Sashe 7
Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi zama tayi saman kujera tana goge hawayan dayake fitowa daga idanunta Saheed É—anta na uku daya ji komai saboda yana falon Ammin yana kallon kwallo, kashe kallon yayi yadawo kusa da mahaifiyarsa yana goge mata hawayan dayake zubowa daga idanunta, tsabar takaici takasa magana wani abu ya tokare mata a kahon zuci, shigowar Ahmad É—anta na biyu wanda suke matukar kama shida Mustapha ganinsa yasa tafashe da kuka, da sauri ya karaso inda take ya zauna a kasa ya kifa kansa saman kafafunta ji yake kamar shima ya fashe da kukan yanzu Surayya takirasa ta gaya masa abinda Abba yayi a gidan, Shaheed ya É—ora kansa saman kafaÉ—ar Ammi yana tayata kuka, jin kukan da Saheed yake yasa ta katse nata kukan tasoma ajjiyar zuciya a jere a jere, idanunta ta rufe
"Shaheed yi shiru daina kukan nan bakai yakamata kayi kuka ba ni ce zanyi kuka an cuce ni, ana kuma ganin laifi na, ni Alhaji ke gayawa magana duk hakurin danayi bai gani ba, gobe zan bar gidan nan ku maza ne ba mata bazan iya zaman hakuri ba, Ahmad kayi aure kabar cikin gidan nan kafin wata masifar ta ritsa da kai zanso ka auri Aimanah hakan zai faranta raina, Shaheed zan tattara kuÉ—aÉ—e na nasama maka makaranta a malesia ko thailand katafi can kayi nisa da gidan nan kaima"
"Ammi munyi maganar nan dake tun kwanaki bazan iya auran Aimanah ba bazan so abinda É—an uwa na ke so ba koda Yaya Musty baya raye bazan iya auran Aimanah ba, bare yana raye wani abu ne ya gifta yasa ba'ayi auran suba, har yanzu ina addu'a Allah ya warware kullin da akayi Yah Musty yadawo hankalinsa ayi auransa da Aimanah"
"Ammi niki nema min auran Aimanah zan aure ta" Shaheed yafaÉ—i haka hankalinsa kwance, Ammi da Ahamad tare sukayi dariya kafin Ahamad yace
"Ina kaga an taɓa haka Aimanah ta girmeka nesa ba kusa ba kai ba sa'an auranta bane yaushe ka gama scoundry ita ko datake fenal year a jami'a"
"Yah Ahamad ai ba haramun bane basai mu tafi malesia tare ba nifa dama can ina yin Yaya Aimanah kawai dai matsalar banida aikinyi" Ammi dariya ta kuma yi tareda shafa kan Shaheed tana murmushi.
*Aimanah*
Agajiye ta tashi daga barci sauri sauri ta shiga bathroom tayi wanka cream kawai ta murza a jikinta ta fesa turare kan doguwar abayar data saka ta fito, kamar yanda tayi zato hakan ce ta tabbata gaba É—aya mutanan gidan na bisa danning ana breakfast wajan Daddy ta soma zuwa hannunta tasa ta rungomo Daddy ta baya ta kwantar da kanta saman kafaÉ—arsa tana kallon fuskarsa tace
"Goodmorning Dad"
"Morning my lovely Douther ya kike hope kin tashi lafiya"
"Lafiya kalau na tashi Dad" wajan Daddy ta bari ta nufi Mahh dake cin abincinta kai bazaka kace tana kallon suba saboda gaba É—aya hankalinta yana kan abincin datake ci
"Kinga basai kin zo ba sarki son jiki ni karki zo ki wani makalƙaleni kamar wata mage, ja kujera kici abinci malama" Aimanah ta ɓata fuska ta tsaya inda take tana kallon Yah Ma'aruf dake mata dariya
"Kaga Yaya kadaina min dariya"
