← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 62

Sashe 8

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yah Mus'af duk bazaku gane ba, baku san irin son da zuciyata takewa Mustapha ba, har a É—azu da safe gani nake kamar ko wanne lokaci zai iya zuwa gareni, amma daga sanda Yah Mas'ud yafaÉ—i maganar nan nasan Musty yariga da yamin nisa koda ayau zai dawo gareni bazan iya auran saba, inna dawo daga school zan kira Abas zan faÉ—a masa na amince dashi yaturo iyayansa"

"A'a karki saurin cewa yaturo iyayansa ku fara fahimtar juna tukun kisan halinsa yasan naki"

"Nariga da na yarda da binciken ka tunda har ka amince dashi nasan halayansa masu kyau ne, bazaka taɓa zaɓan abinda kasan yanada matsala ba"

"Hakane my kanwa zan saka maki credit a wayanki ki kirasa, amasa zafafan kalamai wanda zai sa ya manta hanyar kano"

Dariya Aimanah tayi saboda tina lokacin da tafara soyayya da Mustapha Yah Mus'af ke faÉ—a mata zafafan kalaman da take tura masa duk safiya"To naji zan faÉ—a masa amma ka sake faÉ—an wasu ba irin na Mustapha ba"

"Hhhhhh yarinya nemo da kanki ni zan maki zaman aure ne, nifa zamanki kawai nake a kasar nan daga randa aka É—aura maki aure zan wuce Rasha na cigaba da karatu" Aimanah hawaye tafara sharewa, dariya yayi mata yana tuna mata randa ya tafi A B U zariya yanda ta rinka kuka shima yana tayata, sunata hira har suka karasa ya ajjeta a B U K shi kuma yadawo zuwa Asibitin Aminu kano inda yake aiki.

*ABAS*

Kwance yake a É—aki zuciyarsa fal damuwa gaba É—aya bayajin daÉ—in kwanciyar, agogo ya kalla yaga biyar saura minti biyar 04:55 pm dafe kansa yayi dayaji yasara masa, hannunsa na dafe a kansa yamike yanjin jiri kamar zai faÉ—i, labulan window yaÉ—aga ya kara gudun A c yakoma gefan gado ya zauna yana tina kalaman mahaifiyarsa
"Abas kayi hakuri da yarinyar nan naga kamar ba kaine a agabanta ba kamar tanada wanda takeso a zuciyarta"

"Hajiya bafa kowa a zuciyarta yanzu, kawai wani can banza ne yadasa mata tabo a zuciya wanda yasa takejin haushin maza take ganin kamar duk halinmu É—aya"

"Bazadai ka hakura ba kenan?"

"Hajiya ayi min addu'a kawai Allah yazaɓa alkhairi"

"Amin kagama magana nima inason yarinyar yanayinta yayi min batada hayaniya gata da kunya ba kalar yammatan wannan zamanin bace, duk da na lura gidansu akwai dadtako manyan mutane ne, sun bawa yaransu tarbiya"

"Hakane Hajiya nima abinda na gani kenan shiyasa na nace"

