← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 62

Sashe 35

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abbas zaune cikin office É—insa dake cikin barreck É—insu wayarsa yake kallo ganin kiran Rumana sam yakasa É—aga kiran matukar tausayin yarinyar yake dan daga alamu ta kamu sosai da sonsa, shi har yanzu bazaice yana sonta ba haka bazaice baya sonta ba, shi yanzuma ba wata soyayya a gabansa auran nan zaiyi ne kawai sabida girma da mutumcin Aimanah dayake gani banda haka bayajin nan duniya zai aure yana kallo kiran ya katse bai É—aga ba, bai kuma bi kiran ba har tsawon mintina yana jiran ko zata sake kira amma ba ta sake ba, jiki a sanyaye ya É—auki wayar tasa yabi kiran Rumana wacce yai save da Wife
"Barka da yamma sojana"
"Barka dai Wife yakike ya gida ya shirye shiryen biki"
"Gashi nan munata yi, daman Yaya Aimanah tace nakira ka naji mai zamuyi na shagalin biki?"
"Rumy banda cikakkiyar lafiya, bazan iya halartar ko wanne event ba kuyi ku kaÉ—ai kawai"
"Kana nufin baza kazo ko É—aya daga ciki ba?"
"Bazan sami zuwa ba Rumy"
"Shikenan nagode na kuma fasa auran tunda so kake ka nunawa duniya ba sona kake ba" katse kiran tayi, mikewa tsaye yayi yana zagaye a É—akin kiran Ruma yasakeyi amma bata É—aga ba daya takura da kira ma saita kashe wayar gaba É—aya Tex ya mata ya ajje wayar
Rumana ranta ɓace ta kalli Aimanah
"Na rantse da Allah yaya bazan auri Abbas ba, nizai wulakanta nifa daman bawani sonsa nake ba, biyayya kawai nakeson yi maki",
"Rumana kiyi hakuri zaku sasanta kuma zai zo duk wani event da zamuyi na maki wannan alkawarin" Rumana ta matso kusada Aimanah ta saka hannunta cikin Aimanah
"Yaya bazan ɓoye maki ba inason Abbas tun kallon farko dana masa ranar bikin uncle Yunus na kamu da sonsa, yanda bikinku ya kasance yasa nafara mafarkin auran Abbas, sanda kika zo min da rokonki kan na aure sa nayi farin ciki sosai, sai dai daga baya na fara tunanin nakai kaina inda zan wulakanta bana gaban Abbas ko kaɗan, yau yadaɗa tabbatar min da haka"
"Rumana na rantse maki zaki alfahari da auran Abbas, ki daure komai zai faru a yanzu daga kin shiga ne komai zai wuce kefa maca ce" Da kyar Aimanah ta lalaɓa Rumana ta yadda suka cigaba da shirye shiryan bikin, Daddy da Mah sune sukayiwa Rumana komai na kayan ɗaki a jigawa gidansu Abbas akayi mata jere, sosai aka sha shagalin biki dinner kawai akayi Abbas ma ya halarta washe gari aka ɗaura aure Anty Hasana bata zo ba can a Qatar tayi taronta itada Dr shiyasa Daddy shine komai shiya ɗaura mata aure karfe biyu aka tafi da Amarya Daddy yace karsu sake su kwana suna kai Amarya su juyo, har Aimanah akaje jigawa bayan sun sha rigima da Mistapha yace bazataje ba ta ce sai taje rigima sosai sukayi har gaban Ammi goyan baya tabawa Aimanah ba yanda musty yayi yanaji yana gani haka aka tafi jigawa da Aimanah, hannu biyu Hajiya Hafsatu ta karɓi su Mah abinci kala kala aka kawo masu saida sukayi sallar Insha suka baro jigawa Rumana nata kuka, har Abbas ya shigo tana zaune saman bed tana kuka...✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da biyar*

