← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 96

Sashe 10

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******Tafiya tafara Nisa sun wayi gari ko suturar sakawa Neman gagararta da yayanta takeyi sun koma inda suka fito ga yunwa da azabar aikin wahala Dan haka ciwo yafara kokarin kwantar da ita.

Amatu data fara iya aikin wahalar sai tana kamawa mahaifiyar tata dasu suna samu suna Dan rufawa Kai asiri.

Duk halinda take ciki Babu Wanda ya taba ko kallanta da daraja a gidan bare a tausayawa rayuwarta a dubi marayun yayanta Dan haka take Dan sake dauriya tana dagewa Dan inganta rayuwar 'yayanta Amma jiki da jini dole Jikin ya fara kasawa sosai harta fara kwanciya ciwo kadan kadan saiga abu na Neman tsanani.

Amatu ce dole tafara fita da kanta Tana debo itace da zogalan da suke dafawa ana siyarwa.

Fara fitan Amatu shine yafi daga hankali da zuciyar maamah ba ciwontaba Dan kuwa tana tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo Bata kaunar abinda zai tana daraja da rayuwar 'yarta,
Tinanin idan ta kwanta jinya me karfi Yaya rayuwar Amatu zata kasance acikin wannan gidan?
Yaya zata iya tsayawa ta taimaka gurin Bata kariya daga sharrin mazan gidan?
Komai zai iya faruwa da Amatu tana daga kwance Babu abinda zata iya yi...

Innalillahi wainna ilaihirrajiun,wannan tinanin kawai ke gigitata hankalinta yayi mummunan tashi harta Saka abin a ranta damuwa tayi mata yawa ciwonta sai qara gaba yakeyi.

Babu abinda yafara zuwa ranta da tinaninta sai komawa Abuja gidan Abeeda sbd Koda Allah yasa ciwonta bana tashi bane tasan tabar yayanta inda zasu tsira da mutunci su kuma su samu kariya da kulawa.

Wanna tinanin nata na sake komawa can din yake sake qarfafa a zuciyarta sbd Daman baaso dawowan nata ba ta dawo Amma Kuma babban abinda yake hanata zama acan din shine tayaya zataje tayi zaman dindindin gidan 'aminiyarta duk da ta Dade da zama 'yar uwarta tamkar jininta.

Wanna tinanin shine yake sake addabarta,takasa tafiya takasa Jin nutsuwar zama Dan haka abin ya taru ya sake mata yawa.

Su Amatu ma gaba Daya a tsorace suke da ciwon maamah din Dan kuwa a yanda suke ganin wainda iyayensu suka rasu a cikin wannan gidan almajirai suke komawa na karfi da yaji hakama lalacewansu yawa takeyi Dan haka tsoro ya kamasu Dan su tsoron ma irin wasu abubuwan Dake faruwa a gidan sukeyi sbd maamah datake Saka musu tsananin tsoron Hakan Tintini.

Rashin takamaimai shawara da madafa yasa suke cikin garari kullum Kuma suna waya sosai da Abeeda a yanzu sbd wayar data dawo da ita wadda aka Siya mata tin acan Amma bata iya fada mata halinda take ciki ba.

****Acikin wannan mummunan halin dasuke ciki kwatsam suka wayi gari da Kiran Husnah a wayar maamah din cewan Abeeda ba lafiya sosai.

Labarin shine Mafi tashin hankalin labarin Daya samu maamah sbd Abeeda Bata taba ciwon da harya kaita kwance ba Dan haka zuciyarta tayi nauyi da tsoron meya samu Abeedan,
duk da ita ma a kwancen take Amma ciwon Abeeda ya sata danne nata azaban ciwon ta fara kokarin Shirin tafiya Dan kuwa ita kanta Abeedan zataso ta farfado Taga Asmau acikin wainda suke zagaye da ita.

