← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 62

Sashe 22

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Al'Mustapha yakarasa kusada Sumayya ya zauna nesa da ita kaÉ—an kana ya ce
"Lafiya kike kuka?" É—agowa tayi kallo É—aya ta masa ta sake maida kanta ta kwanntar tareda sake rushewa da sabon kuka
"Ina tambayarki kinmin shuru"
"Murja ce tamin waya ta gayamin an É—aura maka aure da Aimanah"
"Kuma sai tace ki zauna kiyita kuka"
"Dole nayi kuka Musty ni kaÉ—ai a gidanma ban isheka kallo ba inaga ace ga Aimanah a gidan nan nikam nasan tawa ta kare kilama sakina zakayi" ta sakko daga kan gadon ta rarrafo kusa da shi ta rike kafafunsa tana kuka
"Dan Allah Yayanmu dan girman zatin Allah karka sakeni ina sonka wallahi Allah shine shaidata ina sonka ina kaunar zama da kai inka sakeni bansan yanda zanyi ba kilama mutuwa zanyi"
"Ni nace zan sake ne, kinci albarkacin Ammi data hanani sakinki da tuni inma mutuwar zaki tini kina kabari, ki sani ko kaÉ—an bana sonki bana kaunarki dan dole nake buÉ—e idanu nake ganinki a gidan nan, kin ruguzamin duk wani tsarina da burina kin tarwatsa rayuwata, saidai alhamdulillah yau Allah ya maidomin da farin cikina burina tsarina Aimanah alhamdulillah duk wani mai bakin ciki sai dai ya mutu"
"Kayi hakuri sharrin sheÉ—an ne da kuma son zuciyata, nidai na rokeka ka bani dama na gyara kura kuran danayi a baya"
"Allah yasa ki gyaran"
"Insha" tafaÉ—a tana É—ora kanta a saman kafadarsa.

Prop ya kalli yaransa gaba ɗaya dake zaune saman carfet, gefe ɗaya Mah ce da surukanta guda biyu Anty Ummi matar yaya Mansur sai Anty Ruma Matar Yaya Muneer, Zayyad da Zaheed na gefe suna wasa da Noor ɗiyar Yaya Muneer, Aimanah da zazzaɓi ya rufeta na kan kujera ta lulluɓa da hijab ɗinta tana rawar sanyi
"Dadd zazzaɓin nan yayi zafi sosai yakamata a kaita hospital" Mus'af yafaɗa yana taɓa jikin Aimanah
"Yanzu ai ba aikinmu bane wannan Mus'af ka kira Mustapha ka gaya masa" Mus'af ya ɓata rai ya koma ya zauna yana danna wayarsa
"Dad maiya haÉ—a ka Abban Abas tun safe ina cikin damuwa da son sanin abinda ya haÉ—aku" murmushi Daddy yayi yana kallon Ma'aruf dayai masa wannan tambayar
"Bafa wani abu mai zafi bane ya haɗamu, Habu kauyanmu ɗaya dasu babansa manomi ne yayinda mahaifina Baffa yake makiyayi wata rana Baffa ya fita kiro da shanunsa yayi nisa sosai harya kusa isa burtali gajiya ta kama sa ya zauna karkashin bishiya danya huta barci ya kwashe sa kafin yatashi shanunsa sun shiga gonar Iliyasu manomi sun cinye gaba ɗaya shukar datake cikin gonar, hankalin Baffa yatashi sanda ya farka yaga ɓarnar da shanunsa sukayi yakaɗa su zuwa gida da kansa yaje har gida yasami Malam Iliyas yagaya masa ɓarnar da shanunsa sukayi nan fa Iliyas ya rinka masifa yana zage zage har abu yakaisu gaban mai gari, mai gari ya masu sulhu yacewa Malam iliyas ya kirga nawa ya kashe Baffa ya biya, Baffana ya amince zai biya komai amma cikin dare Malam Iliyas ya bankawa turken Baffa wuta shanunsa gaba ɗaya suka kone, sanda Iliyas ya bankawa garkan wuta makocin Baffa harɗo yana kallonsa hakan yasa ya sanar da mai gari ran mai gari ya ɓaci hakan yasa ya kori Iliyas da iyalansa daga kasar sa,"
