← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 62

Sashe 29

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Aimanah tasawa kofar shigowa samanta key ta zare kay É—in ta koma ta zauna kusada Rumana wacce ke kallonta da mamaki
"Wai yaya Aimanah mai kikeyi haka ne kin rufe ko ina kin wani saki labulaye yanzu kuma kin sakawa kofa key Yayanmu fa yana gidan Ammi sanda na fito yana shirin tahowa nan shima fa, ki buÉ—e kofa karya zo yazaci ma wani abin" Aimanah tayi tagumi tana kallon Rumana hawaye suka zubo daga idanunta ahankali ta goge hawayan
"Rumana inason Abas, nasihar da Daddy yayimin randa za'a kawo ni gidan nan ita tasa na kwantar da hankalina na karɓi Musty a matsayin miji na rungumi kaddarata, Rumana inason sanin halin da Abas yake ciki, ina kuma rokon wata alfarma a gareki" Aimanah ta karashe maganarta tana saka hannuwanta cikin na Rumana
"Rumana ina rokonki alfarma ki auri Abas nasan bakida saurayi bakida kowa wanda ke sonki" jikin Rumana ne yahau ɓari tana kallon Aimanah ta zare hannunta daga cikin na Aimanah ta dafe bakinta🤭tareda zare idanu😳ta mike tsaye tanaja da baya baya
"Ni wai haba Allah ya kiyaye na auri wanda kika so haba Yaya Aimanah" Aimanah mikewa tayi ta dawo kusa da Rumana ta tsaya tana sake haÉ—a hannunsu
"Alfarma na nema Rumana ki taimaka kimin wannan alfarma tunda abin nan yafaru nakeji inama inada kanwa na bawa Abas na fara hasaso Surayya sai na gano suna soyayya da yaya mas'ud, tunani na karshe kwakwalwata ta tsaya a kanki, zakiyi farin ciki Rumana Abas mutum ne yayi ta ko'ina ina matukar maki sha'awar auransa, kamar yanda na gaya maki a baya har akai kwana biyar da auranmu da Mustapha banji a raina zanyi rayuwa da shiba, na kudurce a raina saina kashe auran nan na auri Abas amma girma da kimar Daddy tasa na manta da komai na jure zan zauna da Musty da ayanzu nakejin sa a zuciyata fiyeda Abas kawai dai ina tausayin Abas daga sanda kika amsamin kin amince da auran Abas zuciyata zata nutsu nasami nutsuwa da kwanciyar hankalin da zan bawa Mijina kulawa"
"Yaya indai har inna auri Abas zakiyi farin ciki a gidan Mustapha na yarda zan aure sa amma inyace baya sona fa?"
"Bakida damuwa da wannan bani wayarki" Aimanah taja hannun Rumana suka zauna saman kujera tana gayawa Rumana lambar Abas tana sakawa a wayarta tai call saida ta kusa katsewa sannan yai picking call É—in Rumana ahankali ta ce
"Hello" da sauri Abas dake kwance saman gadon asibiti ya mike zaune ya ce
"Haya"..dafe kansa yayi kana yace
"Aimanah" yafaÉ—a da raunanniyar murya
"Ba ita bace Rumana ce" wani bakon yanayi yaji na daban a zuciyarsa daya kasa banbance na mene
"Ga Yaya Aimanan zakuyi magana"
"Abas" Aimanah tafaÉ—a muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka
"Aimanah ya kike ya mi..." sai kawai yayi shuru yakasa karasawa
"Abas ya kake fatan kana cikin aminci" mikewa tayi ta shige bedroom É—inta ta zauna
"Ina lafiya Aimana ina mijinki kika kirani a waya?"
"Baya nan"
"Mai yasa zakiyi haka ki fara neman izininsa sai muyi magana"
"Ka bari muyi magana Abas tanada mahimmanci, nasan matsayina a zuciyarka hakan yasa zan roki wata karamar alfarma a wajanka"
"Wacce alfarma faÉ—i Aimanah ko wacce iri ce zan maki insha Allah"
"So nake ka auri Rumana"
"Rumana" ya maimaita da sauri
"E! Ita"
"A'a Aimanah dan Allah karki ce haka"
"Idan kamin haka raina zaiyi daÉ—i zata kula da kai nasan Rumana batada wata matsala zakaji daÉ—in zama da ita" hmmm Abas ya sauke numfashi
"Idan ni na amince ita fa"
"Nagama magana da ita"
"Shikenan na amince Aimanah, Allah yasa tanada halaye irin naki"
"Tanada fiye da nawa ma"
"Ki kasance cikin Aminci Aimanah ki zauna da mijinki lafiya ina maku fatan alkhairi"
"Nagode, wannan lambar Rumana ce dan Allah naji labari mai daÉ—i da zai sani kwanciyar hankali"
"Kamar ma kin samu ne Aimanah ki saka mana ranar bikinmu"
"Ku fara dai daitawa tukunna san samu karya wuce nan da wata guda"
"Da wuri haka"
"E!"
"Yaya Aimanah kizo ki buÉ—e yayanmu na buga kofa," tajiyo muryar Rumana tana faÉ—a daga inda take, saurin sallama tayiwa Abas ta fita, taje ta buÉ—e kofar, yana shigowa ya eungumeta a jikinsa
"Maye na rufe kofa" yafaÉ—a yana kallon cikin idanunta kamar mai son gano wani abu
"Kuka! kukan me kikayi?" kokarin kwace kanta take amma ta kasa duk kunya ta kamata ganin Rumana na cikin falon,
"Bazaki ce komai ba Aimah" ta buɗe baki zatayi magana ya haɗe bakinsa da nata da sauri Rumana ta salallaɓa tabar falon kar taga abinda yafi karfin idanunta, Musty zama yayi kan kujera ya ɗorata saman cinyarasa yana cigaba da abinda yake,
"Baby Rumana na nan fa"
"Na ganta na guma ga sanda ta fita" wai gawa Aimanah tayi tana kallon kujerar data bar Rumana a zaune taga wayam ba kowa😂
"Kinsa ta gudu kin bata kunya"
"Kabata dai ta faÉ—a tana lakace masa kumatu"
"reina na gaji zumu shiga daga ciki mu raba gajiyar nan"
"Gobe sunday fa nasan zakace zaka tafi ga Sumayya bata dawo ba"
"Munyi waya É—azu sai friday zata dawo, goben ai jirgin dare zanbi ko zakizo mu tafi tare?"
"A'a bazani ba nima monday hutuna zai kare"
"shikenan" musty yafaÉ—a sanda suka ahiga É—akin, hannu yasa ya É—au wayar Rumana daya gani ajje saman gado, ya juya wayar yana kallon Aimanah datayi kasa da kanta
"Wayar wace?"
"Ta Rumana ce"
"Rumana nan kika kawo É—akin kwanan mu?"
"A'a nina yi waya da ita"
"Ina taki wayar?"dawa kuma kikai waya"
"Yah Mus'af" tafaÉ—a muryarta na rawa,
"A'a reina nasanki gaba da baya zan iya rantse maki baki faÉ—a dai dai ba, ba da Mua'ab kikai waya ba, bana son karya akomai ki rinka gayamin gaskiyya komai É—acinta"
"Da Abas nayi waya" Aimanah ta faÉ—a kanta a kasa muryarta na rawa, Musty ya mike tsaye ya kama kugu yana kallon Aimanah, jikinsa a sanyaye ya koma ya zauna
"Aimaahh maina maki nai haka kin kasa mantawa da A"
"Ba wani abu nace masa ba nagaya masa ne ya nemi Rumana da aure"
"Bana so karki sake magana da shi"
"Insha Allah, bazan sake ba,"
"And karki sake ɓoyemin komai, mu rinka tattauna damuwarmu mu samu mafita tare"
"Insha Allah baby" tafaÉ—a tana sake kwanciya ajikinsa.

