← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 62

Sashe 11

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

MUSTAPHA
Wata iriyar rayuwa yake shi ɗaya a india ko kaɗan yaki sabawa da mutane ko yaushe yana gidansa idan ba makaranta ya shiga ba to zaka gansa manne da Sumayya wacce akoda yaushe sonta karuwa yake a zyciyarsa da wani irin matsanancin tsoronta dayake ji Yauma kamar kullum dawowarsa kenan daga makaranta yana shigowa gidan yaji kansa ya sara masa, saurin zama yayi a kasa yanajin ɗakin na juya masa....✍🏻
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Tara*

*Assalamu alaikum masoya barkanmu da safiyar Juma'a, rana mai daraja idin musulmi, kar amanta dayiwa Annabimu salati a wannan rana haka ma kar a manta da karatun suratul khafi*

.......Abas agajiye ya sauka a gidansu can jigawa, bai sami Hajiya a gida ba bata nan taje wajan walimar bikin yar kawarta, bazai iya zuwa ya wuce batare daya ga Hajiyansa ba hakan yasa dole ya kwana a can ba damar komawa Abuja a ranar dole sai washe gari, baisami zama da Hajiya ba sai bayan sallar insha a gaba yasata da hirar Aimanah
"Abas ka zurfafa a soyayyar nan fa, ina jiye maka tsoron kazo baka aureta ba"
"Hajiya kima daina faÉ—ar haka dan Allah, daman É—azu wanta yake cemin yakamata na turo manya a tsaida ranar biki"
"Hmm jiya muka gama maganar nan da Alhaji, harma yabawa Alhaji Baita dama shida Alhaji Habu yaje suyi komai tunda baya nan"
"Masha Allah Hajiya naji daÉ—i sai dai banso a saka lokaci mai yawa ni zanso ma asa wata guda, daman karatu ya hana komai kinga kuma yau kwana uku kenan da sukayi gradution"
"Duk bazai gagara ba daga garemu ba wata matsala sai daga su bansan ko sun shirya ba"
"Hajiya sun shirya nifa banason sumin komai zanyi komai da kaina ko ɓangaran Amarya ma Aimanah kurum nakeso kuma ita kaɗai nakeso su kawomin batare da komai ba, ni zan sai komai na gida"
"Hakan yayi Allah yasa yanda kake kaunar yarinyar nan kaima tana sonka haka" dariya kawai Abas yayi yana shafar sumar kansa,sallama yayiwa hajiyar ya wuce É—akinsa yai shirin kwanciya.