"Dad aiba Baban Abas bane yakamata yaji haushinmu mune yakamata muji kullacesu danna tabbata ɓarnar da akayiwa Baffa ta wuce ta su"
"Haka ne Ma'aruf saidai shi abinda yasa Habu ya kullacemu sanda aka kore su daga gari sanadin haka ciwo yakama Malam Iliyas na bakin cikin barin garinsa wanda ciwon ne yayi ajalinsa hakanne yasa Habu ya kullacemu"
"Allah ya kyauta" Ma'aruf yace yata shi yabar É—akin
"Mah bani ruwa na sha" Aimanah tafaɗa tana daga kwance, da sauri Mus'af yatashi ya buɗe firij ya ɗakko ruwa mai saukin sanyi ya buɗe murfin goran ya ɗagota ya haɗata da jikinsa yana mata sannu yabata ruwan ta sha, ta koma ta kwanta tana sake lulluɓa da Hijab ɗinta, Mas'ud ya fita daga falon yana danna wayarsa, Mustapha dake kwance saman bed ɗinsa Sumayya na gefansa itama a kwance jin karar wayarsa dake ajje saman bedsate drower takai hannu ta ɗakko wayar ta mika masa
"Lafiya zaka kirani da tsohon daran nan" Musty yafaÉ—a da sigar tsokana
"Kaga nifa ba sa'anka bane yanzu surukinka nake dan haka ka girmama ni"
"Sannu gwambo sarkin son girma"
"Yawwa yanzu dai ga Lailarka ba lafiya Daddy yace kazo ka kaita hospital" da sauri Musty ya mike tsaye ya zari car key É—insa yafice daga É—akin
"Wayyo maiya sami reina da daran nan"
"Ban sani ba" Mas'ud yafaÉ—a tareda katse kiran, Musty sosai yake taka motar yau kam ganin nisan gadon kaya yayi sosai duk da kuwa ba wani nisa tsakanin NNDC kwatas da gadom kaya, saida ya faka motar sa a compound gidan gaba É—aya kunya ta kama sa daya ga kayan dake jikinsa shi kansa saida yayiwa kansa dariya, 3 kwata É—in wando ne ja ajikinsa sai t shart baka wacce ta matukar kama jikinsa, yanzu a haka zan shiga gidan nan, mazewa yayi ya fito daga mota ya shiga babban falon gidan yana sanÉ—a yayi sa'a ba kowa a falon hakan yabasa damar wucewa sashin mazan gidan kai tsaye ya faÉ—a É—akin Mas'ud, É—akin ba kowa shuru buÉ—e closet É—in Mas'ud yayi yafito da wandon juens blue yana kokarin sakawa Mas'ud ya fito daga bathroom tsorata yayi ganin mutum na kokarin saka dogon wando ya juya zai koma bathroom Musty ya gansa dariya nacinsa danya gano tsorata yayi ya ce
"Kai dawo nine fa" ajjiyar zuciya Mas'ud yayi jikinsa duk a sanyaye danba karamin tsorata yayi
"Allah yasakamin dan wallahi ka bani tsoro"
"Kai wai bazaka rage wannan tsoron naka ba, a haka kuma kakeson Surayya cab duk taron matsorata in abin tsoro yazo gidan naku ba wani jarumi kaida ita duk tughether"
"Dallah ajjemin wandona"
"Naki na ajje É—in, zoka ranaki É—akin Aimanah nifa wallahi tsoron rikicinta nake"
"OK gobema idam ankai maka ita tsoron nata zakaci gaba da ji kenan?"