Abas da aka sallama suka koma gidansa tareda su hajiya komai yagaya mata yanda sukayi da Aimanah
"Kai ya kake gani?"
"Na yaba da hankalin yarinyar, na kuma karɓi rokon Aimanah amma ki gayawa Baba yaje yafara magana da iyayanta, karki gaya masa Aimanah ce tamin tayinta ki faɗa masa ni na ganta nace inasonta zan gayawa Rumanan da Aimanar subar maganar nan a tsakaninmu"
"Shikenan Abas nayi farin ciki da hakan Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi"
"Amin" yace bayan ya kwantar da kansa saman kujera,

Aimanah tunda yamma tayi tafara kukan shagwaɓa musamman sanda taga yana haɗa kayansa cikin trolly, kwanciya tayi saman bed tana fashewa da kuka ganin Musty ya ɗauki jakarsa zai tafi, cikeda damuwa yadawo ya zauna kusa da ita yadafe kansa, can kuma ya mike ya buɗe wardrove yafara zuba kayanta a trolly
"Nifa bazani ba," tafaÉ—a cikin kuka
"Toya kike so nayi kin tisa ni a gaba kinamin kuka ku tashi kawai mu wuce legos É—in tare"
"Bazan bika ba hakan ai saiya zama rashin adalci ga Sumayya anan ni nabika can ai bamu kyauta mata ba koni akayiwa haka bazanji daɗi ba....✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da biyu*
Chapter 29 · 0% Book details