← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 62

Sashe 28

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amarya tashiga ɗakinta bako sallama turus taja ta tsaya tana kallon Murjana dake kwance saman gado kamar mara lafiya cikeda firgici ta karasa gaban gadon tana taɓa jikin Murjana
"Murja mai zan gani duka kwananki nawa da tafiya dubai É—in nan kikace sati biyu zakuyi da Alhajin" Murjana ta fashe da kuka tana bawa Amarya labarin abinda tagani yatashi hankalinta ya hanata barci, tsaki Amarya taja ta zauna gefan gado tana hararar Murjana
"Yanzu sabida É—an wannan abun kika baro Dubai É—in, kai Murja kinyi asara wallahi, tur maye a cikin wannan É—an abu na lokaci ai koni na samu yi zanyi badai za'a bani kuÉ—i ba, kai Allah wadaranki Murja"
"Mama tayaya zan iya aikata wannan babban zunubin, nayi nadamar biyewa Salim danayi ma harya sani aikata zina yake kuma so ya sake jefani a wata masifar Mama na tuba na daina harka da maza aure zanyi"
"Murja aure kuma yanzu? maiye a cikin auran banda tarin damuwa kina dai kallon halin da yar uwarki ke ciki ai garama ki ci duniyarki da tsinke kiga duniya ki wataya, nima yau na haÉ—u da wata hajiya a wajan boka tamin tallan harkarsu ina ganin ciki zan faÉ—a kawai nima nasami kuÉ—i na daina dogaro da abinda Alhaji zai ban daman ai duk gidan nan nice banda abin yi, Ammi na koyarwa a sa'adatu rimi Momy principal É—in makarantar sakandire ce, ni ce ba cas ba ass to nima na sami abin yi in auran zakiyi sai kije kiyi kyaji da abinda kika tarar a gidan mijin"
"Mama karki min baki mana, ke kullum bakinki baya faɗar alkhairi ne, bantaɓa ji haka kurum kin samin albarka ba sai dai in kuɗi na kawo maki ke kawai abaki ki kawai boka kika sani, kina kallo tareda Surayya da Shaheed muka kammala scoundry school a year ɗin Ammi gashi nan tanata fafutukar samawa ɗanta gurbin karatu a malesia Surayya tuni ta fara poly amma ni karatuna baya gabanki kiwai inje inbawa karti kaina su bani kuɗi na kawo maki, ko sau ɗaya baki taɓa yiwa Abba maganar cigaban karatuna ba, haba Mama ke wacce irin uwa ce?" Mama batace mata komai ba ta shige ban ɗakin dake cikin ɗakinta, Murja tabi Maman nata da kallo tanajin inama ba itace ta haigeta ba, nadama ta daɗa shigarta sosai na abinda ta aikata nasoma istigifari tana neman yafiyar ubangiji.

Musty bai wani jima a waje ba yakoma gidansa yatarar Aimanah na barci ya koma falo ya zauna yana kallo duk minti goma saiya leƙa ɗakin da Aimanah ke barci yaga kota tashi, yanzuma lega wan yayi yatarar tashinta kenan tana kokarin sakkowa daga kan gadon, taimka mata yayi ta mike ya haɗata da jikinsa
"Kinsha barci fatan kin tashi lafiya" batace masa komai ba tasake shigewa jikinsa sosai, kwalin waya ya É—akko daga kan madubi ya É—ora mata kan hannunta, rufe ido tayi ta buÉ—e su tarwai kan kwalin wayar da murmushi saman fuskarta
"Iphone wow, masha Allah ina godiya sosai Yah Musty Allah yakara arziki mai albarka"
"Amin" yafaÉ—a yana shafa kwancancan gashin kanta daya sha gyara sai tashin kamshi yake
"Muje falo kisa sim ki haɗa wayan" yana rikeda ita har suka karasa falon ya mata mazauni saman kujera shi kuma ya zauna kasan carfet yana kallonta ta buɗe wayar ta cirota daga kwali farin ciki sosai yagani shimfiɗe kan fuskarta, ya karɓa ya sama mata screen gart da wayar tazo da shi a kwalin ya mika mata ta kunna wayar
"Wow Yah Musty kalli gaskiya wayar nan tayi kyau sosai"
"Nifa banason Sunan nan maye wani yah Musty dan Allah"
"To baby"
"Yawwa na karɓi wanan nice name" rungume Musty tayi ta sumbaci laɓɓansa
"Wow Reina sake sake dan Allah please" Aimanah rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta tana dariya, ya hawo saman kujerar ya haÉ—eta da jikinsa yana sauke numfashi, sun jima rungume da juna, kafin aka fara looking na kofa, ta tashi zataje ta buÉ—e yadawo da ita ya zaunar da ita saman cinyarsa
"Karki buɗe ko waye zai gaji ya koma baza'a ɓatamin wannan yanayin ba"
"Musty zakuzo ku buɗemin ko saina saɓa maku" suka jiyo muryar Anty Hasana tana faɗa, da sauri Musty ya saki Aimanah ya nufi kofa yama magana a hankali
"Kai Anty kin ragemin jin daÉ—i fa Allah yasa Dr yau ya tattaraki ku koma inda kuka fito" buÉ—e kofar yayi ta sakar masa rankwashi a ka tana hararar sa ta wuce sa zuwa ciki, Shaheed da Rumana suka biyo bayanta suna rikeda manyan ledoji a hannunsu
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da É—aya*

