← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 62

Sashe 38

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tsaye a É—akin nata rike da waya suna magana da Amarya, shigowar Mustapha É—akin yasa ta katse kiran tayi zuru tana kallonsa, zama yayi gefan gado ya nuna mata kusada shi ya ce
"Sumy zoki zauna muyi magana" ba musu ta zauna inda yace É—in, jimm yayi na É—an lokaci har saida ta É—ago kanta ta kallesa taga shima ita yake kallo kasa tayi da kanta tana murmushi
"Sumy kiyi hakuri da abinda zan faÉ—a ki fahimceni please"
"Ina jinka" tafaÉ—a tana wasa da zoban hannunta
"Zan tafi da Aimanah legos" da sauri ta É—ago ta kallesa sai kuma tayi kasa da kanta hawaye masu É—imi suka biyo kuncinta
"Shi yasa nace ki fahimceni Aimanah nada juna biyu, tunda ta sami cikin nan take son kamshin turare na, na ajje mata su dayawa amma sai tace na jikina take so yau ranar komawata legos ta tubure saita bini na rasa yanda zanyi da ita shiyasa nazo na roki kimin alfarma natafi da ita"
"In naki yin alfarma fa?"
"Dole ta zauna ai bazan shiga hakkin ki ba"
"Hakki kuma na nawa Musty, ca nake nan kasai mata motar sama da miliyan talatin ni kuma kasaimin wacce bata kai miliyan goma ba"
"Sumy kibar maganar motar nan, kyauta ce na mata tun tuni na kudurce a zuciyata zan mata wannan kyautar tun kafin ki shigo rayuwarmu, Sumy bazan ɓoye maki ba kin rigada kin sani Aimanah itace jini da tsokata itace bugun numfashi na karki soma kwatanta kanki da ita ina matukar iya bakin kokari na na kamanta adalci a tsakanin ku shiyasa kema na sai maki mota" tabe baki tayi ta tashi zata fita a ɗakin sai da takai bakin kofa sannan ta juyo ta kallesa
"Na amince ku sauka lafiya" fita tayi daga É—akin ta faÉ—a É—akinta ta fashe da kuka, tabbas ayau basai gobe ba zata barwa Mustapha gidan sa bazata zauna kishi ya kasheta ba, to in kuma nabar gidan yasakeni ina zan zauna gidan mahaifina ba daÉ—i Mama tabar gidansu Mustapha ina zan kama tabbas dole na zauna a É—akin mijina in yaso na nemi mafita kawai, ko Mama zanyiwa magana mu koma wajan tsito a farraka tsakaninsu kai ai kuma komai daÉ—ewa asiri zai karye ga zunibi ga ba biyan bikata, ita kaÉ—ai take ta zancan zuci har barci yayi gaba da ita tanata barci Mustapha suka tafi bata sani ba saida ta tashi a barci taga massages na Mustapha yana sanar mata sun wuce yazo suyi sallama ya tarar tana barci in sun sauka zai kirata a waya

Rayuwa mai daÉ—i da kwanciyar hankali Aimanah keyi a legos tayi kiba ta kara yin fresh, kullum suna tareda Musty daga yadawo daga office baya kuma fita ko ina yana gida tare da Aimanah kulawa ta misamman yake bata yana, duk friday yake zuwa kano yayiwa Sumayya kwana biyu ya koma legos,

