← Book details Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 62

Sashe 4

Aimana Mami Yusuf Dabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jiki a sanyaye yake tuka motar haka kawai yau yakejin ransa ba daɗi damuwa da baisan ko ta macece ba duk tabi ta addabi zuciyarsa haka kawai yaji baisan komawa gidansa amma ba yanda zaiyi dole yakoma, badan ransa na soba yakama hanyar zuwa gidan, tun daga falon gidan ranshi yakuma ɓaci wani uban kauri daya jiyo daga kicin yasa yai saurin nufar kicin ɗin abincime ake dafawa yakone yayi baki kirin sai hayaki yake gaf yake da kamawa da wuta da sauri yakashe gas ɗin ya sauke tukunyar kasa, jingina yayi da kantar kicin ɗin yadafe kansa yana faɗin "Ya salam" azafafe yafito ya kalli ko'ina kaca kaca komai zaman kansa yake kudaje sai bin falon suke dafe kansa yayi ganin ko kayan dasukai break ba abinda ta ɗauke yana nan ajje a wajan, afusace ya banga kofar ɗakin nata ya shiga amma duk zafin daya ɗakko sai yaji tayi masa wani gingirim tsoro da shakkarta suka shigesa yaji yama kasa faɗar abinda yazo faɗa, asanyaye ya zauna gefan gadon datake zaune sai faman latsa waya take da alama chat take kasa yayi da kansa kana yace
"Yanzu Sumayya kina kallon yanda gidan nan yake amma kike zaune anan kina chat gaba É—aya gida kaca kaca dan Allah in kikayi baki bazakiji kunya ba" zumburo baki tayi gaba tareda karkata É—aurin É—an kwalinta tana harararsa tace
"Aikai kajawo nace maka kasamo mana mai aiki kace bazaka kawo ba basai kayita kallo ba kazanta yanzuma aka fara, ni katashi ka yo mani take away kunya nakeji kuma bazan iya dafa abincin ba" wani kallo yayi mata kamar bazaije ba amma data É—ago ta kallesa ba shiri yamike zai fita saboda wani tsoronta daya shigesa da sauri yafice daga É—akin yana waiwayanta, amota ya zauna tai shuru yana tinani ahankali yatada motar tasa bai tsaya ko ina ba sai office É—in abokinsa kuma É—an uwansa Mas'ud, Mas'ud dake zaune cikin office É—insa yana danna laptop yaÉ—ago ya kalli Mustapha daya shigo abirkice bako sallama haka yasami waje ya zauna, Mas'ud ya tura laptop É—insa gefe yaja tagumi yana kallon Mustapha dayai wani zuru zuru kamar mara lafiya maganar Mustapha ta katsewa Mas'ud kallon dayake masa murya a raunane Mustapha yace
"Mas'ud na canza ko naga kanata kallo na wai dan Allah nima mutum ne?" aÉ—an tsorace Mas'ud yasake kallon Mustapha jin maganar data fito daga bakinsa
"Mutum ne kai mana maiya faru kake wannan tambayar?"
"Gaba É—aya banida nutsuwa Aboki wani iri nakejin kaina gani nake kamar bani ba"
"Aboki anya kuwa kanada lafiya ko asibiti zamuje a duba ka?"
"Bazamu ko ina ba lafiyata kalau kawai kamin addu'a kagayawa Ammi tayafemin nadaina zuwa gaisheta idan natafi gidan sai naga gaba É—aya na rasa hanyar"
"Mustapha kana azkhair kuwa anya ba aljanu ne suka shigeka ba, kayawaita azkhair sosai sannan kana karatun kur'ani koda yaushe kana sakawa a redion cikin motarka" wayar Mustapha datayi kara tasa ya mike da sauri yafice daga office É—in, Mas'ud yabisa da kallon tausayawa tabbas bako tantama asiri ne ajikin Mistapha inko har hakane tabbas zaiyi tsaiwa daka wajan ganin yataimakawa abokinsa, yazama dole yaje yasami Ammi suyi magana.

Sumayya ta fito daga É—akinta tana waya dariya take sosai harta shiga kicin da sauri ta karasa gaban tukunyar dake ajje a kasa ita gaba É—aya ma ta manta data É—ora girki, da sauri tamaida murfin ta rufe saboda wani kauri daya bigeta ta maida wayarta kunne taci gaba da magana da mamanta Amarya
"Amarya aiki yayi kyau sosai ai kirawa boka tsito kuÉ—i bakiga yanda Mustapha kejin tsorona ba komai nace yayi jiki na rawa yakemin kawai dai maganar yar aikin nan ce dai yaki yadda ki gayawa tsito yayi aiki dan Allah ya amince nasami mai aikin nan, kinsan dai ni Mama ban saba da wahala ba ko gidam Innah ba abinda nake saida agama naci nabar kwano nan bare wannan gidan mai uban girma bazan iya aikin saba wallahi Mama"

"Ke dayallah raguwa kina nan kina kazantarki ko tabbas ki canza inba haka ba zamu sami matsala dake duk abuna bana zama da kazanta, sannan maganar kuÉ—in nan kisake masa magana boka ya tabbatarmin zai bayar yau in aka tambayesa yaÉ—aure masa baki"
"To Mama zan tambayesa yanzu dai na aikesa siyomin abinci"
"Sumayya abinci kuma mai zanji wannan abu ba daÉ—in ji ke bazaki girka ba kenan gaskiyya ki canza koda asiri fa saida kissa wani abun ke tafiya dai dai adaina siyo abincin nan kina dafawa kinfa rigada kin iya komai nida nakeso ki rike zuciyarsa ta yanda koda asirinmu ya karye yaazama akwai wani abu naki da saboda shi kaÉ—ai zai iya zama dake"
"Mama yakike wannan fatan ai bazai ma karye ba muda muke da boka tsito ai bamuda sauran matsala zama daram a gidan Musty nifa Mama sai yanzu ma naji ina son sa da duk kwaÉ—aita min daular da kike bana hangowa sai yanzu danake cikinta" shigowar Mustapha yasa ta katse kiran.

