← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 62

Sashe 40

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby danna min kafar nan sosai zugi takemin bakaji azaba ba" Mustapha dake matsa mata kafa kara himma yayi tareda aika mata sannu akai akai tausayi take basa sosai ganin yanda ta kumbura musamman kafafunta da suka tasa cikinta mai wata huÉ—u inka kallesa zakace yakai watanni bakwai sabida girmansa, wayarta dake kusa da shi ce tayi kara alamar kira ya shigo hannu yasa ya É—auka ya mika mata cikeda É—oki ta É—aga ganin Rumana ce ke kiranta,
"Hasbunallahu wani'imal wakil" Aimana ta faÉ—a a razane tareda sakin wayar tata ta faÉ—a kan cinyarta, a razane Musty ya É—ago ya kalli Aimanah dake kokarin mikewa tsaye
"Ke maine wai nutsu Aimah"
"Baby Rumana ce a asibiti tayi ɓari" tsaki yaja yana cigaba da abinda yake a fusace ya ce
"Shine kika ruɗe haka, dan tayi ɓari Allah zai basu wani ai" saroro tayi tana kallonsa cikeda mamaki
"Baby Rumana fa!"
"Rumana maizan mata fatan samun lafiya kawai zan mata" fusge kafarta tayi ta mike
"Nidai Abujan zan tafi naga lafiyar yar uwata"
"Kiga lafiyar yar uwarki ko ki gano masoyinki"
"Mustapha" Aimana ta faÉ—a cikeda mamakin maganarsa, bai É—ago ya kalleta ba saima danna wayarsa daya fara yi ganin bai kulata ba yasa taci gaba da magana
"Nidai wallahi sai naje na duba Rumana yaufa kwananta huɗu a hospital ta kirani ta gayamin sannan kace bazani ba Allah sai naje naga yar uwata" kanzil baice mata ba saima tashi da yayi yabar mata gidan, bai dawo gidan ba sai batan sallar insha abinda bai taɓa mata ba matsawar yana gari baya fita ko ina ko wani uzirin ne ya kamasa na fita tare suke zuwa ko ina ne, a ɗakinsa ta kwanta ya shigo yana ganinta baice mata komai ba yai shirin barci ya kwanta can karshan gado nesa da ita sosai, ganin haka saita juya baya, washe gari kafin ta tashi yagama haɗa break yaci nashi yabar mata nata nan saman danning ya wuce office
"Kam bala'i" Aimana ta faÉ—a sanda taga abinda yayi agidan kicin ta wuce ta haÉ—a abinda takeso taci ta ajje sauran, saida ta fuskanci lokacin dawowarsa yayi ta koma É—aki ta kwanta lamo kamar mara lafiya, tana ganinsa ya shigo É—akin da sallama kasa kasa, suit É—insa ya cire ya É—aura tawul ya wuce bathroom bai kalli ko inda take ba, yana fitowa daga wanka ya ganta zaune kan gado tana kuka kasa kasa ba karamin juriya yayi ba ganin bai kulata ba, jin kukan yake har cikin ransa, ta gefan idanunsa yake kallonta yayin da yayi kamar baisan tana yi ba, wayarta ta É—auka ta kiran layin Ammi
"Ammi Mustapha zai kashe ni daga nace zanje na duba Rumana shikenan yaÉ—au fushi dani ya daina kulani ya daina cin abinci na yama daina kwana a É—akin danake" murmushin gefan baki yayi yana satar kallonta ganin yanda take haÉ—a masa karya a gabansa ko kunyarsa bata ji
"Shi mai babban sunan yamaki haka, cab bari na kirasa naji dalilin da zaiwa yar Ammi haka kuma ki soma shiri gobe zaki gano yar uwarki" kwalo tayiwa Mustapha a zatonta baya ganinta, Musty yana ganin kiran Ammi yaki ɗagawa saima barin ɗakin dayayi da wayar a hannunsa, saida ya futa compound na gidan kana yabi kiran Ammi daya katse, Aimana batasan ya sukayi ba taga dai yadawo ɗakin ya kwanta baice mata komai ba, sa da tabari yayi nisa a barci ta tashi tsakiyar gado ta zauna tana faman kukan shagwaɓa
"Aimanah baza ki barni nayi barci ba ko?"
"Ba kaine ba kadaina min magana" tafaɗa cikin kuka, dafe kansa yayi gamida zuba mata idanu kana ganin yanda take kukan kasan na zallar shagwaɓa ne, matsowa yayi kusada ita yasata a jikinsa yana buga bayanta a hankali da hannunsa
"Is ok ya isa Reina kece rigimar ki tayi yawa a wannan halin da kike ciki kice wani zakiyi tafi"
"Naga a jirgi zanje kuma ai ba kwana zanyi ba randa naje ranar zan dawo bafa nisa legos zuwa Abuja"
"Hmmm" kawai yace ya kwantar da ita haɗida sata a jikinsa yana share mata hawaye har sukai barci a haka, shiya rigata ta shi yauma yayi abinda zaiyi ya fice sai text messages dayai mata na fatan ta taahi lafiya ya kuma sanar da ita ta shirya zasubi jirgin karfe biyu zuwa Abuja, murna tayi sosai sanda taga sakon cikin lokaci kankani ta gama komai, Aimana maca ce mai tsabta da iya girki ga uwa uba iya ado da kwalliya, ko kafin Musty yadawo tagama komai harta shirya cikin doguwar riga yar dubai tayi matukar kyau, sanda yadawo wanka yayi suka ci abinci ya fita masallaci yai sallah itama tayi nan cikin gidanta yana dawowa suka wuce airport yariga da yasaba indai zaiyi tafiya nan cikin airport ɗin yake varin motarsa inya dawo ya ɗauki abarsa, lafiya suka sauka Abuja duk ɗoki da son ganin Rumana da Aimanah take haɗiye sa tayi dan tunda suka sauka a Airport na Abuja Mustapha ke cika yana batsewa, wani haɗaɗɗan hotal Mustapha ya kama masu can suka sauka a recepsion ya karɓi key na ɗakin ya wuce dan tun a office ɗinsa ya gama komai ta online shiyasa key kawai suka basa anriga da an gaya masa number ɗakin, suna shiga ɗakin Musty tafara rage kayan jikinsa ya rage daga shi sai singlate da gajeran wando ya haye gado yana faɗin wash
"Amma yaya inace hospital ɗin zamuje" kanzil baice mata ba saima gyara kwanciya da yayi yana kallon agogo, ba yanda taso itama kwanciyar tayi nesa da shi ta cure waje guda a haka barci yayi gaba da ita, Kiraye kirayan sallar la'asar ya farkar da Mustapha daga barcin da yayi yaga yanda Aimanah ta cure waje ɗaya, da sauri ya gyara mata kwanciya ya lulluɓa mata blanket ya wuce bathroom yai wanka da alwala ya wuce masallacin dake nan cikin hotal ɗin, harya dawo rike da babbar leda a hannunsa bata tashiba shima bai tashetan ba sai wayarsa daya ɗauka yana dannawa, biyar da kwata Aimanah ta farka taga gari yafara duhu addu'ar tashi daga barci tafara kana ta tashi zaune
"Sannu kin tashi" gira kawai ta É—aga masa ta mike ta shiga bayi tayi wanka da alwala, futowa tayi tana raba idanu
"Yanzu kayan nan zan maida wai" da idanu ya nuna mata ledar dake ajje saman bedsite drowar buɗewa tayi dogayan riguna ne guda biyu yan maroco ja da baka sai manyan hijabai guda biyu, jar tasaka ta ɗaura karamin mayafin rigar a kanta ta saka hijab ɗin tai sallah, kafin ta idar taga yagama shiryawa cikin bakaken suit sak yafito a kalarsa ta ma'aikacin banki🤭tana azkhair ya zauna gefanta ya ajje likab a gabanta, dariya taso kwace mata amma sai ta shanye ta, ta shafa fatiha tana kallon sa shida likabin gabanta
"Kisa muje hospital É—in"
"Inajin yunwa, kuma Allah bazan saka abin nan ba, ban taɓa sawa ba dan haka bazan koya yau ba"
"Aimanah ki taimaki zuciyata ki sakaya min kyakkyawar fuskar nan taki"
"Mustapha kar muyi haka dakai duka akan Abbas ne kake wannan abun, Abas Rumana yake aure, na tabbata a yanzu babu wani sauran abinda yayi saura tsakani na da shi, kai nakeso kaine abokin rayuwar da Allah ya zaɓa min koda baka raye nan duniya bana jin zai iya auran wani kisa a ranka ni taka ce har abada na roke ka ka rage kishin nan naka akan Abbas"
Jikinsa ne yai sanyi da maganganun Aimanah hakan yasa yai shuru tareda komawa gefe ya kira a waya aka kawo masu abinci, basu sami fita ba sai bayan da sukai sallar mangari ba sannan suka fita zuwa hospital É—in da Rumana take
"Baby a ina kasami mota?"
"Munyi magana da yah Mansur shiya saka aka kawo min"
"Mutanan landon ana can"
"Suna can kam ɗazu mukai magana da Mus'ab ma zai wuce Rasha acan zaiyi P h d" taɓe baki Aimanah tayi kana ta ce
"Shikenan gida yazama sai Mah da Ma'aruf kowa yasa gabansa yabar kasar"
"Wanda yasami dama ya dama Aimanah wannan kasar tamu sai dai addu'a kawai nima nafara tunanin komawa jordan can inda nafara aiki"
"Amma badai dani ba"
"Da Sumy" yafaÉ—a yana hararata sunata hira har suka karasa hospital É—in
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da takwas*

