← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 62

Sashe 13

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mustapha sun sauka lafiya a nageria kai tsaye jirginsu a kano ya sauka daga airport texzi yasamu ta kawo su har gidansu wanda baida nisa sosai da airport, ba wanda yagawa dawowarsu hakan yasa kowa na gidan ya shiga murna da dawowar Mustapha banda Amarya da damuwa gaba ɗaya ta mamayeta har ƴar rama tayi na fargabar halin da zasu shiga itada Sumayya Murjana ba karamar ɓarna tayi masu ba hatta aikin da tayiwa Alhaji Kamal saida tabi inda suka binne ta tone komai shima gaba ɗaya ya canza mata, yau tsaka sai ganin Sumayya tayi a ɗakinta saida gabanta yafaɗi ganin Sumayya
"Ke kuma yazaki shigo min nan basai ki wuce gidanki ba, ni basai naje mu gaisa ba"
"Mama Musty fa cewa yayi na zauna zai neme ni" dafe kai Amarya tayi tana faÉ—in
"Shikenan na shiga uku tamu ta kare" Murjana dake zaune a gefe dariya tayi tareda saka eair pies a kunnanta tana faÉ—in
"Kuna ruwa"
"Allah wadaranki Murja ubangiji ya kwashe maki albarka yasaki a masifar da kika samu"
"Mama wannan wacce irin addu'a ce? kefa uwa ce in kina mata irin wannan baki saiya wahalar da ita"
"To Sumayya wahala ta nawa kuma ai wahala yanzu ta fara itace fa ta tone duk abunda muka bunne"
"Duk da haka Mama, Murja ai yarinya ce yarinta ke É—awainiya da ita dan Allah ki daina mata addu'a irin haka" Mama bata sake cewa komai ba taja hannun Sumayya suka wuce cikin É—akinta.

Mustapha kai tsaye É—akin Ammi ya shige yayi sa'a kuwa tana gida lokacin tana tsaye jikin firij zata É—akko ruwa taji an rungumeta ta baya bata zaci Al Mustapha bane duk zatonta Shaheed ne tasan shine mai mata haka
"Shaheed Allah ya nuna min randa zaka girma ka daina min wannan rungumar" jin ansake kankameta ba'ayi magana ba ga wani kamshin turare na daban da takeji yasa tasan ba Shaheed bane
"Hmm Amadu sakeni karka saka na faÉ—i"
"Ammi kin manta dani, Allah yasa ma baki cire ni a jerin yaranki ba" Ammi goran ruwan hannunta ta saki ya faÉ—i a kasa tai saurin janye hannunsa daga jikinta ta juyo tana kallon Mustapha
"Mai babban suna saida kabaro kasar nan kadawo ko?"
"Ammi na gama fa, bakiyi farin ciki da dawowata ba ko? nasani nasan za'ayi haka duba da tarin laifukan dana aikata"
"Nayi farin ciki sosai Yayansu na kuma godewa Allah daya dawomin dakai lafiya, ina matar taka?" ɓata fuska Mustapha yayi ya juya zai fita Ammi ta rike hannunsa
"Ammi ba matata bace sakinta zanyi"
"Karka soma Mustapha ban amince kasaki Sumayya ba kaci gaba da zama da ita sannan ka zage wajan addu'o'i da Azkhar"
"Ammi bazan iya zama da ita ba, Ammi Aimanah tagama school ko?"
"Mubar maganar Aimanah jekayi wanka kazo kaci abinci mayi magana daga baya" Mustapha jiki sanyaye ya fita daga gidan zuwa gidansa, gidan yayi kura sosai, dole yadawo gidansu É—akin Ahmad yai wanka ya shirya, yasa Surayya itada Shaheed su gyara masa gidan, kafin ya gama wankan Ammi ta haÉ—a masa abinci ya zauna taci abincin sosai saboda yayi kewar abincin gida nageria sosai, yana gama cin abincin yayi hamdala yana kallon Ammi
"Ammi muyi maganan Aimanah so nake naje na ganta na wanke kaina"
"Mustapha" Ammi ta kira sunansa tana kallonsa "Kayi hakuri bazan munafunce ka ba, Aimanah tasami wani auranta ma kwanaki suka rage" da sauri ya mike tsaye yana kallon Ammi yakasa cewa komai yai tsaye kan Ammi baki buÉ—e so yake yayi magana amma yakasa saboda wani abu daya tokare masa a makoshi, yakoma ya zauna saman kujera ya kifa kansa saman teble, wani irin bugu zuciyarsa keyi harta Ammi dake zaune kusa da shi tanajin bugun zuciyarsa jin shiru tsawon mintina Mustapha bai motsa yasa Ammi ta É—ora hannunta a kansa, É—agowa yayi ya kalli Ammi idanunsa sunyi ja sosai kamar garwashi Ammi hankalinta ya tashi sosai tasani daman tasan za'arina wai ansaci zanin mahaukaciya tasan tsananin son da Al'mustapha kewa Aimanah,
"Al Mustapha kayi hakuri kaÉ—au abin nan a matsayin kaddara sannan kasa a ranka dama can Aimanah ba matarka bace"
"Ammi kaddara kaddara fa kika ce, sai in tsaya ina nan a raye a aduniya ina numfashi wani can wawa ya aure Aimanah,Allah kar yasa naga wannan rana, da wani ya auri Aimanah ina raye gara na mutu nabar duniya, Ammi wannan kaddarar tamin nauyi bazan iya É—auka ba, Ammi gayamin wacce addu'a akeyi mala'ikan mutuwa yazo ya É—auki ran mutum" Ammi ta mike tsaye tareda kama hannun Mustapha ganin yanda jikinsa ya fara rawa, kalaman dake futowa daga bakinsa kaÉ—ai sun tabbatar mata da Mustapha baya hayyacinsa, bedroom É—inta ta kaisa ta zaunar dashi gefan gadonta ta ce
"Mustapha kwanta ka kaji barci inka tashi zakaji sauki a zuciyarka"
"Ammi barci bazai iya É—aukata a wannan yanayin ba vani aron makullin motarki naje wajan Aimanah"
"Mustapha bazan bari ka fita a wannan yanayin ba ka kwanta nace" bazai iya masu da Ammi ba hakan yasa ya kwantar da kansa saman filon Ammi
"Kayita hasbunallahu wan'?wani'imal wakil zuciyarka zatayi sanyi" yajima yana kwancan yana ambaton hasbunallahu har yaji salama a zuciyarsa Ammi tana can Kicin ya lallaɓa ya fice daga gidan.