Aimanah ta gyara kwanciyarta saman kujera tana kallon Anty Hasana dake mata kallon tausayi
"Sannu Aimanah" kai kurum Aimanah ta É—aga tana kokarin tashi zaune,
"A'a Aimanah basai kin tashi ba yi kwanciyarki ki huta, nima ba zama nazo yi ba zuwa nai namaku sallama Dr ya takura sai mun tafi yau ga Rumana nan, na barta gidan Ana zata kara maku kwana biyu kafin agama mata shirin makaranta ta tafi"
"Anty yanzu tafiya zakiyi?"
"Ya zanyi Aimanah, umarni daga sama, ba yanda zanyi"
"To Anty Allah ya sauke ku lafiya" musty yafaÉ—a yana kallon Antyn
"Daman kai ai so kake na tafi na takura maka ko? toga kanan ga Aimanah nan, Allah yasa nan da wata tara mudawo suna"
"Mom" Rumana tafaÉ—a tana kallon Anty Hasanan
"To uwata hanani magana" ta tashi tana lekawa ko ina na saman tana dubawa kamar yaune zuwanta gidan na farko, ta juya zata fita bayan tabawa su Rumana umarni subar ledojin anan na Aimanah ne, Aimanah ta ruko hannun Rumana ahankali tace
"Rumana inason magana dake fa"
"To Anty gobe zan zo muyi magana" kai kurum Rumana ta É—aga tabi bayan su Anty da Musty da suka sauka kasa, Akasa suka sami Sumayya ta fito daga kicin É—inta batare da Anty Hasana ta tsaya daga tafiyar da take ba takewa Sumayya magana
"Sumayya ga Amarya nan Allah yabaku zaman lafiya sai ayita hakuri mu munkoma inda muka fito" Sumayya batace komai ba tabi Antyn da kallo wacce suka fice tareda Mustapha da alama magana suke mai mihimmanci,
Rayuwa sosai taima Aimanah daɗi a gidan Mustapha sosai yake bata kulawa ko wanne motsinta akan idanunsa kauna tattali da soyayya ba kalar wacce Musty bai bata ba a ƴan kwanakin da sukayi tare, ko ƙasa baya barinta ta sauka da kanta goyata yake a bayanta har kasan, sau biyu idanun Sumayya na gane mata Musty ya goyo Aimanah a bayansa zuwa kasa, takanyi takaici ta shiga damuwa hakan yasa ta nemi izininsa akan tanaso zataje katsina, ba musu ya amince mata, tafiyarta tabasa damar ɓarje amarcinsa son ransa komai tare suke cikin kwanciyar hankali da kaunar juna.

Abas ya kalli hajiyarsa dake kuka sosai ganin yanda Abbas É—inta ya rame ya yi baki sosai dama can shiba fari bane amma bayada duhu kamar yanzun ya wani tara suma kamar wani É—an sudan,
"Abas kaga yanda ka koma?" ashe baka É—auki maganar dana gaya maka ba"
"Hajiyata na É—auka mana naji maganarki zuciyata ce ta kasa jure rashin Aimanah, Hajiya idan na mutu ki gayawa Aimanah ina mata fatan alkhairi, kice nace tabi mijinta su zauna lafiya" Hajiya tasake fashewa da kuka tana rikeda hannun Abas
"Abas ka dai..."Ya isa Baba kayi shuru dan Allah, karka fama inda kemin ciwo, please Baba" Alhaji wada ya goge kwallar data zubo masa yana kallon yaron nasa cikeda nadama
"A'a Abas ka barni nayi magana, kabarni na nemi yafiyarka"
"Yafiyata kuma Baba, ka isa dani ne shiyasa ka yanke hukuncin da kaso, nariga da na É—auki kaddara ko haka bata faru ba daman can Aimanah ba matata bace kamin addu'a nacika da imanai"
"A'a Abas kadaina faÉ—ar haka dan Allah, ka mutu ina zansa kaina yaya zanyi da rayuwata, bazaka mutu ba Abas kai zaka sakani a kabarina insha Allah" likitane ya shigo yana sanye da kakin sojoji ya haÉ—a allura yana kallon Abas ya ce
"Captein zan maka allurar barci"
"A'a Uwaeer karka min allurar nan ka barni na kalli fuskar Hajiyata gani nake kamar yinin yau kaÉ—ai ya ragemin a rayuwar duniya" uweer ya ajje alluran yana kallon Abas
"Captein kadaina faÉ—ar haka cuta ba mutuwa bace anyi nasara jininka ya koma dai dai dan Allah karage damuwa ni dakai duk musulmai ne munyi imani da kaddara mai kyau ko mummuna"
"Nagode Dr, ko nace Captein" dariya Uweer yayi yayiwa su Hajiya sallama ya fita,
Chapter 28 · 0% Book details