*Mas'ud*
.......Gaba É—aya bayajin daÉ—in komai wani iri yakeji idan yaga Abas yazo wajan Aimanah ji yake kamar ya kore sa, haka kurum baisan Aimanah ta auri wani ba Mustapha ba, gaba É—aya ya hana kansa barcin dare raya darare yake yana addu'ar Allah ya dawo da Mustapha hayyacinsa, yau bayan an fito daga masallaci sallar asuba yabi bayan limamin unguwarsu yayi masa bayanin halin da Mustapha ke ciki, Liman yayi jim kana ya ce
"Masa'udu shi wani bin asiri idan anyi wasu binne binne baya sakin mutum har sai anje an tone abubuwan da aka binne, irinshi ne mai wuyar karyewa gashi kace Mustaphan baya kasar nan da sai a haÉ—a masa ruwan addu'a yasha mugani"
"Limana bazaiyu a haÉ—a ba saina kai masa can kasar dayake" Liman yadafa kafaÉ—ar Mas'ud ya ce
"Kayi hakuri kaji kaci gaba da addu'a muma zamu tayaka, idan yadawo kazo ka gayamin akwai abinda zanyi" Mas'ud yayiwa Liman godiya ya wuce gida yanajin zuciyarsa ba daÉ—i, yinin ranar haka yayi sa gashi nan shiba mai lafiya ba shiba mara lafiya ba, har aka tashi daga wajan aikinsu sanyi kalau da shi, ahanyarsa ta komawa gida kawai yasami kansa da canza hanya zuwa gidansu Mustapha bai shiga gidan ba yafaka motarsa a kofar gidan ya kira wayar Surayya kanwar Mustapha karamar Æ´ar Momy, yarinyar slantyly yana hango tahowarta ta gilashin motar sa, yanayin yanda take tafiya a nutse yaji wani abu ya daki zuciyarsa murmushi yayi tareda dukan sitiyarin motar, hannu yasa ya buÉ—e mata murfin motar, bata shiga ba ta É—an durkusa cikin sanyin murya ta ce
"Yayanmu ina yini" haka take gayawa Mustapha shima Mas'ud sau tari hakan take kiransa,
"Lafiya kalau Sury, shigo magana zamuyi"
"Yaya dadai ka fito Ammi ta hanani shiga mota fa"
"Motar samarinki ba, niba saurayinki bane dan Haka ba zance nazo ba" dariya tayi ta shiga motar ta rufe fuskar ta
"Yayanmu ka bani kunya ina naga saurayi ni"
"To bani kunyar tawa na tafi da ita"dariya ta kuma yi tana sake saka hannunta daya sha jan lalle ta rufe fuskarta
"Sury kinsan halin da Musty ke ciki inata ƙoƙarin ganin na fitar dashi amma nakasa yau wani malami yafaɗamin abun da zuciyata takasa nutsuwa" nan yagaya mata yanda sukayi da liman, shiru Sury tayi tana goge hawayan dake zubowa daga idanta
"Nifa ba kuka na kiraki kimin ba" Mas'ud yafaɗa da wata murya da ban wacce shi kansa baisan yanada ita ba😂
"Yayanmu dole nayi kuka, jiya nan fa na shige ta kofar É—akin Amarya naji tana wayada Murjana tana gaya mata ta binne layar nan a kasan murhun mai kosai, kawai jikina yabani kan Yaya ne zasu binne layar" Sury tasake fashewa da kuka
"Sury please stop craying, zakisa zuciyata ta buga fa" da sauri ta É—ago ta kallesa, yai saurin basarwa ya ce
"Yanzu Amarya tana nan?"
"Bata nan ta fita tun safe sai Murjana"
"Yawwa kiramin Murjana nan amshi wannan ki goge face ɗinki, duk kin ɓata kwalliyarki da hawaye sai saurayinki yazo yaga fuskarki a haka yamaki dariya"
"Yaya Nifa Allah vana da saurayi"
"Najib fa?" Saurin amsar hankacif É—in tayi ta fita tana dariya, yaÉ—an jima a motar kamar yatafi jin shiru Murjana vata zo ba, yana kokarin tada motarsa ya hangonta ta fito ko mayafi bata saka ba yana hannunta ta rikesa, kai tsaye ta buÉ—e motar ta shigo bako gaisuwa ta ce
"Surayya tace kana kirana"
"E! dan Allah mai kike so namaki nima inada abinda nakeso kimin" shiru Murjana tayi alamar tana nunani can taÉ—ago ta kallesa
"Kafara faÉ—ar abinda kakeso na maka saina faÉ—i nawa daga baya sabida nawa yanada girman daba lalle ka iyasa ba"
"Nima nawa babba ne"
"Zan maka komai kake so matukar zaka aure ni" dam gaban Mas'ud yafaÉ—i yaÉ—ago ya kalleta ta kashe masa ido É—aya
"Naji zan aure ki indai zaki min abinda nakeso"
"FaÉ—i kawai ko menene zanyi"
"So nake ki rakani inda kuka binne asirin da kuka yiwa Mustapha"
"Waye yafaÉ—a maka wannan maganar?"
"Narida nasan komai wallahi indai aka tone tona rantse maki zan aure ki" Shiru tayi na mintina can ta ce
"Zan tone komai yau da daddare kasani inka yaudare ni komai zai iya faruwa"
"Ba abinda zai faru sai alkhairin aure na dake" fita tayi a motar ta koma cikin gida yana kallo harta shiga gidan yatashi motarsa yanajin nutsuwa a zuciyarsa, Surayya tana gayawa Murjana Mas'ud na kuranta ta wuce É—akin Ammi, Æ´ar É—akin Ammi ce sosai kusan komai nata yana É—akin Ammi, zama tayi saman kujera rufe idonta ta É—ora Hankacif É—in da Mas'ud yabata a fuskarta tana shakar daddaÉ—an kamshin turaran Mas'ud, wani bakon yanayi takeji a zuciyarta gameda Mas'ud
Mas'ud koda dare yayi kasa nutsuwa yayi har saida yakira lambar Surayya wacce har varci yafara É—aukarta cikin mayan barcin tai picking call É—in
"Hello" tafaÉ—a da muryar barci
"HaÉ—ani da Murjana ko ki bani lambarta"
"Bani da lambarta, naga fitarta É—azu wajan tara na dare"
"Ok" kawai yace ya kashe wayar, Ammi dake zaune kusada Surayya ta kalli Surayya ta ce
"Dawa kike waya?"
"Yaya Mas'ud ne Murjana ya ke tambayya" Ammi dafe kirji rayi tareda zaro idanu
"Wayyo ni Saudatu shikenan shima ya shiga komar su wayyo Allah na"
"Ammi vana tunanin wani abu tsakanin Murjana da Mas'ud akwai dai abinda yakawo sa wajanta inaga akan Yayanmu ne" Ammi ta sauke numfashi ta maida kanta ta kwantar jikin filo,Murjana dare tabi ta tone komai batareda Amarya tasani ba saida ta haɗa dukkan abubuwan da suka binne ta kira Mas'ud, yazo ya karɓa cikin dare ya kone gaba ɗaya layun.

Alhaji Habu da abokinsa sukaje suka zo kano aka tsaida auran Abas da Aimanah nan da wata uku...
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Goma*

*Wannan page É—in gaba É—ayansa sadaukarwa ne ga Chamsiyya Louwali Rabo (Mrs Sadauki) Mafiya*

*Mustapha*
Chapter 11 · 0% Book details