← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 62

Sashe 37

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Hmmm Anty Sumayya kenan ke ki godewa ma Allah da wannan É—in ma, kefa kika kawo kanki kika raba masoya Allah yayi kuma da rabon zama a tsakani komai ya rushe daman ai zaki ga abinda yafi haka yayi maki da kauna ma da bai sake ki ba, nifa masifar danake ciki tafi wacce kike ciki cikine dani fa harna tsawon wata uku ban sani ba" karaf maganar a kunnan Mustapha wanda ya shigo basu sani ba, hankali tashe yayi kan Murja da duka bugunta yake ta ko'ina da kafarsa
"Murja mu zaki wulakanta ki tozarta mu kibar mana abin faÉ—a gayamin wane ya maki ciki ki gayamin cikin waye a jikinki" ganin taki magana ya shake mata wuya, idanunta suka firfito waje Sumayya ganin idanun Murja sun canza launi hankalinta ya tashi ta fice daga wajan da gudu ta nufi can cikin gidansu Mustapha, Murjana da taji azabar shaka ta ce
"Na na na Salim ne, salim ne yamin" haÉ—ata yayi da bango ya É—auke fuskarta da marin da azabarsa tasa saida taga wuta
"Waye salim ɗan waye ina ne gidansu zaki magana ko saina zubar maki da hakora" hankali tashe Ammi da yaya Ahmad suka shigo da kyar yah Ahmad ya iya ɓanɓare hannun Mustapha daga jikin murjana
"Mustapha bakada hankali ne mai Murja ta maka har haka dazaka mata irin wannan dukan na fitar hankali"
"Ammi ci ci cikene fa Murja, Murja ta cucemu ta ɓata mana suna" Musty fashewa yayi da kuka kamar wata mace yabar Ammi da Ahmad ba buɗaɗɗan baki, afusace Amarya da dawowarta kenan daga yawonta taga shugowar Sumayya hankali ta she kamar bazata shigo gidan Sumayyan ba sai kuma ta biyo baya taji maike faruwa, ganin Murja zaune kasan tiles tana numfashi ya kuma fusata ta ta karasa gaban Murjan tana tambayarta mai aka mata
"Mama Murja fa cike ne da ita" Sumayya dake can gefe rakaɓe ta faɗa tana kallon maman tasu
"Dan tana da ciki shine mai, a wannan zamanin ai ciki ba wata damuwa bace asibitocin da ake zubad da ciki ai yawa ne da su a garin nan" wasuma watan nin au nawa da aure ko ɓatan wata matansu basu taɓa yi ba shine sabida hassada yata na ɗauke da ciki zaku tara mata mutane, Ammi juyawa tayi tabar gidan ta koma sashinta,
"Amarya kinsan mai kike faÉ—a kuwa yarki ce fa keda cikin shege" Ahmad yafaÉ—a cikeda mamakin maganganun amarya
"Sai me Ahmad, abin kunya ai ba a kanta aka fara ba" Mustapha juyawa yayi ya haye samansa, Ahmad ya fice, Amarya ta ruko Murja suka fita suma, Sumayya kuka ta zauna tayi sosai na bakin cikin abinda yasami yar uwarta, labarin cikin nan dayaje kun nan Alhaji kamal har suma sai da yayi sabida tashin hankali, Murja tarinka kuka kamar ranta zai fita, tun tana basu Mustapha hauci har tadawo tana basu tausayi Alhaji Kamal sanda ya dawo hayya cinsa kasa magana yayi sai hawaye kawai dake bin kuncinsa tsawon lokaci Murja na gabansa tana kuka saida ya É—aga kai ya kalleta kawai, Mustapha dake zaune a wajan tareda Ahmad, Musty yabata umarnin ta fita a É—akin, fita tayi tana waiwayowa tana kallon baban nata
"Abba kayi hakuri mai faruwa ta riga ta faru kasa karka furta kalma mara daÉ—i akanta idan bazaka saka mata albarka ba kayi shuru kar kace komai Abba" Mustapha yafaÉ—i haka jiki a sanyaye
"Sakaci nane Mustapha laifin komai a kaina yake na É—auki kaddara"
"Baba bakada laifin komai kwaÉ—ayinta itada mahaifiyarta shiya jawo komai, ta gaya min duk abinda yafaru dama wanda yamata cikin, zan neme sa muyi magana inyaso inta haihu sai ayi maganar auransu da ita suje su raini yaron"
"Hakan yayi Allah ya sauketa lafiya"
"Amin" suka amsa gaba É—aya, Amarya na zaune a É—akinta gaba É—aya abin duniya ya dameta ko kaÉ—an batai farin ciki da samun cikin nan na murja ba a wannan kadamin data hango wani Alhaji daya mato kan Murja É—in sanda ya ga hotonta a wayarta yace da gaske yana sonta da aure Alhajin É—an siyasa ne, abokin mijin Hanne ne matar ta rasu yanada yara biyar, sosai tayiwa Murja sha'awar auransa musamman ganin yanada kuÉ—i kuma abin hannunsa bai dame saba hannunsa a sake yake,
"Murja cikin nan na waye?"
"Ance min cikin watansa uku a lissafina ciki na Salim ne shine wanda mukai ma'amala watanni uku da suka wuce"
"Kiramin wayarsa muyi magana" kiran wayar tayi Salim ya É—aga bayan sun gaisa da Amarya ta masa bayanin cikin dake jikin Murjana, wata dariya yayi ta shaki yai kana yai fito ya ce
"Mama mama kenan ciki kuma ki tambayeta in zamuyi harka bana bata kwaya tana sha, kwayar hana É—aukar ciki ita kullum nake bata tadai nemi uban É—anta acan bariki badai ni ba" Amarya katse kiran tayi tana kallon Murja
"Kindai ji abinda yace ko"
"Naji daga farkon tarayyarmu inya bani kwayar ina ca amma daga baya sai nake kin sha sai na masa wayo na zubar"
"Yanzu ai kinga wayo, tashi zakiyi muje a zubar da cikin nan bazaki bar min abin kunya ba cikin kishiyoyi"
"Mama zubarwa kuma, dan Allah kibar min cikin nan inason abinda zan haifa na yarda ko katsina ne ki kaini na haihu acan"
"Bazan kaiki ba na rantse da Allah sai kinzo munje an zubar da cikin nan" Murja ba yanda ta iya tabi Amarya suka sami wani asibiti anan aka birge cikin Murja wanda garin haka mahaifarta tasami matsala tanaji tana gani aka cire mata mahaifa yazamo itada haihuwa har abada" kuka take sosai da kuma istigifari tana rokon Allah ya yafe mata zunubanta, sanda Alhaji Kamal yaji labarin anzubar da cikin Murja kuma amarya ce taja nan take ya rubuta mata takardar saki uku yabata yace tabar masa gida bashi ba ita, Murja kuma ya bata sati ɗaya tak ta fito da miji yamata aure ko tabar masa gidansa tabi Amarya, Amarya ko gizo batayi ba dan ita a nata haukan taimakonta yayi yanzu ne zata fantama ta more dasu Hajiya Hanne, kai tsaye ma gidan Hanne ta maida komai nata sashi guda Hanne ta bata aka fara haɗa ta da mata suna holewa........😰
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da shida*

