← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 96

Sashe 84

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mum Aisha da baqin cikin Husnah da maamah ya danne zuciyarta Dake tafasa kaman zata babbake ta kallesu tana Jin inama Wani balain ne ya samesu su taru su halaka akan sabuwar masifar dasuka tado musu akan Wanda haryanxu basusan meye hukuncinsu ba gurin ASH din.

Maamah ta kalla zuciya na tafasa tace

"Na dauka Husnah haukarta ta tabin hankalin data samu ne Ashe harda qarin gadon haukar uwar riqonta,
Ke yanzu da Abeeda ta rasu Bata duniyar meye naki na tada masifar ciki idan ya bayyana a jikin Amatun inace sbd Abeedan ne kike wannan haukar Ashe dai Daman can da ciwon rashin tinaninki kikazo,
Uban waye zai mata ciki bayan ASH din dasuke watsewarsu a tare,
yanzu Dan Allah bakiji kunyar tambayar waye yawa yarki ciki ba bayan kina sane da tashin hankalin da Akai a Greece to na uban meye ne idan ba na kwanan datai a dakinsa ba,
Idan ba cikin ba to musulinci taje karba a dakin nasa kenan."

Maamah rasa cewa komai tayi sbd maganganun mum Aisha din bama ta ganesu Sam hakama ita ta yanda Amatun zatai ciki harya fito haka batasan dashi ba shine yake girgizata Yana Neman buga zuciyarta,
Da Abeedan Bata rasu ba kenan haka zasu wayi gari kwatsam suga cikin ASH a jikin ba shiri.
Tayaya Amatu 'yarta data haifa a cikinta zata boye mata irin wannan babban alamarin?
Shin yaushe Amatun ta janye daga gareta haka bayan ko Tari tayi Bata boye mata?
Meyasa ta munafurceta munafurci me girma irin wannan?.

Kasa daukanta qafafunta sukai tana Neman zubewa zaune kan kujeran kusa da ita khaltume ta shigo jiki a sanyaye da abinda yaketa faruwan basuda iKon ko kallawa ta Kalli maamah ta sanar da ita ana nemanta a waje baqi daga kauye sunzo gaisuwa.

Maamah na Jin Hakan gabanta yayi mummunan faduwa idanuwanta suka sake sauyawa zuwa ja ta Kalli khaltume bakinta na Dan nauyi tace

"Daga kauye?

Gyada Kai khaltume tayi tana juyawa ta sauka

Mum Aisha datake a qule kallan Husnah tayi tana cewa

"Wallahi tallahi tsaf zan sanar da ASH komai Babu gargada na abinda kikaiwa matarsa Dan bazaki sakani a masifar da ba hanyar fita ba, ubanwa ya Hana ki auren bare ki dauki cikin Duk da rasuwar mahaifiyarki Baki tuba ba kenan...

Juyawa tayi tana sauka gaba Daya zuciyarta tafasa takeyi shikenan tana murnar ASH Bai ce musu komaiba yanzu mahaukatan gidan sun debo musu sabuwar masifa batama San Ina zata Saka kanta ba da wannan mugun balain matiqar cikin Amatun ya zube.

A palon baqi na ASH dayake harabar gidan aka saukar dasu kawu suna zaune sanyin AC da qamshin arziki duk ya cikasu ga Kuma abubuwan sha duk an Jere musu saisha sukeyi ahankali suna tande Baki cikin sauti mara qara suna jiran fitowansu maamah da Amatun.

Mum Aisha ce ta shigo palon idonta a rufe da bacin Rai me tsanani
Suna ganinta suka ajiye lemukan hannunsu suna kallanta a mutunce cikin girmamawa suka fara gaisawa suna mata gaisuwan rasuwar.

Amsawa tayi tana kokarin fara magana maamah ta shigo itama jiki ba qwari ta zauna tana gaidasu a mutunce da girmamawa tana tambayar mutanen gida tana boyewa tareda danne damuwanta.

Amsawa sukai Baki a washe suna mata gaisuwan rasuwar itama kafin kawu bello yace Ina Amatu itama.

Shiru maamah Tayi,
Itama mum Aisha datazo da niyar miqa qarar maamah din gasu kawun fasa fada Tayi tana jiran amsar da maamah zata bayar.

Jin shiru yasa kawu ashiru Shima sake tambayar Amatu harma da Abdul duk da sunsan Abdulhameed shi Baya qasar Yana gurin karatu.

Shigowan khaltume da wayar mum Aisha dinne a hannu ya Saka mum Aisha kallanta tana kallan wayar Taga Kiran Naufal ne ta karba wayar tana ficewa duk a rude sbd tasan tasu tazo karshe Kila.

Tana fita kawu bello ya tsayar da kallansa da kyau kan maamah Yana cewa

"Asmau matsalan ciwon ji kika samu ne?
Allah sarki to Allah ya Baki Lfy
AmatulMaleek muka ce Ina take ne ita ma mu gaisa".

Dagowa tayi tareda sauke numfashi da ajiyan me zafi ta bude Baki tace

"Amatu Bata Nan sun tafi asibiti"

Dukkaninsu kallanta sukai kawu ashiru ya amsa zancen da cewa

"Asibiti Kuma?
Waye ba lafiya?

Uzaifa ne ya katse kawun da cewa

"Baba Amatun ce fa aka fita da ita muna shigowa ni naso na ganeta gaskia"

Kawu yusufa da sai alokacin ya shiga zancen yace

"Amatun ce ba lafiya kenan?
Allah ya Bata lafiya to yasa dai da sauki"

Suka amsa gaba Daya suna shiga Wani zancen sbd sunso komawa a ranar Amma Nisan basusan yakai haka ba sosai gashi Kuma Basu samu ganin ASH din ba.

