← Book details AmatulMaleek Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 96

Sashe 57

AmatulMaleek Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalmominta na karshe ne suka Saka maamah data fara yin sanyi da nasihar Farha din sauya zancen tareda dakatar dashi ta hanyar miqa hannunta ta dafa goshin Amatun daya huce Babu zafi a jikinta sbd alluran datasha da magani a asibiti ta Bude Baki tana cewa

"Allah ya Bata lafiya dai."

Amin"Farha ta amsa dashi lura da maamah Bata son ko zancen auren Amatun da ASH tsaban zuciyarta ta bushe qyam akan auren batada Kuma niyar amsar auren.

Wayoyi anty Farha ta fara cikin nutsuwa da sakewa Wanda aket ayi mata na barkan waliman jiya
Maamah kuwa tana zaune tana kulawa da Amatun duk da bacci takeyi sosai batama San waye akantaba.

*****Qarfe goma sha Daya ya fito shirye tsaf cikin navy blue yadi me tsananin tsadan gaske hannunsa daure da agogon Rotary men's Regent watch qamshinsa na tashi a cikin sanyin fuskansa fresh Wani irin nutsuwa ne ya bayyana a tareda shi duk da Shima a sanyaye yake baa ganewa sbd kasalan daya samu kansa acikinta.

Fitowansa yayi daidai da ihun da Husnah ta buga acikin gidan dukkaninta jikinta na tsananin rawa da farin ciki da rudewa harma da firgicin abinda bata taba tinanin zata ji ba arayuwartaba sbd tashin mahaifiyarta Wani abu ne da kusan kowa ya cire ya debe tsammani idan aka cire Dad dinta da Bai taba cire daga tashin matar tasa ba.

Aunt labiba Dake can qasar ce ta kirata ta sanar da ita wannan labarin Daya firgitata ta saki ihun da batasan tayi ba.

Ganin Dad dinta a gabanta lokacinda y Sako Kai palon nasu Dan isa dakin Amatun ya Sanyata qarasowa gurinsa ko Gani batayi Dan tasan ihunta ya sanyasa shigowa tana tsayuwa gabansa bakinta na rawa duk jikinta ma rawa yakeyi tace

"Dad,mum ta farfado, your wife is out of coma, she's conscious Dad.....

Bata qarasaba kawai ta yanke jiki ta zube a ya tarota jikinsa komai nasa na dakatawa Shima cikin Wani irin mamaki da shock Dan bazai yiyu Hakan ta faru ba ace a bakin Husnah din yake ji ba batareda asibitin sun nemesa ba.

Maamah da Farha ne da ihunta suka fiddosa da gudu suka ganta some a jikin Dad dinta da sauri Maamah ta kamota tana dawo da ita jikin Farha suka kamata zuwa kujera shikuwa juyawa yayi ya fice idanuwansa na sauya batareda kansa ya dauki zancenba tsaban tashin hankalin idan ba Wani ne zai rikita masa qwaqwalwan 'ya ba Amma tayaya matarsa zata Farka bayan shekaru a kwance ace ba shine na farko da zaa sanarwaba.

Mr Jameel Dake jiran saukowarsa a guest Palo Dake gefen security room da sauri ya fito ganin Kiran ASH din akan wayarsa.

Yana fitowa Babu mota Kai tsaye ya Bude masa ya shiga da sauri Shima ya shiga suka kama hanyar office Dan vcall yake buqata da Personal attendant na room din da Abeeda take.

Daga securities har mr Jameel take suka fahimci yau din yanayinsa a bayyane yake na bacin Rai da rashin sanin gaskiyar maganar.

Suna isowa office da sauri mr Jameel yabiyo bayansa cikin office dinsa kafin ASH din ya qara taku biyu cikin sanyi da damuwar jinkirinsa da Dan shakku yace

"Tin dare kanada pending call Daya Greece madame is conscious nayita Kiran.......

Dakatawar da ASH din yayi zuciyarsa na daukewa daga wutan bugawa ya Sanya Mr Jameel din yin shiru Yana qasa da kansa cikin damuwa.

Hannunsa Dake nade da bandage yakai ahankali ya dafa table Dake gabansa Dan jiri da nauyin da zuciyarsa ta Dan dauka da abinda Jameel din ke fada masa yanzu.

Ganin hakan Mr Jameel ya dago cikin son isar da sauran bayanin yace

"Nayi booking komai na tafiya zuwa can din komai a shirye yake ticket kawai za'a Siya"

Rintse idanuwansa da sukai jajir ASH din yayi kusan sanyi da Wani irin nauyi dayaji Yana sauka daga zuciyarsa yaji suna gangara jikinsa.

Qarasa zaunawa yayi Yana Bude laptop din da Mr Jameel yayi saurin kawowa ya ajiye gabansa Kai tsaye yayi Saka Kiran Kai tsaye me zuwa dakin Abeeda.

Mintina kafin Kiran yayi connecting aka basa Daman miqa Kiran zuwa dikinta Kai tsaye.

Abinda ya Gani ne ya sanyashi rintse idanuwansa Wani abu me nauyi da tarwatsewa daga kirjinsa idanuwansa sukai sauya take zuwa ja a Karan farko Dayaji yana kasa riqe yanayinsa na farin ciki da mamakin Daya girgizasa ganin Abeeda idanuwanta a Bude aunt labiba na tareda ita da nurse a dakin duk da kwance take Amma idanuwanta dasuke a Bude Kuma itama shi din Daya bayyana tv Dake dakin take kalla hawaye na gangaro gefen idanuwanta suna saukowa.

"Abeedah" ya furta cikin sautin Daya qarawa hawayenta gudu tana Dan motsawa ahankali.