Murjana gaba É—aya duniya tayi mata zafi ta rasa wanda zata kawo har gashi yau saura kwana biyu wa'adin da Abba yabata ya cika, har Salim ta kira kan maganar auran zaki da cin mutumci shiya biyo baya, yau harta kwanta barci ta tina da Alhaji Jamilu da sauri ta cire lambarsa daga black list data saka sa bugun farko yaÉ—aga jiki na rawa ya ce
"Murja nayi kewarki kwana dayawa sau uku ina zuwa kofar gidanku nayita zama amma bana ganin gilmawarki yanzu ina zamu haÉ—u?"
"Alhaji kana sona zaka aure ni?"
"So! sosaima kuwa nake sonki Murja, aure kuma ko yanzu kika ce na fito zanzo ga iyayanki" Numfashi Murja ta sauke kana ta ce
"Ok kazo wajan mahaifina kuyi magana"
"Nayi matukar farin ciki Murja Allah yabamu zaman lafiya amma dai kinsan sai kinyi istibira'i ko"
"Na riga da nayi free"
"Ok ki gayawa Abba gobe zanzo mu gana"
"Allah ya kaimu" tafaÉ—a kana ta kashe wayar ta,

"Aimana yanzu in kika bini yaya zanyi da Sumayya?"
"Ni mai yayi ruwana da wata aba Sumayya ni mafita ta kawai nake nema, inka tafi kabarni yaya zanyi, ina zanji kamshinka nidai Allah binka zanyi" tafaɗa tana dire kafafu irin na shagwaɓaɓɓun yara, dariya yayi yana kallon yanda take kamar wata karamar yarinya, rigima da shagwaɓar Aimanah suna kara narkar da shi a kogin sonta
"Ok dariya ma kake min ko, nidai a zubar da cikin nan tunda ai shine yajamin nakeson kamshin turaranka"
"A'a reina kar ayiwa boy É—ina sharri fisabilillahi kwalba nawa ta turarena na ajje maki amma sai kice ke ba shiba na jikina kike so kawai dai nagano wayon so ake ayita zama a jikina"
"Allah ba haka bane" tafaÉ—a tana faÉ—awa kan gado haÉ—e da fashewa da kuka, zama yayi kusada ita ya É—agota ya haÉ—ata da jikinsa yana kallon fuskarta kana yasa hannu yana goge mata hawaye
"Kinga zaki ɓata min kyakkyawar fuskar nan taki nifa wasa nake maki, tashi ki haɗa kayanki jirgin yamma zamubi motarki da kayan nayi magana da Anty Halima driver ɗinsu zai tafi da su can legos inya kai sai ya biyo jirgi yadawo" tsalle tayi ta ɗane Musty tana ihun murna
"Nikam Aimah zanga randa zaki girma" hara ta masa irinta masoya batace komai ba taci gaba da abinda take, fita yayi zuwa kasa wajan Sumayya
Chapter 37 · 0% Book details