"Ni kuma Allah ma yasa abinci na nake ci bana kallonki" Ma'aruf yafaÉ—i haka ganin irin kallon da Mus'af ke aika masa shiyasa yai saurin waskewa, Mus'af mikewa yayi daga kujerar dayake kai yazo inda Aimanah ke tsaye ya haÉ—a ta da jikinsa kaÉ—an ya ruko hannunta har gaban teble yaja mata kujera ta zauna ya zuba mata fankaso cikin plate kana ya zuba mata miyar agushi data sha wadataccan naman rago a bowl ya mika mata gabanta "Maza cinye min wannan na ajjeki a makaranta"
"Yah wannan fa yamin yawa" tafaɗa ranta ɓace tana cuno baki gaba
"Ok karki cinye baki shirya siyan mota a wannan watan ba kenan" da sauri Aimanah tafara cin abincin tana dariya
"Na shirya fa yaya Dan Allah camry nakeso"
"Bakida damuwa nagama haÉ—a kuÉ—ina cash Mahh kawai nakeso ta amince banida damuwa da Daddy yardar Mah nasan itace tasa"
"Haka mukayi dakai" Daddy yafaÉ—a yana dariya,Ma'aruf yace
"Daddy kowa fa yasani agidan nan Mah itace batason mu huta" dariya a kayi gaba É—aya banda Mas'ud daya kasa cin abincin gabansa yayi shiru kamar mara lafiya...âœðŸ»
07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
â˜€ï¸ *First Class Writer Asso*☀ï¸
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
Shafi na Shida
Wanan shafin gaba ɗayan sa sadaukarwa ne ga masoyan wannan book ɗin musamman ƴan zauran Mami Yusuf Daboo🥰
Mah ta ajje cokalin hannunta tana kallo Mas'ud da damuwa ta bayyana karara a fuskar sa, sosai tabada hankalinta wajansa, musamman ganin yanda tai magana baiji ba hakan yatashi hankalinta sanin halin Mas'ud mutum ne mai faran faran kusan duk cikin yaran yafisu fara'a da surutu ga kirki da son mutane, ba kasafai ta fiya ganinsa a irin wannan yanayin ba, da Mus'af ne sam batada damuwa dashi saboda shi halinsa ne ciccin magani da miskilancin rashin magana da kin mutane,
"Ma'aruf taɓamin na kusa dakai koya kurum ce ne ina magana baiji ba" Ma'aruf yasa hannu yataɓa Mas'ud, Mas'ud jin an taɓa sa yasa ya tsorata yaɗago a firgice, tsam Maah tamike daga inda take ta karasa ta tsaya a kansa cikin kulawa tasoma taɓa jikinsa taji ko zazzaɓi ne ajikinsa tasan rago ne shi, idan zazzaɓi yakamasa baya masa ta daɗi, jikin taji sanyi kalau ba alamar zafi,alamun kalau yake damuwa ce kawai
"Sarkin maka lafiyarka kalau kuwa?"
"Mah ba kalau ba" Mas'ud yabata amsa batareda yaÉ—ago ya kalleta ba
"Taso mu shuga ciki muyi magana"
"Maganar bata sirri bace Mah ayita nan kusan ta shafi kowa dake nan akan Mustapha ne?" Mah takoma wajanta ta zauna tana kallon Mas'ud tace
"Kai nake sauraro sarkin maka" murmushi yayi ba karamin daÉ—i yakeji ba idan Mah ta kirasa da sunan nan, "Mah Mustapha na cikin masifa! jiya nakirasa..."kaf ya kwashe yanda sukayi da Mustapha ya gayawa Mah, gaba É—aya Mah hankalinta yatashi tarinka ambatan "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu har masaifar takai haka na shiga uku ni Aisha" Mah wayarta ta É—auka ta wuce É—akinta, prop bayanta yabi, sam ko kaÉ—an Alhaji Faruok Mai naira baya kaunar ganin gudaliyar matarsa cikin matsala, Mah wayar Ammi takira Ammi na ganin kiran ta É—aga da sauri dan tana cikin damuwa takira wayar yayar tata yafi a kirga amma saita jita a kashe
"Mah ina cikin masifa abubuwa sun run caɓe yaya zanyi?"