Cikeda tausayawa Aimanah takewa Rumana sannu, tana rike da hannunta
"Hajiya ina wuni" Aimanah tafaÉ—a tana kallon Hajiyar Abbas data fito daga bathroom, hajiyar Abbas ta rike baki cikeda mamaki fuskarta da murmushi
"Wa idanuna ke gani kamar Aimanah mutanan legos, yar uwarki ta taso ki ko?"
"Nice Hajiya yamai jikin"
"Jiki da sauki gobe ma zasu sallame mu mu koma gida" Aimanah kan tayi magana aka turo kofa aka shigo Abbas nw shida Mustapha sai Ammi a bayansu
"Lah Ammi daman kina nan"
"A'a yanzu nazo Abbas ne ya É—akko ni a airport ashe kunzo" Musty can gefe yasamu ya zauna saman farar kujera yana kallon Aimanah
"Yaya Abbas ina wuni ya mai jikin"
"Da sauki" Abbas yafaÉ—a idanunsa na kasa, Aimanah sun jima a hospital É—in har tara saura, Mustapha yabawa Abbas hannu sukayi musabaha tareda fatan sauka lafiya, Aimanah tabi bayan Muatapha daya fita bayan tayi sallama da su Rumana,

Aimanah da Mustapha kwanansu biyu a Abuja kana suka wuce kano inda aka fara bikin Surayya da Mas'ud, Aimanah bata wani sake sosai a bikin ba duk da dama ba wani shagali aka sha ba to ango yana india wajan karatu can za'a tura masa amaryarsa bayan an É—aura aure, satin su Aimanah biyu a kano suka koma Abuja,
Chapter 40 · 0% Book details