Sashe 39
Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Hankali tashe likitoci suka karɓi Rumana akai emargency da ita, tsananin tashin hankalin da Abbas ke ciki yasa ko gabansa baya iya gani, Jakop ya taimaka masa ya zauna a recepsion yadafa kansa yayinda shi Jakop ɗin ke zarya tsakanin inda Abbas yake da inda aka kwantar da Rumana
"Ina yan uwan Rumana Mahmud" da sauri Abbas ya mike tsaye yabi likitan zuwa office É—insa, kujera ya nunawa Abbas dake tsaye kikam a kansa, ba musu ya zauna zuciyarsa na dukan uku uku
"Sorry matarka tayi ɓarin cikin wata biyu" a razane ya ɗago idanunsa yana kallon likitan, hawaye suka zubo daga idanunsa shikenan sun rasa wannan cikin da suka kwallafa rai a kansa, ya Hajiya zataji idan taji wannan labarin mai tada hankali
"Kayi hakuri mahaifar Rumana nada rauni koda ta sake samun wani cikin banajin zai zauna sai dai zamu É—orata kan magani sannan zata cigaba da zuwa ganin likita duk bayan sati biyu" Abbas kansa kawai ya É—aga alamar yaji, Dr ya mika masa takarda ya ce
"Ga wannan asiyo waɗan nan magungunan da allurai" karɓa Abbas yayi ya fita, Jakop yabawa takardar shi kuma ya shiga ɗakin da aka kai Rumana, tana kwance samɓal saman gado kamar gawa ko motsi batayi a kallo ɗaya daya mata yaga ta rame sosai kamar wacce ta shekara tana cuta, hawayan idanunsa ya share ya sumbaci kuncinta ya fita daga ɗakin, recepsion ya koma ya kira wayar hajiyarsa bugu ɗaya a na biyu ta ɗaga
"Soja mazan fama barka da yamma ya surukata"
"Hajiya" zuciyarsa ce tai wani irin rauni ya na shashshekar kuka ya ce
"Rumy tayi ɓari"
"Æari! innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu tana ina?"
"Muna hospital"
"Kamata sannu zan biyo jirgi na tawo na kula da ita"
"Hajiya basai kinzo ba zan kula da komai"
"Malam Abbas kabari kawai nazo, kaga yanayin aikin ka yanzu ma ana iya kiranka batada kowa a Abuja wazai zauna da ita kabarni kawai nazo"
"Shikenan Hajiya Allah yakawo ki lafiya" Abbaa komawa É—akin yayi yaja kujera ya zauna kusada gadon hannunta na cikin nasa, motsi tafara yi kana ta buÉ—e idanunta, lemar dataji a kasanta yasa ta kankame hannun Abbas dake cikin nata
"Hayatie maiya same ni mai ya sami cikina?"
"Ba abinda ya sameki Rumy kina lafiya, haka cikin ki ma yana lafiya"
"A'a Hayatie ka faÉ—a min gaskiyya jini ne fa yake bina"
"Kinyi ɓari ne" Abbas yafaɗa a sanyaye
"Cikina ta zube wayyo Allah na"
"Kiyi hakuri Rumy kwana nawa ne zamu sami wani dan Allah karki saka damuwa a ranki Allah shiya bamu wannan lokacin da bamu zata ba ko tsammani, shi zai kuma bamu wani kilama ki mana tagwaye" yakarasa faÉ—a yana murmushin karfin hali, Rumana maida kanta tayi ta kwantar haÉ—eda runtse idanu hawaye na zubowa daga idanunta, Hajiyar Abbas a ranar tazo ita taci gaba da kulawa da Rumana.
*Musty Home*