiga da Dad dinta ta lafe gefensa batareda ta iya ko motsi ba bare magana kaman yanda Shima Babu abinda ya furta.

Faisal ma da kusan Shima a cikin shock yake Baya hayyacinsa dole motocinsu ASH aka taho dashi.

Manyan motocin na barin qauyen gaba daya su kawu suka kwabe manyan rigunansu Dan fuskantar junansu akan uban kudin da ASH ya Basu Dan kuwa tsakanin su da yayansu ba sauki kowa ya shirya abasa kasonsa musamman su uzaifa daya Bada kudinsu daban yace abasu suda suka so auren Amatun.

Hatta su megari babbar kyauta yayi musu
Su kuwa su kawu nasu baa magana ga sadakin AmatulMaleek din Yana hannunsu Dan haka kowa ya kasa ya tsare matse suke dasu Amatun su wuce Daman ayi kason kudin.

Tafiya ce akayo shiru Babu Wanda yake magana a duka motocin sai motar securities dinsa dasuketa murna da farin cikin aurensa tareda mamakin wadda ta zamo matar tasa.,
sai Kuma motar iyayen Naufal da kusan Suma dai suna tattauna yanda lamarin ya kasance ne uwa Uba uncle din dayaso Rabonta ya fado kansa yau shima ya dawo yayi kwanan Kwanciyar hankali da samuwar amaryarsa.

A motansu maamah kuwa daga ita har Amatu dai jikinsu ba sauki tafiyar kawai akeyi Dan haka hankalin abdul dayake gaba Yana kansu Akai Akai Yana juyawa ya kallesu.

Tafiya me Dan tsayi sukai zuwa lokacin duhun yamma ya Sako Kai Dan haka Koda suka shigo gari magrib tayi Dan haka Kai tsaye mansion dinsa Dake garin aka nufa su Kuma su uncles din Naufal masauki kawai Akai dasu Dan daman daga Nan zasu rabo zasubi jirginsu daga masaukin su wuce.

Koda suka Isa Daman akwai aiki a gidan Tini komai yake gyare Amatu Abdul ya kamo ya shiga da ita har makeken bedroom din da aka ce akaita kafin yakoma ya shigo da maamah itama Wani bedroom din Daya kusan girman na Amatun.

Husnah da kanta ta shigo sbd Dad din tini yayi bangarensa sbd alwala ya fito sallah.
Dakin maamah ta nufa ta shige sbd batasan zuwa gurin Amatu tafison gurin maamah din.

Abdulhameed ma alwala yayi ya fito sallar kaman yanda Faisal ma yayi alwala duk suka nufi gurin sallan.

AmatulMaleek da kanta ke tsananin juyawa hakanan ta daure tana ganin jiri ta nufi toilet dayake dakin ta fada hannuwan na rawa ta tsaya jikin kofar lafiyayyan toilet din tareda rintse idanuwanta ko zata samu yar hankalinta ya dawo mata ko kadan ne sbd kanta daf yake da juyewa sbd tinanin komai ta kasa Dan Bata ganewa ma.

Daqyar ta Dan ji karfi ta daddafa ta Isa jikin ruwa Tayo alwala ta fito tana dafa Bango daqyar ta iya fito da kanta dakin tana lalabawa ta Isa Dayan dakin dasu maamah suke ta Bude idanuwanta basa Gani sosai.

Sallah Taga maamah na kokarin tayarwa daga zaune sbd bazata iya tashiba kaman ma ba qafafu a jikinta takeji.

Ganin inda suka kalla alqiblah yasata dawowa dakin itama ta tayar da sallarta sedai jiri sosai yake daukanta Amma ta daure sbd akwai har sallar Azahar a kanta.

Cikin dauriya da karfin zuciya tayi sallolin dasuke kanta tayi magrib ta zame a gurin ta kwanta zazzabi me qarfin gaske kawai Yana rufeta hawaye na bin gefen fuskarta masu tsananin zafi da sai yanzu nauyi da toshewan zuciyarta ke fara motsawa.

Abdul ne ya shigo dakin yayo kanta cikin kulawa da tsananin tausayinta ya tayar da ita zaune suka zauna a qasan dukkinsu tareda jingina da gadon dakin Idanuwansa na sauya zuwa ja sbd shi tako Ina damuwa suke sake nitsasa a cikinta ga bangare daya tinanin Haydar a cikin zuciyarsa dama yanda rana tsaka zaace Amatu ta zama matar ASH TALBA,

Ta bangare daya Kuma yasan Babu Wanda wannan auren zaizo masa a sauki sbd maamah hara abada bayajin zata iya karban wannan auren a yanda Bata hada komai da kaunar datakewa madame Abeeda ba yanzu Kuma ace yarta ta cikinta ce ta auri mijin Abeedan.

Kasancewar Abdul a tareda Amatun ya Sakata sakin kukan Daya taso daga qasan zuciyarta gaba Daya cikin sauti mara qarfi da qunci me tsanani.

Hannuwanta ya riqe mata sbd rawar da sukeyi cikin tausayawa Yana Bata hakurin da baima San meyake cewaba Dan Shima Yana cikin shock din sedai nasa me sauki ne Dan aure ne dai kamar kowanne aure aka daura hakama tinda anriga an daura Babu abinda tashin hankalin zai kawo bayan hakura a rungumi kaddara.

Kuka takeyi sosai duk Wani nauyi da quncin zuciyarta na saki.
Chapter 28 · 0% Book details