← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 62

Sashe 23

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saurin kallonta yayi zuciyarsa yaji tazo masa har wuya a fusace ya ce
"Ki sani aurena dake ba saki inkinga na rabu dake to mutuwa nayi, kuma karki sake min irin wannan maganar idan na fusata komai zai iya faruwa inada kishi ki kiyaye yimin maganar wancan sojan" turo baki Aimanah tayi ta juya can taci gaba da barcinta, Mustapha kusan kwanan zaune yayi duk motsinta yana kula da shi har zuwa safiya, Anty Hasana ta fara zuwa tanata mita dan bataji ba tun dare da ita zata zo ta kwana da Aimanah,
"wannan ai rashin kunya ne zaka zo asibiti ka kwana da yarinya kamar batada gata wama yasan iya abinda ka mata Allah yasa ma baka lalube mana Æ´a ba," Musty baice komai ba yana gefe ya danna wayarsa haÉ—eda murmushi Anty tanata mita har Ammi tazo ita tasa Anty Hasana tayi shiru ta tisa keyar Musty yatafi gida yai shirin komawa legos, yana tafe a mota yana murmushi shi kaÉ—ai musamman inya tina mitar Anty Hasana wai ya lalube masu Æ´a, ina shi ina wannan aikin babba, yana shiga gida Sumayya ta taresa tareda tambayarsa ya jikin Aimanan
"Da sauki" kawai yace ya wuce É—akinsa yasa key, wanka yayi ya kwanta ramuwar barci, bai tashi ba har bayan azahar, sallah yayi yai wanka yasa Shaheed yasai masa tiket yai sa'a akwai jirgin dazai tashi zuwa legos karfe bakwai na daren ranar, gidan Anty Halima kai tsaye ya wuce jiya basu haÉ—u ba yanaso su karasa magana ga zancan haÉ—a lefe, yana shiga gidan yaran Anty Halima suka rinka murna ga Uncle Musty, Mustapha na son yara shiyasa ya rungume su yana tambayarsu school, harya zauna saman kujera yana tareda yaran saida Anty tamasu magana sannan suka fita daga É—akin, ya cire hular kansa ya ajje gefe yana kallon Anty ya ce
"Kin korar min yara"
"Inba subar É—akin nan ba bazasu barmu muyi abinda yakawo ka ba gashi kace yau zaka koma legos" Hmm yaja ajjiyar zuciya kana ya ce
"Yau zan koma ya maganarmu ta jiya"
"Narigada nayi masa magana yace anjima zaije ya gano wajan sai asan abinda za'ayi"
"Ok yanzu dai ga ATM card É—ina nan ayi duk abinda yakamata bana son lissafi anyi kaza na kaza kawai ayi komai sannan kuyi magana da Anty Hasana gobe kuje ku haÉ—a lefe, Akaiwa Aimanah, Anty kusai kaya mai kyau da tsada kuÉ—in ciki zai isa komai insha Allah,"
"Bakada damuwa ÆŠan uwa kawai dai kasan Anty Hasana akwai faÉ—a da mita"
"Wai kema tana maki?"
"To Anty wata kyale kowa ma yi masa take" Musty yai dariya kana yace
"Kibita a hankali zaku gama komai lafiya"
"Insha Allah" Anty ta faÉ—a, mikewa yayi sukayi sallama yatafi, asibiti ya wuce yatarar tuni an sallamesu sun koma gida, Anty yakira yana korafin mai yasa ba'a gaya masa ba
"Sannu Mahd ubanmu"
"Nifa Anty ba nan na dosa ba" kashe wayarta tayi bata jira jin mai zai ce ba, Musty yaso yaje gidansu Aimanah amma ya kyale saboda sunyi waya da Ammi take gaya masa gidan akwai mutane dole ya hakura haka yasa kai ya wuce legos batareda yasake ganin Aimanah ba.

