← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 96

Sashe 7

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Akai ishai baazo antafi dasu can gurin masu gidan ba sbd umarnin da Abeeda ta bayar na a barsu suyi kwana biyu suci su huta yanda ya kamata kafin su fara Dan zagayawa sbd sam Bata kaunar ganinsu a yanda suke din.

Da daddare maamah barwa Abdulhameed da Amatu gadon tayi sbd baida Wani girman da zai daukesu su uku Dan haka tayi kwanciyarta qasa tabarsu a saman sukai bacci.

Bacci sukai sosai Wanda suka jima Basu irinsa ba sbd samun gurin baccin me nutsuwa ba sauro ba komai Dan haka har Akai asuba Basu saniba Saida gari yayi haske Maamah ta Farka tana tashi zaune kafin ta miqe ta nufi toilet Tayo tsarki da alwala tana fitowa kafin ta tada sallah ta tana Amatu tana Kiran sunanta a nutse.

Cikin baccin dabe saki Amatun ba ta Bude idanuwanta masu Dan girma tana cewa

"Maamah baccin be sakeniba"

"Tashi kiyi sallah Se ki koma tinda Babu aikin da zamuyi anan din."

Sake Dan juyawa tayi tana Bude idanuwanta tareda Kai hannuwanta duka biyu tana ture kafafun Abdul Dake kanta cikin Wani shegen mugun bacci Wanda ko a gida haka suke kafin safe ba qaramin shuri takesha a gurinsa ba sbd Mayen baccinsa.

Saukowa tayi gadon tana murza idanuwanta ta nufi bayin ta shige tana Bude idanuwanta dakyau sbd kada ta zame.

Koda ta fito Maamah tagama sallah tana zaune tana Dan kokarin tada Abdul Shima cikin kulawa da rarrashin ya tashi yayi sallan.

Sallah tayi tana idarwa itama ta zauna gefen maamah din wadda da kanta takai Abdul toilet yayo fitsari da alwala,
Inda ma Allah yayi mata babban rufin asirin dukkaninsu yayan nata Babu me fitsarin kwance da batasan ya zatai ba.

Bayan sun gama sallah Amatu ce ta kwanta qasa Maamah din Kuma da Abdul suka koma kan gadon suka kwanta dukkaninsu baccin ne ya sake daukansu hankali kwance.

Se qarfe Tara aka kawo musu abincin breakfast Wanda Tintini Daman sun tashi har sunyi wanka sbd kada Azo a taddasu da kowacce irin rashin tsafta.

Ayau ma lafiyayyan breakfast suka sake karyawa dashi Wanda kusan iri Daya Dana jiyan ne sedai yau tareda Wani Irin tea me shegen kauri Daya Saka Abdul ringa fadar akwai Madara sosai a cikin shayin.

Haka suka sake wuni guda Babu Wanda yazo ya tafi dasu sedai abincin da aketa kawo musu da lokacin cinsa yayi.

Bata damu da cewa Se sunje gurin Abeeda ba sbd tasan tana sane dasu Kila wata hidimance ta riqeta Batada lokacin ganinsu yanzu.

Abdul kuwa Jin yayi shikam yafara son gidan sbd dadin dasuke ci Kuma basa komai bayan kwanciya da Shan AC Wanda sanyinsa yafara taba Amatu ita Dan Sam Bata son sanyi duk da tana yarinya yanzu ne ze tabata.

****Kwanaki kusan hudu masu kyau aka Basu suka huta yanda ya kamata bayan ci me kyau da sha me kyau Babu abinda suke Samu,
Hatta yar suturar sakawa anbasu dukda ba masu yawa bane Amma sukam a gurinsa me yawan ce,

Abdul sosai a yanzu yaji bayason su koma gida Dan kuwa shi ko wannan ci a koshin da abinci mekyau aka barsa ganin yakeyi duniyarsu ta gyaru Dan haka tini shi Kam ya fara kumatun Kwana biyu,
Amatun ma ta Dan yi kumatun duk da batada jikin kiba ko kadan Amma dai ita cima me kyau da wuri take nunawa,
Maamah kuwa sosai ta dage da kulawa da inda aka ajiyesu din sbd karsu lalata inda aka ajiyesun kafin su tafi hakama duk takai kayan abincinsu kitchen seta Dan taimaka musu da Wani aikin sbd Bata Saba da zama Babu aikin komai ba Jin takeyi duk ba dadi sbd su Basu Saba da Hutu ba da wahala suka Saba.

