← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 96

Sashe 27

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakin kawu bello na rawa yayi saurin cewa

"Tabbas mun amince mun bawa duk Wanda kazaba aurenta a daura a yanzu.

Kawu ashiru ma Dayake Jin qamshin kudi aduk lokacinda ASH ya motsa shi kudi kawai yake hangowa da Jin qamshi yace

"Tabbas mun amince har Naufal dinma idan kace shi kakeso mun basa Allah ya Bada zaman lfy da hakuri,zasu daidaita ne daga baya idan sungama rigingimunsu."

Su Auwalu kowa kasa kunne yayi zuciyoyinsu na tsalle,
Faisal kuwa rawa hannuwansa keyi zuciyarsa na bugawa hakama iyayen Naufal.

Boyayyan numfashi me dumi ya sauke batareda yace komaiba ya Ciro wayarsa yayi rubuto ya ajiye.

Minti Daya Bata gama cikewaba saiga AK babban security dinsa Ya shigo da sauri ya wuto har inda ASH din yake ya ajiye masa daurin kudin dasuka Saka kowa hadiye yawu a gurin suna kallan kudin.

Auwalu take yaji shi in kudin zaa bawa Wanda zai hakura to ya hakura ya janye yabarwa 'yan wahala.

Sadi ma Jin yayi yafison kudin akan Amatun,
Uzaifa ne yafara wasi wasin daurin kudin ko Amatu.

Kallansu ASH yayi Dayan bayan da idanuwansa masu kyau da tsari Yana karantar kowannensu da a Fili son kudin ya take Wani maganar auren Amatun batareda sun fada ba.

Wani numfashin ya sake saukewa me zafi a boye tareda rintse idanuwansa a karo na farko dataji krjinsa yayi nauyi da abinda yake Shirin faruwa dashi din ayau Wanda baitaba tinani ko kawo Hakan akansa ba Amma baida zabi ko mafita bayan wannan din sbd kashe matsaloli da fitintinu harna da bawa maamah Mafi girman adalci da halaccin data buqata na tsawon shekarun datai tana kulawa da iyalinsa da Gidansa bisa Amanar da Babu Wanda zai iya masa Hakan.

Kudin ya Kai hannunsa Akai ya dauka ya miqawa kawu bello cikin nutsuwa da Hana kowa fahimtar abinda yake ransa ya Bude Baki Kai tsaye yace

"Ga sadakin AmatulMaleek dinnan a daura mata aure a yanzu"

Hannu biyu kawu yasaka ya karba hannuwan na rawa sosai harsai da kawu ashiru ya Saka hannu ya kama masa sbd kada kudin su zube qasa yanda hannuwansa ke rawa.

Tsit masallacin ya dauka aka rasa Wanda zai motsa bare magana
Su kawu kuwa Babu abinda suka tsaya jiki na rawa suka kalli su me gari da liman suna cewa

Bismillah ranka ya Dade megari da liman ayi haramar daura auren,batareda sun tambaya waye mijin ba.

Sauran jamaar masallacin tini suka fita suka farfadowa mutane aure zaa daura ba Bata lokaci jamaa suka ringa dirarowa masallacin take ya cika anata rarraba idon daurin auren wasu Kuwa ASH TALBA kawai suka ringa zuwa Gani Wanda duk Taron Jamaar gurin har lokacin tirarensa ya doke duka qarfin warin zafin dayake tashi duk da securities sunso Hana kowa shiga masallacin Amma ASH ya Bada damar duk Wanda yazo abarsa ya shiga.

Sbd son zuciya Dana Rai take aka fara kokarin daura auren da Basu San waye mijin ba Saida akazo ambatar sunan mijin Kawu bello ya Fadi sunan da ya Saka duka masallacin daukan shiru tareda shiga mamaki da firgici lokaci daya.