Abas wata irin rayuwa yake mai cikeda kunci da damuwa, gaba É—aya bashida kuzari haka yakejinsa kamar wani mara lafiya ga ayyuka da suka saka sa a gaba, yau yana kwance a É—akinsu dake barreck, Sulaiman ya kallesa ganin yanda ya kurawa waje É—aya idanu yayi shuru yana dafe da kansa, Sulaiman dake zukar sigari ya matso kusada Abas ya mika masa sigarin
"Ka karɓi wannan kaɗan zuka aboki, zata rage maka damuwar nan" kai kurum Abas ya girgiza masa alamar bazai sha ba
"Aboki bana son ganinka cikin damuwar nan wai ga manyan babys nan a gari ka tsaya kan wannan yar tatsitsiyar kana ɓatawa kanka lokaci ka shirya a daran yau mu futa club tare, za ka sami wacce zata ɗebe maka kewa ko rumans ku ɗanyi ka rage zafi" Afusace Abas yata shi tsaye yana huci ya nuna Sulaiman
"Ki fita sabgata Suleman dole sai nayi rayuwa irin ta ka ne?"danna shiga damuwa saina jefa kaina a bala'i da fishin ubangiji lokacin inada kuruciya ban nemi mata ba, ban sha sigari ba bare yanzu da shekaru na suka haura arba'in, a yanzu fatana da buri na mutuwa a ko yaushe, nifa musulmi ne na yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau, domuwar nan da nake ciki jiki da zuciya ne suka kasa sabawa da rashin Aimanah amma na yarda da kaddara daman banada rabon aurenta, inada kur'ani shine yake mantar dani duk wata damuwa, taba sigari ko wata mace tayi kaɗan ta ɗeban kewar Aimanah" fuuu ya fuce daga ɗakin a fusace, Sulaiman taɓe baki yayi ya koma inda Abas yata shi ya kwanta.

Murjana tana tsaye gaban closet tana zuba kayanta cikin babbar trolly, da sallama Sumayya ta shigo É—akin ta zauna gefan bed tana kallon Murjana data zama wata katuwa tayi fari É—au da alama mai tafara shafawa sabida da ba haka take ba baka ce ba can ba bakinta mai kyau ne
"Wai lafiya yaya kika zuba min idanu haka?"
"Gani nayi kin zama wata hajiya ga uban fari da kikayi nidai Allah yasa ba blecing kika fara ba" Murjana tayi far da idanu tai juyi ta ce
"Ai ina gaya maki kuÉ—i duniya ne, kinga kuÉ—in danake kamawa kuwa ai Salim ya kyauta min da ya nunamin wannan harkar yanzuma wani Alhaji zanyiwa rakiya Dubai"
"Murjana wai bakiji maganar dana gaya maki ba ran nan, Murja wannan rayuwa bata da tabbas dan Allah kibar wannan harkar ta É—aukar zunubi"
"Nifa inada mijina a hannu kuma shiya nunamin har kar nan ke karshe shiya haÉ—ani da wannan alhajin yace namasa rakiya Dubai" Sumayya tagumi taja tana kallon Murja, Amarya ta shigo É—akin ba ko sallama tasami gefen Sumayya ta zauna tana aika mata da harara,
"Murja ga wannan boka tsito yace a zubawa Alhaji a abinci zai manta dake indai yaci abincin bazai sake tunawa da ke ba sai randa ya ganki" tsalle Murja tayi ta É—ane Amarya tana murna
"Sai dake Mama ina alfahari dake uwata maganin kuka na"
"Mama yanzu dan Allah kema biyewa Murjana kike keda yakamata ki gaya mata gaskiyya haba dan Allah karuwanci fa kenan kika É—aurewa Murja kugu tayi a cikin gidanmu"
"Gidansu dai, ke kunada gida ne, indai namiji ne gaki nan ga shi nan, badai kince ke kin daina asiri ba karya ne gashi nan ai kin fara gani kina zaune a gidan zaki zama bora, maza Murjana ta shi kije ga Alhajin can ya aiko a ɗauke ki naga irin motar jiya ta paka a kofar gida" Murja ta saɓa jaka a kafaɗarta tasa kai zata fita Amarya ta ce
"Yawwa murja nace dan Allah karki manta da abayar nan dana nuna maki irinta babar Salim"
"Bakida damuwa Mama zan siyo maki wacce tafi tatan tsada" Sumayya ta kalli Amarya ranta ɓace
"Mama maice kuma abaya dan Allah Abba fa yana matukar bakin kokarinsa mai kika nema kika rasa na sittura zaki wane ce a siyo maki Abaya ayau kika gayawa Abba kinason Abaya saiya baki kuÉ—i kin siya"
"Ke! zoki fita daga nan kibar min gida na"
"Mama nifa gaskiyya nake faÉ—a maki"
"Sumayya koki fita daga ɗakin nan kona saɓa maki" Sumayya ta fita zuwa ɗakin Ammi suka gaisa sun jima suna hira tana bawa Sumayya hakuri kan auran da Mustapha yayi batareda sanin ta ba ta gaya mata yanda abin yafaru, ta bata shawarar yanda zata zauna da mijinta da kuma abokiyar zamanta Aimanah.
Chapter 23 · 0% Book details