Aimanah ta tsaye a kicin tana soya irish Mustapha ya shigo kicin, rungumeta yayi ya zagaye ta da hannunsa É—aya É—ayan kuma yana shafa cikinta
Reina yakamata ki rinka samun hutu fa tun asuba kina nan kina fama nace zan samo maki mai aiki kinki yarda"
"Allah ya kiyaye baby inban kula da kai wazanyiwa ni bana bukatar wata mai aiki kawai ta kwace min kai" dariya Musty yayi haÉ—i da kwantar da kansa a bayanta yana lumshe idanuwansa
"Reina zuciyata taki ce ke É—aya ko bake a duniyar nan bana jin zan so wata bayan ke, ina sonki ina kaunarki! zuciya da ruhi duka na begenki hmmm reina baki yayi kaÉ—an ya iya bayyana kalar son danake maki ki kalli cikin idaniya su kaÉ—ai sun isa su bayyana maki kalar so da kaunar danake maki, ko yaushe in ina tare dake ji nake kamar nan duniya gaba É—aya babu sauran kowa daga ni sai ke Aimah I love you"
"Love you tuch baby" tafaÉ—a tareda sumbatar hannunsa,
"Kawo na karasa kije ki huta bari zan haÉ—o komai"
"A'a baby kabarni na karasa ladana"
"Nima ki bari na sami ladan, kije kawai bana son musu Aimah" hannunta tasa ta kunna famfon sink ta wanke hannunta ta fita, tana zuwa wanka ta faÉ—a ta shirya cikin farin wando dogo da karamar riga black colour ta É—aure gashinta waje É—aya bata saka hula ba ta fito falo tana danna wayarta, ya gama haÉ—a komai yana zaune a danning area yana amsa waya, kujerar kusa da tasa taja ta zauna tana kallon yanda yake dariya da alama ko da wa yake waya wayar na masa daÉ—i
"Aboki bazaka gane bane abar maganar nan sai anyi bikinku da Surry zaka bani labari" tana jin haka ta gano da yaya Mas'ud yake waya, bataji mai yaya Mas'ud É—in yace ba taji Musty na faÉ—in
"Kaga gimbiyya na kusa bazaka cinye mata sauran lokacinta ba in na shigo kano ma karasa maganar amma dai nace ka zaɓi India kasar nada daɗin zama" bai jira abinda Mas'ud zai ce ba ya katse kiran, yaja plate yana zuba mata soyayyan irish ya mika mata gabanta tea ya haɗa mata yasa tea spoon cikin mug ɗin ya ce
"Ha na baki a baki"
"Zan iya jira ka bani kuwa nifa yunwa nakeji sosai" ɓata fuska yayi yana mata hararan masoya
"Nidai saina baki Allah" yafaɗa a shagwaɓe haɗi da ɓata fuska
"To naji gashi na buÉ—e bakin" Irish É—in ya É—iba ya zuba mata a baki ta soma ci a hankali, saida ya tabbatar ta koshi kana ya kyaleta
"Baby nima tsaya na baka" zama ya gyara ta ciyar dashi cikeda kauna, har wajan mota ta masa rakiya tanata masa shagwaɓa harya kusa makara yatafi tana ɗaga masa hannu, sai da get man ya rufe get san nan ta koma ciki, gyara ko ina tayi ta sannan ta shiga kicin ta tarar ya wanke kayan da sukai amfani da shi, ta wanke plate da Mug ɗin da sukai amfani dasu ta wuce bedroom ta kwanta, bata tashi ba sai azahar sallah tayi tai wanka ta zauna suna chat da Rumana datake bata labarin rayuwar da suke itada Abbas tana mata godiya bisa zaɓin data mata, ganin biyu da rabi har tayi yasa ta mata sallama ta wuce kicin, wake ta ɗora a electry kana ta ɗora shinkafa kan gas ta ɗebo kayan miya ta wanke ta saka hand clove ta gyara kayan miyan ta cire dattinsu ta sake wanke su sosai da gashiri kana ta markaɗa su a blandar kafin la'asar ta gama haɗa lafiyaryar shinkafa da wake da miyar dake ta tashin kamshi ta yanka salad tumatir cucumber da albasa har green pepe ta zuba haɗaɗɗiyar kula ta kawo su dannin area ta ajje, salla taje tayi bayan ta idar azkhar na maraice tayi ta ɗau wayarta ta kira Mustapha, bugun farko yai pickin call ɗin
"Barka da aiki Rayuwata"
"Barka dai habibiya"
"Baby inajin yunwa fa baka dawo ba har yanzu" shafa kansa yayi yana murmushi yayinda kujerar dayake kai ke juyawa da shi, sai wani kumshe idanu yake da gani wayar na masa daÉ—i
"Beb kici kawai, ayyuka sun rikeni Aliyu baya nan ya haÉ—amin aikin office É—insa da nawa gaba É—aya ni nake yi inaga sai mangari ba zan da wo"
"To abincin fa? haka zakayita zama bakayi lonch ba gaskiyya bazan laminta ba, sai yunwa ta kama min kai,"
" zan.." A'a Baby karka gayamin zaka ci abincin waje, Allah bazan yarda ba, ko nazo na kawo maka nan"
"A'a bari na turo driven mu na office ya karɓar min ki bawa Joseph in yazo sai ya basa" dariya Aimanah tayi tana mamakin kishin Mustapha
"And kisa hijab kuma basai kin masa magana ba zan masa waya"
"Baby"
"Uhmm bebyn baby yane" .
"I love you" kissing wayar tayi kana ta katse kiran, tayi kamar yanda ya ce, bai dawo gidan ba kuwa sai gabda sallar insha, wanka kurum yayi ya fita masallaci dake nan kusada gidan, wajan takwas da rabi ya shigo gidan ya tarar tana zaune a danning area, can ya isketa yana mata sannu, soyayyar taliyar da tayi wadda taji kayan lambu ta zuba masu a plate suna ci a hankali suna hira jefi jefi