*AIMANA*

tagama shirinta na kwanciya ta kwanta kusada Zaheed tana gyara masu blanket wayarta tayi kara hannu tasa saman bedsite drower ta É—auki wayar tata ganin bakuwar lamba ba suna yasa ta ajje harta katse bata É—aukaba sau biyu ana kira bata É—auka ba sai ana ukun ta É—aga kiran tareda karawa a kunnanta
"_Amincin Allah yatabbata a gareki ya tauraruwa a cikin taurari_" dim taji gabanta yai wani irin faɗuwa ta ciro wayar daga kun nanta ta kalli screen ɗin taga sam batasan lambar ba batama taɓa ganin ta ba
"Afuwan ba wannan layin kake nema ba"
"Shi nake nema mana Hayatie yakike ya daran?" tsaki taja takashe wayar gaba É—aya tayi addu'ar kwanciya barci ta kwanta da hannun dama rufe idanunta tayi bayan tayi bisimillah ahankali tasoma rero karatun suratul mulik har barci yayi awon gaba da ita.

Abbas ganin ta katse kiran yayi murmushi ya fito daga É—akinsa zuwa na Hajiyarsa, Hajiya Hafsatu mahaifiyar Abas na zaune cikin bedroom É—inta tana duba littafin addu'o'i na hislum muslim É—agowa tayi tareda amsa sallamar gudaliyar É—annata murmushin fuskarta ta faÉ—aÉ—a haÉ—i da faÉ—in
"Malam Abas bakayi barci ba nazaci gajiyar hanya zata saka kayi barci da wuri"
"Hajiyata ina zan iya barci banzo munyi hira ba gaba É—aya aikin nan baya barina sakewa dake sosai kamar da, Hajiya kinsan me?"
"Bansani ba Malam Abas saika faÉ—a"
"Hajiya kinyi suruka" Abas yafaÉ—i haka yana sunkuyar da kansa alamar jin kunya
"Nayi farin ciki sosai Malam Abas Allah yasa albarka yatabbatar mana da alkhairi"
"Amin" yace ahankali yakarasa gabanta ya tsugunna yaɗora kansa saman cinyarta "Hajiyata kimin addu'a yarinyar nan tasoni fiyeda yanda nake sonta Hajiya nafaɗa sosayayya mai zafi kowane bugu na zuciyata yana bugawa da soyayyatar ta" Hajiya Hafsa na murmushi tadafa kan yaron nata tana masa addu'a, ba sabon abu bane a wajansa tun yana yaro haka take masa harya saba indai yanason wani abu yakan tsugunna a gabanta yace "Hajiya amin addu'a" ba ɓoye ɓoye a tsakaninsu komai yana iya faɗa mata baya shayi ko shakkar faɗa, Hajiya Hafsatu wayayyar maca ce tana matukar son ɗannata guda ɗaya tak da Allah yabasu itada mijinta Alhaji wada idiris, Hira sosai Hajiya da Abas suke har zuwa sanda Alhaji Wada yadawo Abas yabar ɗakin bayan sun gaisa da Abban nasa...✍🏻

Game bukatar shuga group ko gyara ko wani karin bayani 07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GMAOuujeP6dLtFTHo1Edxx

🌹 *AIMANA*🌹

Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

Shafi na HuÉ—u

Ahankali take karanta addu'ar tashi daga barci, idanunta nakan agogon bangon dake manne jikin bangon É—akin, karfe biyar saura na asuba sakkowa tayi daga kan gado ta shiga bathroom ta É—auro alwala jin anata kiran sallah raka'anun fijir tasoma yi bayan ta idar ta zauna tana addu'o'i kafin sanda taji anyi assalatu, ta tayar da sallah, tasbihi tayi bayan ta idar da sallar tasoma karanto azkhair na safiya, harta kammala sannan ne Zeeyad yatashi tana kallonsa yashuga bathroom yaÉ—auro alwala yatada sallah, tamike tareda É—auke daddumar datayi sallah akai ta linke ta maida ta ma'ajjiyarta, tashin Zaheed tayi ta taimaka masa yayi alwala shima yai sallah wanka tamasu ta gama masu shirin makaranta sannan suka fito, lokacin bakwai saura Leena suka tarar tagama shirya kayan breakfast bisa danning ta koma kichin, Aimanah tana zama ta tina da wayarta ta kalli Zeeyad tace
"My Son É—akkomin phone É—ina a É—aki" yamike a nitse ya tafi, dai dai sannan Anty Ummi da Yaya Mansur suka sakko daga sama, Aimanah tagaidasu cikeda ladabi, tare sukayi break fast gaba É—aya bayan sun gama Yaya Mansur ya wuce wajan aikinsa tareda yara zai ajjesu a school, Aimanah tana buÉ—e wayarta sako na shugowa kamar daman jira ake ta buÉ—e wayar
Chapter 4 · 0% Book details