← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 62

Sashe 56

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

AIMANA
Sai da tai sati guda bata ko motsi sai yau data cika sati guda sannan ta buÉ—e idanunta, lokacin Mom na É—akin da sauri ta mike ta kira Dr ta cikin telephone É—in dake cikin É—akin nan da nan sai ga Dr da Nurse a tare, Dr yakarasa gaban gadon da Aimanah ke kwance wacce keta dube dube
"Sannu yaya jikin?"
"Da sauki ta faÉ—a a hankali"
"Ya sunanki,kinsan wannan?" Dr ya tambayya yana nuna Hajiya Zainab
"Ban san sunana ba, itama ban santa ba"
"Yasalam" Nurse tace tana komawa gefe ta tsaya, Hajiya Zainab ta share hawaye tana zubawa Aimanah idanu
"Hajiya abinda muke gudu yafaru fa sai dai zamu É—orata akan magani mu gani"
"Yanzu ina ne ke maki ciwo"
"Bako ina" Aimanah ta faÉ—a a hankali
"Hajiya zamu sallame ku ku koma gida sai dai zakuna zuwa ganin likita duk sati, sannan ayi kokari a samo yan uwanta ina zaton in taga wani nata komai nata zai dawo dai dai"
"Insha Allah zamu bincika Dr" Hajiya Zainab ta kira Moha yazo ya É—auke su, Aimanah da idanu kawai take binsu, sosai Mom ke kula da Aimanah gefe guda tana binciken yan uwan Aimanah, wasa wasa Aimanah sai da ta shafe watanni biyu da wani abu tana cikin wannan halin,
Zaman Aimanah a gidan zama ne na gata sosai Mom da Muhd suke kula da ita, a wajan Azinatu kawai take samun damuwa, Aimanah shuru shuru ta koma bata cika son zama cikin mutane ba kusan ko yaushe tana É—aki, cin abinci wanka sallah komai sai Mom tace tayi sannan take, yau gidan antashi sosai da murnar dawowar É—an Hajiya zainab tun safe Ramla dake aure a kaduna tazo, sai É—orawa da saukewa ake
Hajiya Zainab haifaffiyar nan garin Abuja ce, mijinta tuni Allah ya masa rasuwa tana zaune gidanta itada yaranta guda huÉ—u Muhd shine babba sai Yasar Ramla sai auta Azinatu, Ramla an mata aure tuni tana kaduna tareda mijinta Allah bai basu haihuwa ba, Muhd baiyi aure ba andai saka masa rana da yar kanwar babansa, Yasar shekarunsa bakwai kenan rabonsa da nageria yana zaune a madina inda yayi karatu tuni harya fara lacture a jami'atul madina, takurawar da Mom ta masa na rashin zuwa gida yasa zai kawo ziyara ya koma, sai da suka gama komai suka gyara gidan yanata tashin kamshi sannan Muhd ya zo suka tafi airport É—akko sa sabida jirgin da yasar ya biyo na gafda sauka, Ramla Azinatu su suka tafi ba yanda Mom batayi da Aimanah ba wacce suke kira da Aysha ba kan tabi su tace bazata ba hasalima komawa tayi É—aki ta kwanta,
Yasar rungume Muhd da Ramla yayi yana kissin É—insu ta ko ina
"Nayi kewarku sosai, Yaya Moha ka kara girma, Anty Ramla tawa kin kara kiba" dariya duka sukayi banda Azinatu dake can gefe tana taɓe baki, dariya Yasar yayi sanda ya hangi Azinatu
"Autar Mom sarkin rigima haka kika kara tsayi, amma dai taliya Mom ke baki ko"
"Kaifa daman bakinka baya shuru, wuce muje" Moha yafaÉ—a yana rike da jakar kayan Yasar, tunda suka shiga mota bakin Yasar bai yi shuru ba sai surutu yake dan dama shi ba baya ba wajan magana, har suka karasa gida suna yi da Ramla Moha sam baya saka masu baki danshi mutum ne ba mai son magana ba,
"Our wellcome ustaz" Mom tafaÉ—a sanda ta rungume Yasar, Sun batar ta kawai yake ta ko'ina yana rungume da ita
"Mom nayi kewa" yafaÉ—a yana share hawaye
"Nima nayi kewar surutun nan naka, ince dai larabawa basu canza min kai ba"
"Ai wallahi ko kaÉ—an Mom É—anki bai canza ba, tunda fa muka tawo yake surutu shida Ramla, surutu cai cai kamar yaci aku nifa harya samin ciwon kai, Dan Allah Mom kar a ce ya zauna a É—akina kamar yanda muke da, ga É—akin Ramla can ya sauka anan, bazan iya da surutun Yasar ba"
"Caii wai nine mai surutun, Mom inama É—akin Yah Moha É—in yake tabbas can zan sauka yau kwanan hira zamuyi anjima ba'ayi hirar zumunchi ba"
"Mom ina Aysha ne, banga motsinta ba" Moha yafaÉ—a yana kallon kofar É—akin Mom
"Tun bayan fitar ku ta kwanta barci, ke Azinatu taso ta, tazo aci abinci da ita"
"Mom wace Aysha ko anyi bikin Yaya Moha ne banda labari"