Halinda ta shiga na tsananin damuwa da kokarin boye nata ciwon akan son zuwa inda Abeeda da kwana biyu batasan inda kanta yake ba yasa Amatu shiga mummunan damuwa itama da tausayin mahaifiyarta datasan tana cikin nata mawuyacin halin Amma kaunar datakewa Abeeda yasakata dannewa idan ba ganin kanta tayi sun Isa inda Abeedan takeba bazata taba nutsuwa ba.

Acikin kwanaki biyu sukai Shirin tafiya Abuja,
Dayake batada lafiya yanda ya kamata da Kuma kudi da Babu a hannunsu dole tareda kawu bello suka taho har cikin garin Yola suka banki ta basa komai aka ciro kudi daga bankinta ya cire kudin da aka basu aro daga can na tahowa tareda nasa kudin komawar harma Dana Shan ruwa a hanyar komawa tukuna ya rakasu suka hau motar Abuja shikuma ya hau ta komawa kauye.

Koda suka dauki hanyar Abuja a mota shiru Amatu tayi tareda zubawa hanya idanuwanta dasuka fada kwana biyu sosai sbd jinya da kulawa da maamah,

Wannan tafiyar tasu kaman yanda maamah ta fada ba lallai me dawowa bace sbd tanason Koda zata kwanta tabarsu a hannun 'yar uwarta,
Meye makomarsu daga ita har Abdul idan maamah ta tafi kaman yanda take fada?
Daga dangin uwa harna Uba basuda takamaimai inane kaddararsu zata kaisu Dan haka take fata da adduar Allah yabarsu da mahaifiyarsu har girma da tsufa su rayu tare su mutu tare.

Kaman yanda sukasha wahalar hanya wancan Karan wannan ma sunsha sedai wannan da sauki sbd sunsan Daman tafiya ce me Nisa zasuyi ba kaman na farkon ba da basusan Nisan tafiyar ba.

Sai bayan ishai suka sauka Abuja Dan haka Kai tsaye driver ne yazo daukansu harda Husnah wadda itace tazo da driver din sbd ta matsu su maamah din su iso.

Tana ganinsu jikin Maamah ta fada tareda fashewa da kuka sbd tanata Neman Wanda zatai kuka a jikinsa Amma Babu Dan kuwa duk kauna da gatan da mum Aisha ke nuna mata ita Bata Jan Yara a jikinta ga mommynta akwance kwanaki batasan inda kanta yake ba.

Ita kanta maamah Jin tayi idanuwanta na cikowan da hawaye na tsinkewan zuciya Amma hakanan ta daure tana boye nata ciwon suka nufo gida.

Dayake dakinsu na Baya Yana Nan Babu kowa a cikinsa anan suka sauka bayan duk masu aikin gidan sun tarbeta tareda mata sannu da zuwa harma da gyara mata dakinta da wanke toilet da komai.

Basu zaunaba sai da sukaje har palon mum Aisha suka gaisheta tareda mata jajen jikin Abeeda din.

Sama sama ta amsasu tana kallan yanda duk suka sauya ba kamar yanda suka bar Nan din ba musamman Amatu data rame sosai.

Abdul ne ma dai take Dan sakewa Dan haka shi ta ringa tambayar Yaya kauye da karatu Yana amsawa har suka fito suka koma inda suke.

Wanka sukai dukkaninsu suka gasa jikinsu musamman maamah da jikinta yayi nauyi sosai na ciwo da gajiya.

Abinci aka kawo musu Saida sukai salloli suka ci take kowannensu bacci ya kwashesa a qasan tiles din sai maamah suka barwa gadon sbd rashin lafiyanta.

Washe gari Babu tinda Babu abinda sukeyi bayan cin abincinsu da mum Aisha zata asibiti ta tafi da Maamah gurin Abeeda din sbd yanda duk maamah tayi zuru zuru Babu baccin arziki sbd rashin sanin menene yake damu abeedan.

Koda suka Isa babban private asibitin me tsadan gaske suka Isa sama har dakin da Abeedan ke kwance baa Wani shiga sbd baa son motsi me yawa ko karfi.

