← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 62

Sashe 60

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Murjana na zaune lafiya itada Alhajinta da yara uku na Kishiyarta da har yau basu san inda take ba, yaran daman ba wani sabawa sukai da Mamansu ba tun suna tambayat tana ina har suka ma daina suka maida Murjana komai nasu itama ta rungume su suka zama tamkar ita ta haifesu, har sannan suna tareda nanny É—insu sai kanwar mahaifiyar Alhaji Jamil É—in da suka É—akko daga kebbi take nan tare da su, duk inda Alhaji Jamil za shi suna tare a nan gida ko a kasar waje, ko kusa batayi saken da zata basa wata dama da zai kula wata mace ba, yau tana kwance a É—aki barci harya fara É—aukarta da gudu Ansar ya shigo É—akin yana tsalle irin nasu na yara
"Momy kizo ga mamanmu tazo tace ki fito" gaban Murjana sai da ya buga kamar bazata fito ba sabida batasan da mai tazo ba sai kuma dai ta kamo hannun Ansar suka fito tare, jefa idanunta ko ina take a kayataccan falon nata tana hangen inda zata ga Maman Jannart muryar Rahila taji daga bayanta
"Sannu Murja sannu da kokarin kula da yara" da sauri Murjana ta zauna nan kasan tiles tana kallon matar da taji muryat Rahila daga bakinta idanu buÉ—e take kallon gurguwar matar da toyayyar fuska
"Wai ina Maman Jannart ne?" Murjana ta faÉ—a tana kallon su Inna Fure da Nanny É—insu Jannart
"Kema baki gane ni ba Murjana, kaico nayi nadama da biyewa gangar sheɗan na taka rawa, Murjana a daran da Alhaji jamil ya sake ni gidan hajiyar nan naje na kwana washe gari muka tafi Kaduna tare da sauran wasu matan mukai hatsari Hanne ta mutu sauran na motar ma sun mutu daga ni sai wata muka rage ita lakarta ta tsinke ni kuma na karye fuskata ta kone Allah yataimake ni ban rasa gani na ba sai kafata ɗaya da aka yanke sabida rashin kulawa ba kuɗin gyaran karayar da nayi kuɗin da aka min aiki ma aka cire kafar sai tallafi asibitin suka nema min da kyar na samu, da aka sallame ni rasa inda zani nayi sai kauyanmu na koma can na samu ɗaki na zauna nake fita bara ina samun kuɗi dana tara su ne na shigo mota yau na zo na ganki na baki amanar yarana na shaida maki nabar maki su duniya da lahira, nasan ni tawa ta kare mutuwa zan ina rokon ki kiyafe min in Abban jannart yadawo kice ya yafe min," ta karasa faɗa cikin kuka, Murjana itama kukan take sosai kenan dai tafiyar Rahila ɗaya da mamansu kaico rayuwa bata masu daɗi ba, sun jima anan falon anata kuka har Rahila ta mike zata tafi, Murjana kuɗi ta bata masu yawan gaske tace mata tasai waya in tana bukatar wani abu ta kirata ko bata zo inda take ba zata saka driver ya kawo mata, Rahila ta kalli Ansar da ya lankwaɓe a jikin Murjana tana murmushi ta ce
"Zo nan Ansari na muyi sallama" sake shigewa jikin Murjana yayi yana kankame ta alamar bazaije wajanta ba,
"Murja ki rike min yaran nan da amana dan Allah ki kula da tarbiyarsu da kawayan da zasuyi mu'amala kawa sharrinta nada yawa ita taja ni ta kaini ga halin da nake ciki, Allah yamaku albarka yarana" tafaÉ—a tana share hawaye, Jannart ta rungume maman tasu tanata kuka dakyar aka rabata da mamanta

AIMANA
Bayan sunyi sallah aka ci abinci, Ammi tuni ta wuce gida tace yara na hanyar dawowa daga makaranta, Mah da Mom hira suke sha sosai kamar daman sun san juna, Yaya Muhd na tareda Ma'aruf da Azinatu suna zagaya gari suna ganin garin kano Azinatu zuwanta na farko kenan garin da taji ya matukar burgeta har tana sha'awar zama a ciki, yan awannin da sukai tareda Ma'aruf ta kamu da matsananciyar kaunarsa, Aimanah ko na tare da Anty Ramla a É—akin Aimanan na yammatanci suna ta hira, har Mistapha ya zo gidan yatafi basu sani ba, yanata leken inda zai ga Aimanah amma bai ga motsinta ba da kunya kuma ya tambayi Mah ina Aimanah, Mus'af daya koma Rasha yau dai sunyi waya da Aimanah yafi sau goma lokaci bayan lokaci yake kiranta yana jin muryarya, bayan mangariba suna nan falo anata hira sai ga Rumana, da gudu Aimanah taje suka rungume juna suka saki kuka lokaci É—aya, Mah na dariya ta ce
"Wai to kukan na me ne kuke yi?" ke Aimanah sake ta baki ga halin da take ciki ba, da sauri Aimanah ta kalli Rumana ta rike baki tana dariya kasa kasa
"Ikon Allah himma bata ga rago sannu maman twince, hala wasu twince É—in kika samo mana" turo baki gaba Rumana tayi ta baje kasan carfet tana maida numfashi, Abbas ne ya shigo yana rike da twince da sauri Mah ta mike ta amshi yaran tana dariya
"Sannu Abbas keta bari da rukon yara, bisimillah zauna" Mah tafaÉ—a tana nuna masa kujera, har kasa ya tsugunna ya gaida su Mah da Mom kana ya zauna inda Mah ta nuna masa ya zauna
"Ya Abbas barka da dare ya hanya ya twince da mamansu" Aimanah ta faÉ—a batare data kalli inda yake ba tasa hannu ta É—auki usaina tana mata wasa
"Masha Allah Rumana mai kike basu haka tubarkallah masha Allah ɓulɓul da su" Aimanah ta faɗa tana ɗaga Usaina sama, Abbas kasa kasa yake jifan Aimanah da wani sassanyan kallo, Rumana na ankare da shi ko kaɗan bataji komai a ranta ba, ita ganau ce ba jiyau ba akan kaunar da Abbas ke wa Aimanah bata wasa bace tasa ni koda yace mata ba Aimanah a zuciyarsa faɗa kawai yayi tasan baikai har zuciyarsa ba
YASAR
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da Takwas*
Chapter 60 · 0% Book details