"Kiyi hakuri Saudat bansan abin yakai haka ba kwanan nan kinsan haÉ—uwa tayi mana wuya sanda zaki tashi a aiki ni kuma sannan zan tafi nawa, jiya nake cewa inna koma aikin safe nan gidanki zan wuto inna tashi,yanzu kuma Mas'ud yagayamin abinda yatashi hankalina"
"Ki bari Maaa wallahi yaron nan yana cikin jarabawa Allah ya fiddasa daga wannan masifar da haushin sa nakeji yanzu kuwa tausayin sa nake ji"
"Ba komai Ammi komai zai wuce yazama tarihi insha Allah yanzu mu haÉ—u gida anjima zanyiwa su Yaya Muntari magana, mu haÉ—e gidan Ana zan kira Alhaji usaini ma, sannan karki kuskura ki gayawa Hasana komai kin santa da masifa yanzu ta baro Qatar tazo tayi ta bala'i da mutane"
"Bazan gaya mata ba jiyama munyi waya tana tambayata Mustaphan nace mata baya nageria ya koma jordan,wallahi Maaah nakasa aikata komai a makarantar nan jiya na gayawa yara zamuyi test yau amma nakasa shiga class"
"Yi hakuri daure kiyi komai yanda kika saba khairan insha Allah" Maah data gama waya ta kalli prop dake zaune gefan gadonta yayi lamo kamar wani karamin yaro
"Lafiya na ganka a wannan yanayin prop"
"Lafiya kalau kawai banji daÉ—in labarin nan danaji daga bakin Mas'ud ba," "Mata masifa ne! ni daman tun farko matar nan ta Alhaji Kamal batamin ba kawai dan ya nace ne na gaya masa yaki ji, dayabi tani bazai aure ta ba"
"Ya za'ayi prop haka Allah ya tsara matar sace kaga harda Æ´a a tsakani ai dole ayi aure, ni da cewa nayi zan aiki Mas'ud wajan yaya liman can kauye koda abinda za'ayiwa Mustapha"
"E kiyi hakan jiya ma gwaggo ta kirani bikin jikarta nan da sati biyu"
"Allah yakaimu, Aimanah naji tana maganar zuwa kauye sai tayi shirin zuwa biki nikam banajin zanje, satin ne bikin Raudah".
Ainamah shirye cikin shirinta na tafiya makaranta tayi sallama a É—akin Mah ta nemi izinin shiga maa tayi mata izini sannan ta shiga, sallama tayiwa Maaa da Daddy ta fito, ta tarar har Yah Mus'af yafitar da motarsa wajen gidan, a can tasame sa ta shiga yatashi motar suka soma tafiya, Aimanah wayarta take dannawa Yah Mus'af yakira sunanta ganin yanda ya kira sunan nata ya tabbatar mata da magana zai mata mai mahimmanci hakan yasa ta saka wayarta cikin hand bag É—inta ta É—ago tana kallonsa
"Aimanah bani aron hankalinki" sake nutsuwa tayi tana cigaba da kallon sa shi kuma hankalinsa na bisa titi "Aimanah Abas yana matukar sonki, naga ke kuma hankalinki baya kansa, nakasa gane inda kika nufa, inma har yanzu Mustapha ne a ranki to kiyi gaggawar shire sa sabida ko yau Mustapha yadawo hayyacinsa yazo bazan taɓa amincewa da auranku ba saboda wahala zaki sha zama da irin mutane su Amarya ba abu bane mai sauki indai akace maki abu akwai asiri ka nisanci abin nan duk tsananin son da kakewa abin, koda kin auri Mustapha bazasu taɓa bari kiji daɗin gidan auranki ba, haka yasa yanke hukuncin Abas zaki aura, akwai freind ɗina da muke aiki dashi a asibiti shima ya nuna yana sanki na taka masa burki saboda naga shi ɗan tsalle tsalle ne yau kajisa anan gobe acan, kirike Abas sosai yana matuwar sanki zan iya rantse maki da Allah yafi Mustapha sanki, mahaifiyarsa na sonki in har kika aure sa insha Allah bakida matsala a gidansa, sai dai binciken danayi antabbatar min shi ɗin soja ne,zaki iya auran soja?" ya karasa faɗa da murmushi yana kallota
"Zan iya auransa tunda har kana sonsa nima zan so sa insha Allah duk abinda kake so nima inaso"
"Au zama ki so sa wai har yanzu baki sonsa cab sannunki"