"Wata yarinya ce fa Mom ta kaɗe ta wata uku kenan amma an rasa iyayanta take zaune anan" Azinatu ta faɗa tana taɓe baki, hararta Anty Ramla tayi kana ta shiga ɗakin Mom inda Aimanah ke kwance
"Anty Ramla kun dawo?"
"Mundawo Ashanty Mom tace ki fito aci abinci ga Yasar ma yadawo" mikewa Aimanah tayi tana gyara zaman doguwar rigar dake jikinta tabi Ramla suka fito tare, da sauri Yasar ya kalli yarinyar da ta fito tareda Ramla zaro idanu yayi sanda idanunsu suka gauraya dana juna
"Kambu, Mom maza bani ruwan zam zam a jakata" da sauri Aimanah ta juya zata koma ciki, caraf yayi ya ruko hannunta ya zaunar da ita nan saman tiles yana zare idanu,
"Kai É—ago ka kalle ni," yafaÉ—a da karfi yana zare idanu, kai Aimanah ta fara É—agawa,
"Azinatu Ramla kubar falon nan" Yaseer yafaÉ—a cikin bada umarni
"Wai Yasar ban gane ba mai kake wa yarinyar nan haka ne, maca ce fa kake kiranta da kai"
"Zauna Mom da aljani kuke tare, asiri ne a jikin yarinyar nan bani zam zam dan Allah" Sim sim Azinatu tayi ta fice daga gidan gaba É—aya jin an ambaci aljani, Anty Ramla zama tayi tai tagumi tana kallon Aysha dake bubbuga kafa
"Bazaka É—ago ka kalle ni ka gaya min waya turoka ba" nan ma kai Aimanah ta kuma É—agawa kanta na kasa
"Anty bani cup" ta tashi ta É—akko cup É—in a kicin ta dawo ta basa, zam zam É—in hannunsa ya fasa ya tsiyaye a cikin cup É—in ahankali yafara karatu cikin ruwan, tsawon lokaci kana ya kalli Mom
"Mom rike min cup É—in nan ki rike sosai, zan matse bakinta ki zuba mata ki rage min kaÉ—an" Mom tayi yanda yace É—in sauran daya rage ya cewa Ramla zoki shafa mata a jikinta, Ya soma karatun suratul bakara a hankali cikin kira'a mai daÉ—in sauraro
"Wayyo wayyo ku daina zamu fita zamu fita, daman aiko mu akai turomu akai mu shiga jikinta mu É—auke mata tunaninta ta manta komai har zuwa sanda zatayi idda ta zama ba matar Mustapha ba, yau kwana huÉ—u kenan data kammala daman muna shirin tafiya, kana kona mu kana konamu kabari zamu tafi"
"Zaku tafi kamar ya ku zauna, ina mijin nata yana ina"
"Yanzu haka yana wajan aikinsa"
"Mai sukai maku da zaku rana auran sunna"
"turomu akai kishiyarta ce ta turo mu"
"To ku fita kuma ku karya asirin da kukai masu, kuna jina"
"Munji zamuyi yanda kace"
"Nafa sanku bakuda alkawari, in bakuyi abinda nace ba zansa a kawo min ku nan kuna ji"
"Zamuyi komai yanzu ma" shuru Aimanah tayi tareda jero atishawa, can kuma ta buÉ—e idanunta ta mike a guje zata fita, rike ta yayi gam yana kallonta
"Kinga nutsu kina cikin aminci" Wani kuka ta saki tareda kokarin kwace rukon da yayi mata
"Musty ka sake ni barin gidan nan zanyi, kariga da ka yanke igiya É—aya ta auranmu ka sake ni nasamu na fita daga wannan gidan na bala'i"
"Kinga buÉ—e idanu ki kalle mu sosai nan ba gidan ki bane, Mom ta bike ki kusan wata uku kenan" da sauri ta buÉ—e idanunta tana kallonsu É—aya bayan É—aya
"Ya sunanki" Moha ya tambaya a hankali
"Aimanah Farouk mai naira ni haifaffiyar kano c.........nan ta basu labarin ta da abinda ya fito da ita daga gida, Mom sosai ta tausaya mata anan take Aimanah ta bada lambar Ammi aka kirata a waya, Ammi dan Murna ji take kamar ta fasa wayar ta shigo ciki, cewa ma tayi gatanan zata biyo jirgi tazo Abujan, Mom ta hana ta tace su yakamata suzo gobe zasu biyo jirgin safe, Yasar mikewa yayi ya shiga É—akin Moha yayi wanka kana ya fito, kallon Aimanah yayi yana murmushi
"Sannu Ummu ya kike ji, kanki baya ciwo ko" kai ta girgiza alama e
"Ba da kai zaki min magana ba baki zaki buɗe kimin magana ɗago ki kalli idanuna naga wani abu" ɗagowa tayi tana kallonsa da fararan idanuwanta, wani abu yaji ya tokare masa a kirji, ya lumshe idanu yana ambaton Allah a hankali, yana buɗe idonsa sukai ido huɗu da Mom murmushi mom tayi tana bin Yasar ɗin da kallo yanda ya kafe Aimanah da idanu, kallo ɗaya inkayi masa fuskarsa zata fallasa asirin zuciyarsa....✍🏻

07039793439
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da shida*
Chapter 56 · 0% Book details