Shi kansa madaurin auren rudewa yaso yi dole aka nutsu aka daura auren da sai bayan da aka daura me sanarwa cikin babban sauti da farin ciki ya sanar da "AN DAURA AUREN MAI GIRMA ASHRAF MUH'D TALBA da ABEEDA AMATULMALEEK SANDA FULDE AKAN SADAKI NAIRA DUBU DARI BIYAR"
##MAMUH#
for more pages join vip or follow me at mamuhgee arewabooks

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

25
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

***************
kawu tsabar farin cikin auren da rawar jiki shi da kawu ashiru rungume juna suka ringa yi sunawa juna barka barka da Arziki.

'Yayansu ma da a take sukasan tinda ASH ya aureta sallamarsu zeyi tini suka hau washe Baki ba baqin cikin komai suna juyewa zuwa yayun amarya Kuma wainda suka hada dangataka yanzu da ASH TALBA suka hau amsa gaisuwar masu Allah ya Sanya alkhairi.

Jamaar masallacin sai murna ake Taya ahalin Sanda Fulde ana Basu hannu suna gaisawa da mutane.

Su kansu iyayen Naufal dole suka tashi suka iso gaban ASH din suka miqa masa hannu cikin tsananin girmamawa suna masa Allah ya Sanya alkhairi da albarka.

Abdulhameed kasa gasgata dauruwar auren yayi da ASH sbd a yanzu bama Faisal dayake gabansaba yajiwa sai Haydar Talba Wanda yasan yanda yafi kusan kowa son Amatun.

Faisal da Daman yasan ASH TALBA bazai taba aura masa Amatu da hannunsa ba sbd magana Daya yake Kuma yayita atin lokacinda aka fasa aurensu farko da Amatun,
Amma Kuma Bai taba tinanin su kawu zasu barwa ASH komai a hannunsaba bare Kuma wannan mamakin na karshe Daya kashesa daga inda yake zaune.

Abdulhameed da Faisal dinne kawai Basu motsa ba kaf masallacin sbd shiga Mafi girman mamaki da tashin hankalin wannan auren.

Kawu Bello ne ya ankare dashi ya Dan waske ya iso inda yake da qafa ya shuresa Yana cewa

"Tashi zakayi ka nuna farin cikinka Koda kuwa bakayin farin cikin Dan kuwa wlh ko uwarku bazata kunce wannan aurenba ya dauru Se lahira tinda muka daurasa"

Kasa magana Abdul yayi sai miqewa tsaye da yayi Baya gane komai ya nufi gaban Dad din ya Dan ranqwafa zaiyi masa Allah ya Sanya alkhairi Amma ya kasa Bude Baki yace komai Saida kawu ashiru dayake kusa ya karbe zancen da cewa

"Abdulhameed Allah dai yayi muku albarka yaji qan mahaifinku Sanyawa wannan auren albarka da tsawon Rai"

Sai alokacin Abdul ya iya Bude Baki ya amsa da Amin Yana tofa tasa adduar shima cikin girmamawa ga Dad Wanda ya amsa Yana miqewa tsaye ya fito masallacin gaba Daya su kawu na biye dashi kowa bakinsa a Bude sai gasar nuna jajayen hakora sukeyi.

Acan cikin gida kuwa Abdulhameed ne yafara shigowa jikinsa na Dan rawa Amma Yana kokarin dannewa da nutsuwa ya qaraso gurinsu maamah wadda tinda ta gama sallah tana kan shimfidar sallan zaune Bata tashi ba, Husnah na gefenta kusan a maqale da jikinta, AmatulMaleek kuwa tana gefe kan shimfidar sallah a lokacin take sallar Azahar din.

Husnah ce ta dago daga jikin Maamah cikin sauri tana kallan Abdul din zuciyarta a qage da son jin idan an daura auren Kuma da waye.

Maamah Bata motsaba bakuma ta tambaya ba Dan kuwa zuwa yanzu ta fadawa Allah,ta sake fadawa Allah Dan haka ta San Allah zai dubi maraicinsu itada yayanta yayiwa Amatun zabi Mafi Alkhairi.