Abbas ya tsaya a kanta yama rasa mai zaice mata can dai ya zauna kan gadon yasa hannu ya buÉ—e mayafin data rufe fuskarta da shi, ido huÉ—u sukayi da sauri Abbas ya É—auke ganinsa kana ahankali ya ce
"Kiyi shuru Rumy ki daina kukan nan yana tadan hankali" Ai kamar wanda yace cigaba da kuka ta kuma rushewa da kuka
"Kinga tashi kiyo alwala muyi sallah mu godewa Allah daya mana wannan ni'imar mu rokesa yabamu zaman lafiya da fahimtar juna mai ɗorewa da zuri'a ɗayyi ba" bata masa musu ba ta mike tashiga ban ɗakin dake cikin ɗakin tayo alwala ta fito, yana tsaye kan daddumar daya shimfiɗa binsa tayi sukai sallah raka'a biyu sosai yamasu addu'a kana ya fita zuwa kichin yadawo rike da plate da ya ajje a gabanta kallo ɗaya tayiwa plate ɗin ta kauda idanunta kaza ce dataji kayan haɗi sai tururi take da tashin kamshi, lemu ya zuba a cup ya mika mata karɓa tayi ba musu ta sha kaɗan, ahankali yake bata zallar tsokar naman kazan tana taunawa kamar mai cin magani bata wani ci dayawa ba ta ce
"Na koshi" kallonta yayi da murmushi a fuskar sa
"Baza dai kici dayawa ba sabida tsoro ko" dariya tayi ta mike ta koma gefan bed ta zauna, tana kallonsa yagama kwashe komai yamaida kicin yadawo sanye da farar jallabiya ya kwanta É—an nesa da inda take kwance, baice mata kala ba haka itama batace masa ba, har barci yayi awon gaba da su, da asuba ita ta rigasa farkawa mamaki tayi ganinta a jikinsa ya zagaye ta da hannayansa ta shiga jikinsa sosai, hannunta tasa tana kokarin cire hannunsa daga jikinta taji yayi motsi, a kunnan ta yake magana a hankali
"Asuba tayi ne?" bata iya magana ba sai kanta data É—aga alamar e, tashi yayi zaune kafin ya sakko kasa ya mika mata hannu ta É—ora nata saman nashi ya mikar da ita, tare suka shiga bayi sukai alwala ya wuce masallaci ita kuma ta tada sallah anan É—akinta saman dadduma, Abbas bai dawo É—akin ba sai bayan bakwai na safe ya tarar Rumana harta koma barci nan saman daddumar É—aukarta yayi ya maida ta kan gado, ta buÉ—e idanunta dasuka soma canza kala ta kallesa kana tace masa
"Ina kwana"
"Kin tashi lafiya ya kwanan bakunta" dariya tayi haÉ—eda runtse idanunta ganin ya cire jallabiyan jikinsa ya rage daga shi sai gajeran wando da farar singleti gadon yahawo yajawo ta jikinsa, bikinsa ya haÉ—e da nata yana aika mata da wasu sakonni masu wuyar É—auka, safiyar wannan rana Abbas yamaida Rumana cikakkiyar mace, yasha kuka yakushi harda cizo, barci ne yayi gaba da ita, shi kuma ya mike ya shiga bayi ya tsarkake jikinsa yai wanka ya fita sai faman murmushi yake shi kaÉ—ai, sashin hajiya ya shiga har bedeoom É—inta ya tarar bata É—akin ya shiga É—akin Babansa inda yake zaton tana can nan ma É—akin ba kowa, motsin daya jiyo a kicin yasa ya leka, Hajiyarsa ce tsaye tana aiki a kicin É—in, babansa kuma na tsaye jikin gaban teble yana gyara attaruhu, dariyar dayayi yasa suka jiyo gaba É—aya suna kallonsa baba ma dariyar yayi ya ce
"Kamin dariya mana, fisabilillahi da girmana da shekaru na akawo ni kicin asani gyara attaruhu wai lalle sai anyiwa surukata girki harda ni" Abbas dariya yayi sosai harda rike ciki yana kallon hajiyarsa data sha mur, ya karasa gaban Babansa ya karɓi wukar hannunsa
"Abbas fita ka koma É—aki kayi barcinka barsa Allah dashi za'ayi girkin nan,"
"Hajiya da dai kun barshi basai ayo order ba da safan nan ki wahalar min da Baba" hajiya batace komai ba taci gaba da abinda take, Haka Babanma Abbas ya gaida su ya fita yana dariya, sanda ya koma É—akin Rumana na zaune kan gado farkawarta kenan daga barci gaba É—aya jikinta ciwo yake mata musamman ma kasanta wani raÉ—aÉ—in azaba take ji ko motsi ta kasa, kallo É—aya ya mata ya shiga bathroom ya haÉ—a ruwa mai É—umi yadawo cak yaÉ—auketa daga gadon bai direta ko ina ba sai cikin ruwan daya haÉ—a, wata karar azaba ta saki tana kokarin fitowa daga cikin ruwan
"A'a Hubbi daure ki zauna zaki daina jin zafin yi hakuri kinji" yafaÉ—a a tausashe kamar mai shirin mata kuka
"A'a Kalbie bazan iya ba zafi nakeji wayyo Allah Anty zan mutu" hannunsa duka biyun yasa ya riketa ganin tana kokarin futowa daga cikin ruwan, bai saketa ba saida ya tabbatar ruwan ya yi sanyi kana ya fito da ita daga ruwan yace
"Yi wanka" juyawa yayi ya fita daga bathroom É—in ya koma É—aki ya zauna haÉ—e da yin tagumi, ya zubawa kofar bathroom É—in idanun yana jiyo zubar ruwan datake wanka,
kulawa ta musamman Abbas ke bawa Rumana satinsu ɗaya a jigawa suka koma Abuja, saiga Rumana a gidan Abbas gidan daya gama tsara yanda zaiyi rayuwa da Aimana, gaba ɗaya ya manta da Aimanah yanda yakejin Rumana yanzu bazaice ta wuce Aimanah a zuciyarsa ba amma kam sosai yakejinta a zuciya musamman yanda take da biyayya bata taɓa masa musu ba iya tsawon zamansu, tana da tsafta batada son jiki ga iya girki da kwalliya.
Chapter 35 · 0% Book details