"Gobe kuma haba sai friday goben fa zan koma legos, inna koma zan samo hutun sati É—aya nazo na more amarci na"
"Angonci dai, ba kwaran kawai"
"E naji nine ma kai, yanzu dai rakani dan Allah aboki"
"Kasan Allah bazani ba tana ma sashin daddy"
"Jar uba wai kana nufin can zan shiga a haka da kananun kaya amma ka cuceni da baka gayamin tun farko ba"
"Ni na hanaka ka nutsu kenan ka tuna gidan surukai zaka zo"
"Nidai rakani please"
"Lalle naka wasa ne bari ma kaga na kwanta"
"Dan Allah kataimaka ka rakani fitsarin nan zai zubo tsoro nakeji" gaba É—aya suka tun tsure da dariya harda rungume juna
"Kasan Allah aboki inna tuna rayuwarmu ta booding sainayita dariya ni kaÉ—ai, yanzu dai muje na raka ka aramawa kura aniyarta"
"Allah ya nunamin auranka da Surayya nazauna na bata labarinka da sanda ka shiga firgici sanda kaga aljana" dariya suka kuma yi Musty harda rike cikinsa dan dariya kamar yafaÉ—i
"Allaj sarki Fahad ubangiji yai masa rahama oh rayuwa"
"Ameen" Mas'ud yafaÉ—a dai dai sun shiga falon Daddy,Musty idanunsa akan kujera inda yake zaton Aimanah ce kwance ganin ana rawar sanyi cikin hijab kai tsaye wajan ya nufa bako kunya ko gaida su Daddy baiyi ba ya kalli Mus'af
"Baka kallon rawar da jikinta keyi ka barta haka ba wani taimakon gaggawa"
"Ba ɓangare na bane" Mus'af ya mike yabar falon, Musty buɗe hijab ɗin yayi ya ɗagota ta buɗe idanunta da sukayi ja taga shine komawa tayi ta maida kanta ta kwantar sannan tasa hannunta ta ture hannun Musty dake taɓa jikinta dayaji yai masifar zafi
"Ka shika ni karka sake taɓani" tafaɗa lokacin daya sanya hannu yana kokarin tashinta zaune ɗan matsawa yayi kusada ita sosai bakinsa saman kunnanta ahankali kamar bayason magana ya ce
"Ki tashi na kaiki hospital ko kuma na É—auke ki da kaina ba ruwana da su Daddy suna kallona" da sauri ta mike zaune ta zira plate shoe É—inta dake zube saman carfet ta mike tana kokarin faÉ—uwa yai saurin rukota jikinsa suka fita daga falon
"Mah waisu kaÉ—ai zasu tafi?"
"Ko zaka bisu?" dariya Ma'aruf yayi ya fice daga ɗakin yana masu saida safe, Musty da kansa ya buɗe mata murfin motar ta shiga saida ya gyara mata zaman ta yamaida kofar ya rufe, ya zagaya driver seat, ahankali yake tukun mota yanayi yana kallonta hannunsa na cikin nata, yana kallonta cikeda kulawa, har suka kara wani babban pravite hospital dake zoo raod, lokacin jikinta yayi zafi sosai, yana rikeda ita a jikinsa, cikeda kulawa nurse suka karɓesu kai tsaye gado aka basu sanda Dr ya dubata yacewa Musty damuwa ce kawai sai fever jininta kuma ya hau dole sai an bata gado
Musty ya siyo komai da suke bukata aka saka mata drip tuni barci yayi gaba da ita, Mustapha ya zauna gaban gadon saman farar kujera ya zuba mata idanu yana kallonta, Mas'ud ya kira ya sanar masa an basu gado yafaÉ—awa Mah, Mah ta kira Musty sukayi magana ko Anty Hasana tazo shi yatafi gida yabar Sumayya ita kaÉ—ai, yace basai kowa ya zoba zai zauna zuwa safiya sai Antyn tazo, ajjiyar zuciya ya saki sanda ya ajje wayar shi gaba É—aya ma ya manta da wata Sumayya a gida, yagama duba wayansa yaga ba lambar Sumayyan wayar Shaheed ya kira, Shaheed da baiyi barci ba yana falon Ammi yana kallon wasan kwallo yaga kiran Yayansu
"Hello Yayanmu barka da dar"
"Barka dai Autan Ammi, kaje ka gayawa Sumayya ta rufe ko ina ta kwanta bazan dawo ba ina Hospital Aimah ba lafiya"
"Yayanmu maiya sami Aimah?"
"Fever ne"
"Ok Amma Abba ya rufe gida kasan doka ne, bari na duba in Murjana batayi barci ba saita kira ta a waya ta gaya mata"
"Ok" Musty yafaÉ—a yai saurin katse kiran ganin Aimanah tana motsi
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha bakwai*
Chapter 22 · 0% Book details