Ranarda suka cika kwana biyar da zuwa aka Aiko khaltume ta tafi dasu cikin asalin gidan inda masu gidan suke,
Kai tsaye sashen Abeeda aka nufa dasu khaltume na gaba suna biye da ita.

Abdul na hannunsa na riqe cikin na maamah sbd kada yanda yake kalle kalle,
Amatu kuwa tana gefen maamah din itama tana Dan kallan koina.

Babban palon Abeeda ko yau aka nufo dasu suka zauna 'yayanta na gefenta matse da ita suna Dan kallan makekiyar flat screen tv din Dake aiki a palon ba murya sosai.

Abdul sai taba Amatu yakeyi Yana nuna mata abubuwan da duk idanuwansa suka Gani na mamaki ita Kuma tana gyada masa Kai sbd batasan me zata ce masa ba.

Basu Wani jimaba Abeedan ta fito fuskarta dauke da murmushi me yalwa da kulawa tareda kauna a Fili tana kallansu ta qaraso sanye cikin Wani milk dry lace Daya gama bayyanar da kudinsa sbd yanda take a kwance kamar cotton.

Zaunawa tayi idanuwanta dasuka fada suna kan AmatulMaleek wadda gabaki daya Babu abinda ta baro na mahaifiyarta Asmaun sai haske data Fi Asmau Amma komai na maamah dinne.

Manyan idanuwanta farare ta kalla tana mamakin Irin kamannin Asamun da Amatu ta koma sak,
Numfashi ta sauke ahankali tareda sake fadada murmushinta da kulawanta tana miqa hannunta ta Kila Abdul Wanda yake kallanta Amma ya kasa zuwa sai maamah Daya kalla wadda cikin murmurshi ta gyada masa Kai tana cewa

"Jeka ka gaida mommyn UK da kaji Amatu na fada"

Amatu kuwa cikin nutsuwa da girmamawa itama ta Bude Baki ta gaidata cikin Dan sakewan fuska da ganin mommyn.

Amsawa tayi itama tana Jin kaunar yaran tace

"Asmau AmatulMaleek ta fara zama budurwa Ashe,
Allah yasa dai kada iyayen Nan nasu Maza suyi tinanin yimawa auren kauye da wuri sbd bazamu yarda ba Sam da wannan dabiar ta kauye"

Dariya mara sauti maamah tayi tana cewa

"Toh ai sedai ace Allah ya tsare Amma Kam Kila Hakan zaa samu"

Dan kame fuska Abeeda tayi tana sake qarewa Amatun kallo Tana cewa

"Sam wannan bazai yiyuba sbd zasu kashe rayuwarta ne,Ina Sam Sam,wannan ai rashin hankali ne da cutatar da rayuwar Yara qanana sbd wasu shekarun nasu da gaske Basu kaiba."
#MAMUH#
#AMATULMALEEK
#ASH
#ROMANCE
#NAUFAL
#FAMILY
#WEALTH
#LA HOT

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story #

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

7
Maamah kasa cewa komai tayi sbd batasan mema zata ce din ba idan Akan wannan maganar ne Dan kuwa ko ita bazata taba son ayiwa AmatulMaleek auren wuri na kauye ba Amma Babu yanda zatayi idan su kawu suka Yanke mata Hakan.

AmatulMaleek kuwa da Abdul dasuke gurin Basu Wani Maida hankali ga abinda su maaman ke magana akaiba Dan kallo sukeyi,

Ganin Hakan Abeeda takira khaltume ta tafi dasu palon Husnah da Haydar suyi kallon acan.