"Saika cigaba da nacin nidai na baka nan da sati guda indai yarinyar nan bata canza ba ka hakura kawai ga Nafisa nan ƴar kanwata kaje kawai ayi yar gida" shiru yayi bayan ya gama tina maganarsu da hajiyarsa, zafi yakeji sosai duk da sanyin A C daya mamaye ɗakin shi gumi yake haka kurum yakejin faɗuwar gaba yau tinda yatashi aduk sanda yatina da Aimanah sai gabansa ya faɗi, bathroom yashiga yayo wanka yafito ya tsaya gaban madubi yana karewa kansa kallo yana neman abinda ya gaza a jikinsa da har Aimanah ta kasa karɓar sa a matsayim masoyi, ba laifi shi ɗin kyakkyawa ne ajin farko irinsu ne ake kira da black beauty, baki ne shi wankan tarwaɗa inji hausawa bakinsa mai kyau ne, yanada tsayi sosan sosai bashida kiba tsayin sa shiya shanye kibar sa, yanada doguwar fuska mai ɗauke da ɗan madaidaicin bakinsa, idanunsa ba farare bane launinsu ya ɗan sirka da ja, kasancewar yanada matsalan ido, sumar kalar ta filani a kallo daya inka masa zakasan sun haɗa jinsi da filani, shafa kwantancan gashi kansa yayi da yasha gyara, ya busa iska a bakinsa ya furzar da iska mai zafi yana jera ajjiyar zuciya, shiri yayi cikin kakin sojoji yai matukar masa kyau ya saka gilashi a idonsa wanda yake kara masa karfin gani, glass ɗin ba karamin kyau yayi masa ba, ya fito daga ɗakinsa hannunsa na rike da hular sojoji, sojoji ne birjik a compound na gidan nasa sun kusa guda goma, da sauri wani yatawo garesa ganin ya nufi mota ya buɗe masa murfin mota, ya kame waje ɗaya tareda sara masa, Abas yai murmushi yasa kafa ya rofe mirfin motar ya buɗe murfin gaban motar ya shiga frot seat, sojan ya maida murfin motar ya rufe ya zagaya da sauri ya shiga drever seat yatada motan, saida suka hau babban titi kana yace
"Oga ina muka nufa?"

"Brecck" Abas yabasa amsa batareda ya kalli inda yake ba yaci gaba da magana "Joshua nasha gaya maka ka daina buÉ—emin bayan mota nafison zama na anan amma bakaji"

"Sir wani iri nakeji idan kana kusa da ni ba girmanka bane zama anan kagi dacewa da bayan ni ina nan ina aikina" murmushi Abas yayi yamaida hankalinsa kan wayarsa sau uku yanayi kamar ya kira Aimanah saiya fasa, yanzuma har ya danna call kiran yafara tafiya yai saurin katsewa saboda yanda gabansa yai wani irin faÉ—uwa, kansa ya kwantar saman seat ya lumshe idanunsa bai buÉ—e ba har suka karasa bareck, yanajin gaisuwa da sojiji ke masa tun daga bakin get bai iya amsa masu sai dai kawai ya É—aga kansa, jin an tsaya yasa ya buÉ—e idanunsa, yana kallo É—aya daga cikin sojojin dake tsaye a wajan ya buÉ—e masa murfin mota ya fito, gaba É—aya sojojin wajan suka kame lokaci É—aya suka haÉ—a baki wajan faÉ—in "Wellcome sir" suma bai iya ce masu komai ba ya É—aga kai kawai da sarsarfa ya shiga office É—in Muhd Ahmad ÆŠan batta ( *SOYAYYA DA ZUMUNTA*) ya iske yana nan aiki ma yake a laptop É—insa, zama yayi a kujera yai shiru yakasa cewa komai, Muhd ya É—ago kai ya kalli Abas, dariya yayi sosai kana ya rufe laptop É—insa ya shiga rera waka "So yakama ni, kauna ta shiga ran wani bai shirya ba"

"Moh Dan Allah kabari bakasan yanda nakeji ba, zuciyata saura kiris ta buga" Moh dariya yaci gaba dayi sosai kana yace

"Mazaje kana bani dariya wai duk sone ya maida ka haka?"

"Moh waike mantawa kayi inace nan kazo kasani a gaba har kuka kamin akan Zuhura sai anyi magana kace tausayinta kakeji ashe taka soyayyar ce tazo harda su kuka akan mace ba gwara ni ba"

"Kaga mufar maganar naji karka ci gaba da kiramin Zuhra anan yanzu na tafi wajanta na manta dakai anan, wai har yanzu yarinyar nan bata canza ba, nifa kawai gani nake ka hakura da ita" kiran sallah akayi gaba É—aya suka mike zuwa masallaci, É—abi'ar su ce komai suke aka kira sallah sukan ajje sa aje ayi sallah in andawo a É—ora.