Abdulhameed na zuwa tsayawa yayi daga gefe Yana tauna yanda zai isar musu da wannan sabon lamarin da zai girgiza sauran nutsuwarsu.

Husnah ce ta miqe tsaye tana nufarsa muryarta na Dan rawa idanuwanta na cikowa da hawayen da batasan na Menene ba tace

"An daura auren ne?
Da Faisal aka daura?

Idanuwansa da suka sauya ya zuba mata Dan Jin ita Faisal ne kawai a gabanta ba damuwar kowa ba,
Kan maamah da baisan Yaya zata amshi lamarinba yayi kafin ya Maida kallansa kan Amatu Dake sallah a natse kafin ya Bude Baki zaiyi magana maamah ta dago ta kallesa sbd itama zuwa lokacin amsarsa take Jira hakama wainda suke dakunansu kusa dasu suna jinsu kasa kunnuwan abinda Abdul din zai fada sukai a qage.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda numfashi me dami kafin ya Bude Baki Kai tsaye yace

"An daura Auren.....

Shiru yayi ya sake Dan numfasawa kadan
Zuwa lokacin zuciyar Husnah takusa bugawa har rawa qafafunta keyi sbd son Jin idan Faisal aka daura dashi.

Miqewa maamah tayi ahankali tana kama Husnah da qafafunta ke rawa ta kalli Abdul din zatai magana ya rigata da cewa

"Da Dad dinsu Husnah din aka daur......"

Qarasa zubewa qasa Husnah tayi hawayen datake riqewa idanuwanta suna gangarowa.

Maamah kuwa Bata gama fahimtar wane Dad dinsu Husnah din ba Dan haka ta saki Husnah din tana dagowa idanuwanta jajir akan Abdul tace

"Wane Dad dinsu Husnah din?
ASH??

Gyada kansa yayi ahankali cikin sanyin jiki da damuwa sedai Bai gama jimaminba yaga maamah na Neman zubewa qasa
Kawu Dasuka shigo gidan cikin daga murya da sauri yace

"Karki yarda ki Suma bari a qarasa Miki Dalla Dalla tukuna ki sumen gaba Daya"

Kawu ashiru kuwa Abdul ya hau yiwa fada Yana cewa

"Abin farin ciki kukeson mayarwa na baqin cikin??

AmatulMaleek Dake sallah kasa riqe firgicinta tayi sbd sallarta ta riga ta lalace bayan duhu Babu abinda Idanuwanta ke Gani sai kawai ganin sukai ta silale qasa ita Kam a somen da Husnah da maamah suka kasa qarasawa.

Sakin maamah Abdul yayi yai kan Amatun Yana ambatar sunanta a cikin tsananin kauna da kulawa tareda firgici da tsoron kada Wani abun ya sameta.

Husnah ajiyar zuciya ta ringa jerowa a jejjere kaman me asthma sbd a mummunan bazatar da Bata taba tinanin shiga ba da Jin zancen Dad dinta yayi aure a yau bayan shekarun Daya dauka jiran mum dinta ta tashi
Hakama auren da AmatulMaleek wadda ko Haydar Bata taba hangowa aurenta ba Amma Dad dinsu gaba Daya shine ya aureta.

Maamah ma numfashin take fitarwa zufa na jiqata sosai sbd ciwonta kawai Daya yunquro Yana Neman tashi Dan haka amaryar kawu bello Tayo kanta da sauri tana mata fita taba ambatar sunanta.

Kawu bello Daya ga alamar wankin hula na Neman kaisu nesa batareda sun sanar da ita cikakken bayanin wannan auren duk Wanda yace bayayinsa wlh sedai ya mutu su binnesa Kuma a Dora inda aka tsaya ya Bude murya yanda maamah din zata jisa yafara cewa
Chapter 27 · 0% Book details