......Aimanah a shirye ta fito daga É—akinta gidan shiru ba kowa, kowa ya wuce wajan aikinsa ita kaÉ—ai ya rage a gidan itama yau dan bazata fita da wuri ba, tana fitowa compount taga shigowar motar Ammi fasa karasawa wajan motar tata tayi ta nufi motar Ammi, motar Ammi tinted ce na waje baya ganin na ciki amma na ciki yana iya ganin na waje, buÉ—e murfin motar Aimanah tayi cikeda É—okin ganin Ammi kasancewar sun jima basu haÉ—u ba
"Ammi Wellcome" Da sauri Aimanah tayi baya tareda dafe kirjinta, tsaye tayi tana kallon Musty dake jingine jikin mota yana aika mata da zazzafan kallon love wanda ya kusa tarwatsa zuciyarta, tabbas yasani bata jure irin wannan kallo ko acan baya bare hanzu, juyawa tayi zata bar wajan da sauri yakira sunan ta
"Aimaah" cak ta tsaya ta kasa tafiya na ƴan sakanni can kuma yaci gaba da tafiya da sauri ta nufi motarta, tasa makulli zata buɗe motan Al'Mustapha ya ɗora hannunsa saman nata ya zare car key ɗin daga jikin mirfin motar ya zirasa a aljuhunsa ya harɗe hannayansa a kirji yana kafe Aimanah da lumsassun idanunsa masu kama dana maijin barci.....✍🏻

*Saura kiris adaina fitar da Littafin Aimanah za'a daina posting É—insa a ko wanne group sai Aimanah fans group da Aimanah comment section idan har kinsan kinason cigaba da karanta Aimanah maza yi save É—in wannan lambar 07039793439 kiyi magana ta whatssapp zatayi adding naki a group É—in da zaki karanta hankalinki kwance batare da ko sisinki ba*
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na goma sha biyu*

.....Aimanah kasa jure kallon nan tayi hakan yasa tayi kasa da idanunta gabanta na cigaba da dukan uku uku
"Aimaah nasani ni mai laifi ne a wajanki, kiyi hakuri ki yafe min bada sanina hakan ta faru ba"
"Kamin shiru ka kyaleni Al'Mustapha ka bar nan wajan bana sonka bana kaunar ganinka" Aimanah tafaÉ—a tana rushewa da kuka
"Aimaah please stop craying kukanki kin sani yana taɓan zuciya kiyi shiru muyi magana ta fahimta"
"Na fahimceka? wazan fahimta? kai can a baya mai yasa katafi ka barni da ciwo a zuci sai yanzu kadawo kace na fahimceka, Musty nariga nawuce level É—inka kaje can ka zauna tareda masoyiyarka wacce ka guji kowa sabida ita"
"Aimah komai zan faÉ—a maki bazaki gane ba ki bani dama a karo na biyu a zuciyarki"
"Zuciyata a yanzu babu kai Abas ne aciki shine mai mulkin zuciyata dan Allah indai zancan soyayya ne yakawo ka kabar nan"
"Bazan bari ba Aimah yazama dole ki tsaya muyi magana, ashe daman har akwai wani da zuciyarki zata so bayan ni?"
"Kasa a zuciyarka ban taɓa soyayya da kai ba, lokacin dana so ka bansan zaƙi da ɗacin so ba, kasani a yanzu bana sonka! bana sonka!! bana sonka!!! nafaɗa bana kaunarka" taci gaba da kuka tareda kwasa da gudu ta shige falo ta rufo kofa, da sauri yabi bayanta kafin yakai harta sakawa kofar key da karfi yake buka kofar yana faɗin Aimah Aimah please ki buɗemin kofa"
"Bazan buÉ—e ba kafita kabar mana gida mugu macuci mayaudari azzalumi"
Aimanah ta dafe kirjinta datake ji yana wani irin bugawa da sauri sauri "Mai yasa kadawo yanzu? mai yasa zaka shigo rayuwata a yanzu, Abas kazo ka É—auke ni nadaina ganinsa" haka tayita surutai bayan ta kulle kofar tana jiyo sa yana rokonta amma takasa cewa komai kuka take sosai na tausayin kanta.
Chapter 13 · 0% Book details