*AIMANA*
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GMAOuujeP6dLtFTHo1Edxx

🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Bakwai*

Aimanah tana tashi daga makaranta kai tsaye gidan Ana ta wuce, Ana kakarta ce itace wacce ta haifi su Mahh, Ana yaranta biyar uku mata biyu maza Muntari shine babba sai Aisha mah kenan sai Saudat Ammi sai Æ´an biyu Anty Hasana wacce ke aure a Qatar sai Alhaji hussain, Ana da mijinta Alhaji Mahmud suma haifaffun garin É—anbatta ne kauyansu bashida nisa danasu Alhaji farouk mai naira mahaifin Aimanah.

Akofar gidan Anan adaidaita sahu ya ajjeta ta basa É—ari biyar bata tsaya jiran yabata canji ba tayi gaba abinta, da sallama ta shiga gidan, Ana ta washe baki tana faÉ—in "Ga Aimanah ga Aimanah yau agari" Aimanah ta yi murmushi kana ta tsugunna har kasa tana gaida Ana "Nayi fishi Aimanah fisabilillahi kwananki nawa rabonki da gidan nan"Ana tafaÉ—i haka tana kyauda kai gefe

"Ana kiyi hakuri karatu ya rikeni bana samun zuwa ko ina daga gida sai makaranta, yanzuma Mah tace inbiyo tanan intazo saimu wuce tare"

"Allah yataimaka Ummu Aimanah, Aisha basu karaso ba É—azu wannan É—an yakirani yafaÉ—an zasu zo gaba É—aya ko lafiya" Aimana ba tace komai ba tamike ta shige falon Ana

"Wash" Aimanah tafaɗa sanda ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake tsakiyar falon Ana, danna wayarta take jefi jefi suna magana itada Ramla mai aikin Mah wacce ta shigo bayan ta shigo ɗakin ta kawo mata abinci, tana nan zaune har su Mah sukazo kusan tare suka shigo, gaba ɗaya gaidasu tayi tana kallo suka shige can bedroom ɗin Ana, batasan mai suka tattauna ba amma dai tasan koma maine akan Mustapha ne, wanda yanzu takejin matukar tausayin sa, Yau gaba ɗaya ta nemi son Mustapha ta rasa wani tausayinsa takeji, duk cikin sallolinta azahar da la'asar datayi a makaranta gaba ɗaya addu'o'in da tayi rabi Mustapha tayiwa, sosai takejin matukar tausayin halin dayake ciki, haka wani gefe na zuciyanta na matukar tausayawa Abas ganin irin nacin dayake mata, kenan irin yanda takeji a zuciyarta game da Musty haka Abas yakeji akanta, tabbas batayiwa Abas adalci ba yazama dole ta kira yau basai gobe ba ta amince ta soyayyarsa, wayarta ce tayi kara saida gabanta yafaɗi duk a zatonta Abas ne yau gaba ɗaya bai kirata ba tex ɗinma dayake yawan yi mata yau ko ɗaya baiyi mata ba, sanda ta kalli screen na wayar dariya tayi ganin Yah Mus'af ne "Hello yayana" Amainah tafaɗi haka a shagwaɓe bayan ta ɗaga kiran

"Ke ina kikaje?"ba karfe huÉ—u zaku tashi ba yau? yanzu har shida saura minti goma baki dawo gida ba"

"Ina gidan Ana fa Mah ce tagayamin na sauka acan inna dawo" Aimanah ta faÉ—i haka tana turo baki gaba, tanajin sanda ya yi ajjiyar zuciya sannan ya ce

"Mai yasa baki gayamin ba kinsa sai zarya nake daga nan zuwa bakin titi"

"Yi hakuri Yaya mantawa nayi, yanzuma zamu tawo gida" tafaÉ—i haka ganin su Mahh sun fito daga É—akin Ana gaba É—ayansu fuskarsu ba annuri, sosai idanun Ammi sukayi ja alamun taci kuka ta koshi,katse kiran tayi ganin su Ammi sun nufi kofa, gaba É—aya sukayiwa Ana sallama ko wanne ya shiga motarsa yaja, Aimanah tana tsaye jikin motar Mahh tana kallon inda Mah da Ana suke tsaye da alamar wata maganar suke tattaunawa sun jima suna magana kafin sukayi sallama, suka shiga mota zuwa gida.

*Gidan Mustapha*
Chapter 8 · 0% Book details