← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 62

Sashe 54

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

KANO
Ammi gaba É—aya hankalinta ya gama tashi da jin labarin da Shaheed ke bata kuka take sosai a cikin hospital É—in, Momy da Yaya Ahmad ke lallashinta
"Naso na gano wani abu sanda naje Abuja amma danayiwa Alhaji magana sai yace ba haka wai na cika zargi daga nan nabar maganar, kaico kaico da wannan auran na Aimanah tabbas gobe saina je abuja sai Mustapha ya saki yarinyar nan, hmmm Mustapha Allah ya.."
"A'a Ammi dan Allah karki yiwa É—an uwana baki"
"Ko kusa Ahamad bazan taɓa aibata ɗan wani ba bare ɗana dana ɗauki cikinsa tsawon wata tara na shayar da shi na watanni goma sha tara ba baki zan masa ba Allah ya shirye sa zance" Aslam da Tasnim Momy ce ta wuce gida da su binciken likitoci ya tabbatar lafiyarsu kalau, Islam ce dai maleria da typod suka ci karfinta, saiko olsa data kamata hakan yasa aka ɗorata kan magunguna da allurai amma sun kwantar da ita a hospital ɗin danci gaba da kwaje kwaje, Alhaji Kamal ma yaji haushi da bakin cikin abinda yafaru hakan yasa yaɗau alwashin kafarsa kafar Ammi gobe da shi za'ayi tafiyar nan zuwa Abuja,

AMARYA
Shiri suke sosai na tafiya taron da zasuyi a kaduna Hanne an kasa zaune an kasa tsaya kasancewarta babba a harkar shiyasa take ta amsa kiran waya kala kala, wajan tara na safe suka É—auki hanyar kaduna a motoci uku Hanne da Amarya da Rahila sai wasu matan guda biyu sune a sahun farko, driver É—in Hanne ke jan motar tasu, kaguwa da Hanne tayi ta ganta a kaduna yasa ta azalzali driver É—in dayayi gudu sosai suna gafda shiga zariya sukai mummunan hatsari ba kyan gani Hanne tuni ta amsa kiran Allah sakamakon kanta da babbar mota ta taka yai kaca kaca akan kwalta, Amarya kuwa a sume akayi hospital da su itada sauran yan motar, abin Allah driver É—in ba abinda yasame sa sai buguwa da yayi a gefan kansa mota kuwa tuni ta tashi a aiki, Amarya lokacin data farfaÉ—o ta dawo hayyacinta shuru tayi tana kallon yan asibitin ba inda ke mata ciwo amma tayi tayi ta tashi ta kasa hakan yasa ta É—aga hannunta ta kira wani likita dake tsaye kusada gadon wata mara lafiya da alama duba ta yake, sai da yagama da ita kana ya karaso inda Amarya ke kwance kan gado
"Sannu kin farka kenan, ya kike jin jikin?"
"Ba inda ke min ciwo sai dai nakasa ta shi zaune" zaro idanu likitan yayi alamar firgici ya É—auko allura ya caka a kafarta yaga ko motsi batayi ba
"Bakiji zafi ba"
"Ba zafi, ji nake kafar kamar ba'a jikina take ba"
"Hajiya ina yan uwanki, sai an maki hoton baya muga ya lakar ki take da alama fa kinsamu tsinkewar laka, hoton zai nuna mana in wanda zai gyaru ne sai ayi gyara" hawaye Amarya ta soma musamman bayan tafiyar likitan da driver É—in su ya shigo shi yake shaida mata mutuwar Hanne da halin da sauran ke ciki, tayi kuka sosai tai nadamar wannan tafiyar tana faÉ—in data sani bata zo ba, shi ta bawa lambar Murja ya kirata ya gaya mata Mamanta tayi hatsari tana asibiti ana bukatar ganin wani nata, hankali tashe Murjana ta kira Sumayya ta gaya mata, ita kuma ta fara shirin tafiya zari'a itada Alhaji Jamil