Ahankali maamah ta iso har bakin gadon Abeedan tana kallanta da idanuwanta dasuka fara cikowa da wasu irin hawaye masu dumin kayewan zuciya na ganin mace kamar Abeeda a kwance gabaki daya kamar ba itaba a cikin qanqani lokaci Allah ya Maida ita Hakan,

Tayi Wani irin haske tayi fayau kamar wadda Babu jini ko kadan a jikinta hakama fatarta kamar wadda aka shafe da yar farar Hoda.

Kasa riqe hawayenta tayi suka fara gangarowa tana Sauke idanuwanta daga kan Abeedan tanajin kaman zuciyarta bazata dauka ba sai kawai ta fashe da Dan kuka mara sauti tana Jin halinda Abeedan ke ciki har cikin zuciyarta.

Ita kanta mum Aisha duk tazo Jin takeyi zuciyarta na karyewa sbd abu ne dayazo lokaci Daya hakama ASH TALBA yakasa fada musu abinda likitoci sukace akanta tin ranarda aka kawota asibiti zuciyarsa ke cikin Wani mummunan hali Amma qarfin halinda yaqi nunawa,

Abeeda wata tsoka ce a zuciyarsa dayakejinta musamman duk da baisan Menene so ba,
Idan Hakan shine so to tabbas Abeeda tagama zama sonsa qwal Daya da bayajin zai samu sassauci akan Hakan.

Kuka sosoi maamah Tasha a asibitin Wanda yasaka nata ciwon datake dannewa tashi sosai sbd Daman ita Kuma matsala ce ta zuciya datake kumbura tsaban kunci da damuwar datake ciki.
#MAMUH#
For more pages follow me @Mamuhgee at arewabooks or join vip

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

10
Badan mum Aisha taso ba dole ta Bada dama likita ya duba maamah a asibitin sai gata itama anbata gadon sbd sosai jikinta ya rikice.

Bayan likita ya gama komai akan mamah din ansamu tayi bacci yayiwa mum Aisha bayanin ciwonta da hutun datake buqata ya tafi.

Babu abinda mum Aisha take tinanin tsayawa tayiwa maamah din Dan haka ta dawo gida saima data huta tayi sallah taci abincin ta Tina da maamah din tasaka khaltume ta hada Amatu dame aiki Daya aka kaisu asibitin gurin maamah.

Amatu karan farko tana ganin halinda mahaifiyarta take ciki Jin tayi komai nata yayi sanyi sbd Koda sukazo tayi Amai Amma Babu kowa adakin bare ya taimaka mata harta koma bacci ahakan.

Share hawayenta dasuka gangaro tayi ta qaraso tafara kokarin tsafatace maamah din batareda wadda aka hadota da ita ta taimaka mata ba duk da qarancin shekarunta ita kadai ta tsafatace mamanta ta gyarata zuwa lokacin jikin maaman ya sake rikicewa Dan kuwa kaman Wanda beso aka zo asibitin ba.

Tsoro dukkaninsu suka shiga sbd Dena numfashin da maamah tayi hakama yanda take fizga tini suka kirawo likita Yana zuwa akace su fita.

Suna fitowa dole Fatima ta tausayawa Amatu itama jikinta yayi sanyi sbd itama marainiya ce tasan suna rasa mamansu a yawon aikatau Kila Suma zasu qare.

Zaman Jira suka dasa a wajen dakin har likita da sauran nurses suka gama duba maamah din suka fito suka wuce Babu Wanda yace musu komai sbd ganin basune sukeda iKon Jin komai ba sai mum Aisha tazo itada ta kawota.

Ciki suka koma suka zauna shiru Babu me magana sai kallan maamah da Amatu keyi a Kai Akai.

Anan Amatu ta kwana tareda Maamah ita kadai sbd ana kawo musu abincin dare aka koma da ita.

Husnah ma taredasu Abdul da Haydar akazo dasu suka duba mommynsu da maamah din suka koma.
Chapter 10 · 0% Book details