Fitowa Akai dasu aka kaisu Daya Daya Dake bq tareda Kai musu lafiyayyan abinci da abubuwan sha aka aje musu kafin su samu ganin ASH din ko yau din ko gobe.
#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

74
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

*************
Asibitin Yana Isa parking yayi tareda fitowa cikin saa Dr beeba na harabar asibitin tana waya shigowarta kenan itama asibiti Bata qarasa shigaba Daman Taga motar gidan ASH din ta farko ta shigo saiga ta biyu kafin ta kashe wayarta saiga ta ukun take ta qaraso gurinsa daidai ya fito da Amatun
da sauri cikin daga murya tafara Kiran nurses suka fito da sauri akai ciki da Amatun.

Emergency dinsu dayake sama aka nufa da ita Kai tsaye aka shiga da ita Dr beeba din na tambayarsa meya sameta Bai iya cewa komaiba bayan ta dubata tareda tabbatarda Babu abinda ya samu cikin jikinta ko yayane su kokarta kawai.

Tabbacin zasu kokarta din ta basa tareda shigewa aka rufo kofar.

Mr Jameel da sauri ya nunawa ASH din gurin zaman Dake gurin Yana komawa mota Dan kawo tissues da wipes da zai goge jinin Daya taba kayansa sosai.

Anty Farha kuwa kanta har Wani sarawa yakeyi tana Jin da tanada Iko Amatu na tashi ba zata koma gidan ba gidanta zata tafi da ita.

Abdulhameed kuwa hannunsa yake Dan girgizawa a wuyansa cikin fargaba da tsoron Wani abu ya samu yar uwarsa ko cikin dayake jikinta.

Haydar har lokacin Bai samu kuzari ko nutsuwan tambayar abinda ya juyar masa da Kai ba kawai lafiyan Amatun yake fata kafin biyowar komai.

Ga Dad dinsa Babu ko fuska data bawa kowa Daman ko kusantosa bare tambaya.

Zaman shiru sukai a gurin harna kusan awa biyu kafin Dr beeba ta fito tana kallan Mr Jameel da anty Farha da suka Dan fara motsawa tukuna ta nufo ASH Dake zaune har lokacin bai iya cewa komaiba bayan idanuwansa da suka qara daukan Jan yanda zuciyarsa ke dauke da zafi me tsanani.

Dan sauke kallanta Dr beeba tayi daga idanuwanta tareda miqawa anty Farha takardar hannunta ta maganin data sauyawa Amatun ta Dan sake kallan ASH Daya dago idanuwansa ya zuba mata tana Neman rudewa sbd shakkar yanayin nasa tace

"Cikin ya Dan zuba ne Amma Allah yasa Bai fadi ba sai Kuma BP nata Da yayi mummunan Hawa sosai Wanda Bai kamata ace me ciki BP dinta Yana kaiwa Hakan ba kusan ma shine ya Sakata sumewa cikin na kokarin fita so,
Amma Inshallah komai is ok yanzu Se a kula sosai please musamman Daya fara zuba cikin komai zai iya faruwa idan aka sake ganganci"

Mr Jameel da anty Farha kusan a tare suka saki ajiyan zuciya a Fili abinda ya danne kirjinsu Yana fadawa,
Abdulhameed ma numfashinsa dayake a rikice ne ya sauka tareda dawowa daidai.

Haydar kuwa sai alokacin hankalinsa ya dawo daidai ya zubawa dukkaninsu idanuwansa tinaninsa na tsayuwa guri Daya shine cikin waye a jikin Amatun?
Yaushe tayi aure?
Dama zata iya aure batareda ya saniba duk tsawon lokacin Nan harma da qaruwar ciki??

Juyawa yayi batareda ya iya cewa komaiba yabar gurin Abdulhameed Daya lura da tafiyarsa juyawa yayi ya bisa jikinsa na sanyi.

ASH kuwa miqewa yayi ahankali daidai lokacinda aka fito da ita aka kaita Wani lafiyayyar dakin da kaman a luxury hotel room kake me nutsuwa.

Gadon da zaa maidata shine da kansa ya Saka hannuwansa biyu cikin kulawa ya dauketa ya kwantar bacci takeyi batama San waye akantaba.

Nurses din na ficewa ya zauna ahankali gefen gadon tareda zubawa cikinta idanuwansa Daya ji suna Neman tara ruwa a cikinsu na abinda yake Gani a gabansa.

Cikinsa ne a jikinta,
Haifar masa 'yaya zatai bayan ya cire Rai daga sake samun wasu yayan,
Duk wannan lokacin Dasuka dauka nesa da juna ciki ne a jikinta batareda ya saniba,
Azabar Daya ringa bawa kansa na rashinta Ashe baida Rabon kulawa da jininsa dayake cikinta ne,
Da mahaukatan gidansa sun Saka cikin ya fita da shikenan yayi rashin tsatsonsa batareda ya San dashi ba ne ko me??
Meyasa farha duk tsawon lokacin Nan Bata sanar dashi Amatun juna biyu ne da ita ba,
Tayaya yarinyar da Bata taba ciki ba zaa barta da dawainiyar renan cikin ita kadai,
Yasan tayi kuka tayi rashin bacci ta shiga tashin hankali da fargabar maamah dinta gameda ciki Amma batada me Bata kariya da kulawa......

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na qara masa ciwon halinda ta shiga batareda saninsaba,
Duk wanna lokacin a cikin qunci sa radadin zuciya yake na rashinta Amma ya zabi hukuntasu su dukan akan lefin mahaukatan gidansa da sunyi Nisan da basa Jin kira.
Chapter 84 · 0% Book details