Ammi nayin sallar asuba bata koma barci ba ta hau shiri karfe shida na safe suka É—auki hanyar Abuja itada Alhaji Kamal da Ahmad saiko driver É—insu, wajan sha É—aya da wani abun na safiya suka shiga abuja gaban Ammi bugawa yayi sanda driver É—insu ya faka motar a cikin gidan Mustapha, jiki sanyaye Ammi itada Ahmad suka jera zuwa ciki musty na zaune saman kujera yayinda Sumayya ke tsaye tana danna waya murmushi shimfiÉ—e a fuskarta kamar ba ita Murja ta kira tana gaya mata mahaifiyarsu na hospital ba, É—agowa tayi ta kalli su Ammi da suka shigo da sallama, daga kallo É—aya bata sake yi masu wani kallon ba ta maida kallonta ga madubin wayarta tana cigaba da murmushinta
"Ammi barka da safiya kune da safan nan, Ahmad bisimillah zauna" Mustapha yafaÉ—a yana nunawa Ahmad kusa da inda yake zaune,
"Bazama mukazo yi ba, Mustapha ina Aimanah?"
"Aimanah ai bata gidan nan Ammi tun jiya na sallameta na bata takarda ko Honey" yafaÉ—a yana kallon Sumayya
"A'A kaga ba ruwana, karka sako ni a zancan ku yanzu matar nan ta ce na maka asiri ka rabu da matarka, bayan ni banma san anyi ba"
"Ke!!! shiga hankalinki kisan da wacce kike magana" Ahmad yafaÉ—a a zafafe harda mikewa daga inda yake zaune yana huci kamar zai kai mata duka, Ammi kasa magana tayi sai ma buÉ—e É—akin Aimanah da tayi ta shiga, shuru É—akin sai darduma a shimfiÉ—e, takardar dake ajje saman gado ta É—auka hannunta na karkarwa ta buÉ—e ta karanta
_Ni Mustapha Kamal Sareena na saki Aimanah saki É—aya_ dafa bango Ammi tayi tana hailala da tasbihi ga ubangiji lalle mutum abin tsoro futowa tayi daga É—akin tana kalllon Ahmad,
"Muje Ahmad" bata tsaya ba tayi gaba abinta, Alhaji Kamal na tsaye jikin mota yaga futowar Ammi da Ahmad harma da Mustapha da Sumayya, har kasa Sumayya ta tsugunna ta gaida Abba daya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa
"Abba wai dama Aimanah bataje gida ba, tun jiya da yamma fa tabar gidan nan Mustapha ne ya bata takarda sabida ya kamata ta satar masa kuÉ—i, ba yanda banyi da ita ba akan ta zauna mu basa hakuri ta kafe sai da ta tafi ko ina taje, Allah yasa tana lafiya" Sumayya ta faÉ—a harda kukanta kamar gaske, kallon mamaki Ammi kewa Sumayya lalle mace shu'uma ce
"Assha Mustapha garin yaya haka ta faru banyi farin ciki da jin maganar nan ba"
"Abba ba wannan ba, bar waɗannan mutanan mu fara kiran yan uwa ko Aimanah taje kano" kusan duk wanda Ammi ta kira amsa ɗaya ce bata zo ba, haka ya kuma tasar hankalin Ammi sosai, hankali tashe suka baro Abuja suka juyo zuwa kano, Ammi kuka sosai take da tunanin inda zasuga Aimanah anan kano bincike sosai akayi har mutuware sai da Ammi da Ahmad suka rinka zuwa suna dubawa wai ko ta taho sukai hatsari ta mutu, wasa wasa tun ana ɓoye magana har magana ta fito sarari Aimanah ta ɓata, hanakali tashe yayu da iyayan Aimanah suka duro kano, Mus'af kamar yayi hauka lokacin da labari yaje masa yana sauka a nageria Abuja daman ya sauka sawa yayi yan sanda suka kama Sumayya da Mustapha da zargin sun ɓatar da yarinya, anan sell na yan sanda yabarsu ya hau jirgi ya wuce kano, sai da Sumayya da Mustapha suka kwana biyu a cell sannan Mus'af yafaɗa yasha faɗa a wajan Daddy shiya tilas ta sa aka sake su suka koma gida Sumayya na daɗa cin alwashi...✍🏻
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Talatin da biyar*

Hajiya Zainab zaune gaban gadon da Aimanah ke shimfiÉ—e kamar gawa, Muhd na gefanta yana dannan waya yayinda Azinatu ke zaune itama kan gadon daga gefan Aimanah, gaba É—aya sunyi shuru abin duniya duk ya dami Hajiya Zainab zuciyarta fal da zulumin kar yarinyar nan ta mutu
"Moha a fara binciken daga ina yarinyar nan ta fito, na tabbata zuwa yanzu iyayanta na cikin tashin hankali yau kwana shida fa kenan"
"Mom wannan fa daga gani irin yaran nan ne dake aiki a gidajan masu kuÉ—i kilama sata tayi aka koreta daga inda take aikin" Azinatu ta faÉ—a tana hararar Aimanah wacce bata san tanayi ba
"Wannan ce tai maki kama da masu aiki, ke dai kawai kin saba saikin ai bata mutum, ke bazaki canza hali bako, bar asibitin nan ki sani É—an adam ba abin wulakantawa bane kilama tafi ki gata" Azinatu hararar yayan nata tayi tareda kyauda kai gefe
"Moha bana son hayaniyar nan taku kuje gida dan Allah"
"Gaskiyya Mom anemo wacce zata kula da yarinyar nan ki koma gida yaufa kusan sati kenan rabonki da gida, ga ranar Anty Ramla inda tana nan da tini ita ke kula da yarinyar nan" Muhd kallon Azinatu yayi ya fice daga É—akin batare daya ce mata komai ba, da sauri ta mike tabi bayan Muhd tasan ba karamin aikinsa bane ya tafi ya barta anan, Hajiya Zainab mikewa tayi ta shiga bathroom tayi alwala ta tada sallah nan cikin É—akin, tana zaune saman dadduma tai nafila raka'a biyu ta soma jero addu'o'i har barci ya É—auke tana nan saman daddumar
Chapter 54 · 0% Book details