A kano tuni aka É—aura auran Murjana da Alhaji Jamil ta tare a gidansa da yake tare da matarsa anan tarauni , sam bata sami matsala da matar saba mace ce yar ba ruwana aikinta kawai tasa a gaba sai dai ta kula tana yawan tara mata a sashinta datayiwa Alhaji Jamil magana yace ai tana business ne shiyasa, ganin bata shiga sabgarta itama saita kama kanta kusan ma ba zaman kasar suke da ba kullum suna tafe itada Alhaji Jameel data zamo masa jela.

*Gidan Abbas*

Ruma na kwance lamo kan kujera yayinda Abbas ke zaune kan carfet yana aiki a laptop É—insa, jefi jefi yake kallon ta ganin yanda take juyi kan kujera
"Rumy yane?" yafaÉ—a yana barin danna laptop É—in dayake
"Hayatie cikina ciwo wayyo Æ´a'Æ´an cikina zasu zubo" da sauri ya mike ya karasa kusa da ita ya É—agota ya haÉ—ata da jikinsa
"Daman bakida lafiya baki gaya min ba mai yasa kika ɓoyemin"
"Yanzu ne fa, yanzu naji cikina na ciwon wayyo zan mutu" tafaÉ—a tana juyi tareda wata mika, gaba É—aya hankalinsa yata shi lambar nurse jamila dake cikin barreck É—insu yake kira amma bata shiga, da sauri ya mike ya É—auki Rumana cak ganin idanunta sun kakkafe, yafita da ita yana kwalawa jakop direver É—insa kira da sauri jakop ya karaso inda uban gidan nasa ke kiran sa
"Jakop maza É—akko mota muje hospital Rumy ba lafiya" yafaÉ—i haka yana leka idanunta dayaga sun kafe waje É—aya
"Jakop" yafaɗa da karfi hankali tashe a bayan mota ya kwantar da ita yana tukin da hankasa, mahaukacin gudu yake bisa kwalta yanayi yana juyowa yana kallon Rumana dake kwance kamar gawa....✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da bakwai*

*Wannan page É—in gaba É—ayansa sadaukarwa ne ga yan Aimanah real fans group 2 comment É—inku na matakur sani nishaÉ—i ina godiya da kulawa mutane na*
Chapter 38 · 0% Book details