Bayan antafi dasu AmatulMaleek din zuwa can Abeeda kallan Asmau tayi a natse tana son jin da gaske idan auren kauye din zaawa AmatulMaleek.

Shiru Maamah tayi sbd batasan me zata fada ba Dan kuwa kota Bude Baki ta fada ko kada ta fada Abeeda tasan batada ta cewa akan Hakan,

San numfashi kawai ta sake tana cewa

"Tinda Bata karatu Kam ai auren dole ne da wuri Koda bamuso Hakan ba"

Cikin mamaki da Dan takaici Abeeda tace

"Ke Zaki yarda kenan ayi mata Hakan?
Kuma Asmau me zaisa ki bari 'yarki taqi karatun Boko?
Yanada mahimmanci fa kema kinsan Hakan.

Fada Abeeda ta hau yi sosai Wanda ya Saka maamah yin shiru kanta a qasa batareda tasan me zata ce ba Dan kuwa fada ne Abeedan keyi kamar tanayi da 'qanwarta ko 'yar aikinta.

Abeeda ji tayi duk haushin Asmau ya rufeta Dan haka ma ko firar kirki basuyiba saita damuwa da takaici.

Su Amatu kuwa suna can zaune palon su Husnah duk da Husnah din Bata Nan tana can tareda mum Aisha tin da Akai rasuwar Basu dawoba tkuna Haydar ne kawai anan.

Kallo sukasha sosai hankali kwance sai kusan magrib maamah ta jasu suka koma inda suke wato bangaren masu aiki.

Kwana sukai Abdul na firar abinda suka ringa kalla a TV ita Kuma Maamah cikin damuwa ta kwana sbd Abeeda datai mata fada da maganganu dasuka Saka zuciyarta rauni akan rayuwar datake ciki da 'yayanta.

Amatu kuwa data fahimci damuwa a tareda mahaifiyarta itama sanyi jikinta yayi Dan haka dukansu a sanyaye suka kwana.

Koda gari ya waye maamah data Dan fara sabawa da fitowa Taya masu aiki ayyukansu,fitowa tayi ta nufi dakin khaltume ta kwankwasa mata ta tambayeta idan akwai aikin da zaa Taya dashi.

Ba musu khaltume ta nufi kitchen da ita ta tayasu da aikin fere dankali da doya harma da wasu ayyukan Dan kuwa maamah din tanada nutsuwan aiki da tsaftan Daya sakasu Dan bari tana Saka hannu a aikin.

Dayake kowa ya samu Rana shanya garinsa yakeyi sai gashi cikin kwanaki kalilan masu aikin gidan Kokuma ace khaltume datake babba a cikin ma'aikatan gidan sun mayarda Maamah din kamar me aikinsu Suma kusan duk wasu ayyukan kitchen din Banda girki itace take yi musu,

Ita Kuma Bata taba Jin gazawa ba ko jin an Renata ko wulaqanci ne sbd dadi ma takeji ganin tana yiwa Abeeda da Ash hidima a gidansu da karfinta tinda batada abin biyansu da tarin alkhairansu gurinta Dan haka da zuciya Daya take aikinta.

Abeeda batasan tana aikinba sbd sam Bata zama sosai yanzu da asmaun iyakacinsu suzo su gaidata ta danyi fira sama sama da asmaun su koma.

AmatulMaleek ma data ga dai aikin na gaske ne itama sai tana biyo maamah din kitchen tana kama wasu ayyukan Dan kuwa zuciyarta Bata nutsuwa ganin mahaifiyarta na wahala duk da aikin gidan Sam bama zasu kirasa da aikin wahala ba tinda komai a tsare akeyinsa yanda yake a tsare.

Sunanan Babu cikakken sanin matsayin zamansu Wanda ake nufin jiran dawowar Me gidan sukeyi da mum Aisha maamah tayi musu gaisuwar rasuwar data sakota zuwa Amma ba alamar zasu dawo kusa hakama ita kanta Abeeda tafiya kamata tayi zuwa porthcrt ta kwana biyu Dan haka tana tafiya suka sake zama Wani iri a gidan.
Chapter 7 · 0% Book details