Motsawanta ya Sanya aunt labiba fashewa da sabon kukan farin ciki shikuma Jin yayi Babu abinda yake buqata a wannan lokacin bayan ganinsa a Greece Dan haka Tim kafin ya dago ya Kalli Mr Jameel dayafi kowa sanin maanar ko motsin ASH da sauri ya juya ya fice Yana Ciro wayarsa daga jikin tsadaddiyar suit dinsa take yakira ya Siya ticket din da zasu Isa Lagos a ayau gobe su wuce.

Madame abeeda kuwa hawayenta ne suke qara gudu ganin fuskar mijinta datafi so fiyeda komai da kowa,
Shine hasken idanuwanta Kuma qarfinta kuzarinta da yayanta Dan haka hawayenta ke qara gudu tanajin tsananin son ganinsa a kusa da ita shi da yayanta.

A nasa bangaren kasa magana yayi bayan sunanta dayake ambata yanajin yau ranar itama ta musamman ce a garesa da rayuwarsa.

Mr Jameel kuwa tini ya fara clearing schedules din ASH din gaba Daya na wannan satin da satin gabansa Dan kuwa a yau zasu wuce Lagos.

A can gida kuwa a lokacinda maamah da anty Farha ke kokarin dawo da Husnah hayyacinta tana Bude idanuwanta abinda ta fara kallan maamah tana furtawa shine

"Maamah mum dina ta farfado,
Mum dina ta tashi,
Mum dina zata dawo gareni ga mijinta Dad dina,
Maamah mum Bata barmu ba ta dawo"

AmatulMaleek data farfado daga nata baccin a lokacin cikin Dan samun karfin jiki da kuzari ta tashi zaune ba zazzabi a jikinta Dan haka wayarta kawai ta miqa hannu ta dauka Dan Neman anty Farha a waya tazo sai alokacin idanuwanta suka sauka kan sakon anty Farha din tin na cikin dare.
#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

50
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER

08142800199
07068558096

****************
Zubawa wayarta Dake hannunta idanuwanta Dake a kumbure tayi ahankali kalmomin Dake rubuce a cikin sakon ma shiga Kai zuwa ciyarta daki daki.

Nauyi idanuwanta suka fara qarawa ahankali tana kokarin ajiye wayar sbd nauyin dataji tana yi mata a hannu batareda ta kira anty Farha din data so Kiran ba.

Kofan bedroom din aka Bude da sauri aka shigo,
Kasa dagowa tayi sbd nauyin da komai yayi mata har ganin nata,

Anty Farha dakatawa tayi tsakiyan dakin tareda zubawa Amatun idanuwanta cikin tsananin tausayi da damuwa ganin halinda take ga wayar a gefen hannunta da alama Kila abinda tazo gogewa da sauri shine Amatun ta riga ta karanta.

Jin shiru ya Sanya Amatun dagowa ahankali tana danne dukkanin abinda take ji na ciwon jiki dana zuci dayake sauka ahankali duk yanda takeson yaqansa Hakan na Neman gagararta ta zubawa anty Farha idanuwanta suna sake sauyawa da dukkanin jarumtarta take danne hawayenta da sedai ganin kallan da anty Farha ke Mata cikin tsananin sanyi da tausayi harma da damuwa ya Sanya hawayenta gangarowa ahankali tana rufe idanuwanta.

Anty Farha da sauri ta qaraso tareda zaunawa gefen gadon tana rungumeta cikin kulawa da kauna me girma tana kasa magana itama.

Runguman da anty Farha tai mata ya Sanyata sakin sauran hawayenta tanajin zuciyarta na nauyi me nauyi sosai Wanda batasan na Menene ba Amma dai tasan tana cikin nauyin kirji da Kuma ciwon da ke damunta.

Ahankali anty Farha ta Bude Baki tana cewa

"Komai ze wuce,komai zai koma kaman baayiba,Zaki warke,Zaki iya fuskantar komai na rayuwa da sauki inshallah"

Batasan me take fahimta ba bayan abinda takeji kawai Dan haka hawaye sosai takeyi tana kokarin bawa kanta qarfin halin danne ciwon jikinta datake ji tareda zafi da radadin inda Akai mata dinki.

Share hawayenta tayi tareda dagowa ta Kalli anty Farha tace toilet zata shiga.

Kamata anty Farha tayi har bakin toilet ta shige ahankali tana tafiya a Dan ware ta rufo kofan.

Anty Farha kuwa fitowa tayi ta wuce maamah da Husnah Dake palon cikin tsananin rudu da farin ciki harma da gargaba da tashin hankalin ta inda maganar auren Nan zata fara bullowa Abeeda.

Qasa anty Farha ta sauka ta nufi kitchen ta samu khaltume na aiki tareda su karima,
Kariman ta kalla tace taje ta gyara dakin Amatun kafin ta fito wanka.

Dawo da kallanta tayi kan khaltume ta fada abinda takeso a dafa mata sharp sharp.

Tea me kauri sosai Wanda Milo yafi yawa ta hadawa Amatun ta wuce sama dashi tana Isa still bedroom din Amatun ta wuce ta shigewarta.

Amatu kuwa a cikin toilet din yakice komai take kokarin yi daga zuciyarsa Wanda shedan yake Neman cusa mata Dan lafiyanta da yanda maamah zata kasa gane halinda take ciki take nema.

Ruwan zafi sosai ta Tara a bathtub ta zare towel din data daura ta fara zira qafarta Daya kafin ta shigar da dayar ta shige ruwan ahankali ta zauna acikinsu.
Chapter 57 · 0% Book details